HASUMIYAR TSARO—NA NAZARI Afrilu 2018

Wannan fitowar tana dauke da talifofin nazari da za a yi daga ranar 4 ga Yuni zuwa 8 ga Yuli, 2018.

Yadda Za Mu Sami ’Yanci na Gaske

Wasu mutane suna so su sami ’yanci daga cin zarafi da nuna bambanci da talauci, wasu kuma suna neman ’yancin yin magana da na yin zabi. Zai yiwu mu sami ’yanci na gaske kuwa?

Ku Bauta wa Jehobah, Allah Mai Ba da ’Yanci na Gaske

Ta yaya ruhun Jehobah ya ’yantar da mu? Me zai taimaka mana don kada mu yi amfani da ’yancinmu a hanyar da ba ta dace ba?

Dattawa da Bayi Masu Hidima​—Ku Bi Misalin Timoti

Da alama cewa Timoti bai da karfin hali sosai sa’ad da ya soma hidima tare da manzo Bulus. Wane darasi ne dattawa da bayi masu hidima za su iya koya daga misalin Timoti?

Mu Yi Koyi da Jehobah​—Allahn da Ke Karfafa Mu

Bayin Jehobah sun dade suna bukatar karfafa.

Mu “Kara” Kwazo Wajen Karfafa Juna

Da yake ranar Jehobah ta yi kusa sosai, muna bukatar mu rika kaunar ’yan’uwanmu domin mu karfafa su idan da bukata.

Yara da Matasa, Ku Kafa Makasudai a Bautarku

Shawarar da matasa suke bukatar su yanke da kuma wasu abubuwa da suke fuskanta suna iya daure musu kai. Ta yaya za su iya yin zabi mai kyau?

Amsoshin Tambayoyin Masu Karatu

Me ya sa bai dace mu saka littattafan da Shaidun Jehobah suka wallafa a dandalin sada zumunta da dai sauransu ba?

Amsoshin Tambayoyin Masu Karatu

Zabura 144:​12-15 yana magana ne game da mutanen Allah?