Koma ka ga abin da ke ciki

Koma ga abubuwan da ke ciki

“Mai-Shari’an Dukan Duniya” Yana Yin Abin da Ya Dace a Kowane Lokaci

“Mai-Shari’an Dukan Duniya” Yana Yin Abin da Ya Dace a Kowane Lokaci

Dutse ne shi, aikinsa cikakke ne; gama dukan tafarkunsa shari’a ne.”K. SHA. 32:4.

WAƘOƘI: 112, 89

1. Ta yaya Ibrahim ya nuna cewa ya tabbata Jehobah zai yi abin da ya dace? (Ka duba hoton da ke shafin nan.)

SHIN “mai-shari’an dukan duniya” ba za ya yi abin da ya dace ba? (Far. 18:25) Wannan tambaya da Ibrahim ya yi ya nuna cewa ya tabbata Jehobah zai dauƙi matakin da ya dace a kan biranen nan Saduma da Gwamarata. Ƙari ga haka, Ibrahim ya tabbata cewa Jehobah ba zai taɓa ‘kashe masu-adalci tare da mugaye’ ba. Ibrahim ya san cewa yin hakan “ya yi nisa” da Allah. Bugu da ƙari, bayan shekaru 400, Jehobah ya ce kwatanta kansa: “Dutse ne shi, aikinsa cikakke ne; gama dukan tafarkunsa shari’a ne. Shi Allah mai-aminci ne, marar-mugunta, kuma, mai-adalci ne shi mai-gaskiya.”K. Sha. 32:4.

2. Me ya sa za a ce Jehobah ba zai iya yin rashin adalci ba?

2 Me ya sa Ibrahim ya tabbata cewa Jehobah zai yi abin da ya dace a kowane lokaci? Domin Jehobah ne yake kafa mizanan yin gaskiya da adalci. Sau da yawa ana amfani da waɗannan kalmomi “gaskiya” da “adalci” tare a Nassosin Ibrananci  domin suna nufin abu ɗaya. Saboda haka, da yake mizanan Jehobah daidai ne, zai yi abin da ya dace a koyaushe. Ƙari ga haka, Littafi Mai Tsarki ya ce: “Yana ƙaunar abin da ke na adalci da gaskiya.”Zab. 33:5.

3. Ka ba da misalin rashin adalci da ake yi a duniya.

3 Masu zuciyar kirki suna farin ciki idan suka koya cewa Jehobah yana yin abin da ya dace a kowane lokaci, domin ana rashin adalci a ko’ina a duniya. Alal misali, ana kama mutane kuma a saka su a fursuna ba tare da ƙwaƙƙwarar tabbacin laifin da suka yi ba. Amma da aka soma gwaje-gwajen matattarin sanin asalin halitta, wato DNA sai aka gano cewa wasu da aka saka a fursuna da suka yi shekaru da yawa ba su ne suka aikata laifin da aka tuhume su da shi ba. Irin wannan rashin adalci yana sa mutane baƙin ciki da kuma fushi. Duk da haka, akwai wani rashin adalci da ake wa Kiristoci da yake da wuyan jimrewa. Mene ne wannan?

A CIKIN IKILISIYA

4. Ta yaya za a iya jaraba bangaskiyar Kirista?

4 Babu shakka, mutanen da ba sa bauta wa Jehobah za su iya yi wa Kiristoci rashin adalci. Amma, za a iya jaraba bangaskiyarmu idan muka yi zaton cewa an mana ko wani da muka sani rashin adalci a cikin ikilisiya. Wane mataki ne za ka ɗauka idan kana ganin cewa an yi maka rashin adalci a cikin ikilisiya ko kuma wani ɗan’uwa ya yi maka hakan? Shin hakan zai sa ka daina bauta wa Jehobah?

5. Me ya sa Kirista ba zai yi mamaki ba idan ya lura cewa ana rashin adalci a cikin ikilisiya ko kuma wani ɗan’uwa ya masa hakan?

5 Domin dukanmu ajizai ne kuma mukan yi zunubi, mun fahimci cewa zai yiwu a yi mana rashin adalci ko kuma mu sa a yi ma wani rashin adalci a cikin ikilisiya. (1 Yoh. 1:8) Ko da yake hakan ba ya yawan faruwa, Kiristoci masu aminci ba sa yin mamaki idan aka yi musu rashin adalci. Ban da haka ma, ba sa daina yin tarayya da ikilisiya don hakan. Shi ya sa Jehobah ya ba mu shawara mai kyau a cikin Littafi Mai Tsarki da za ta taimaka mana mu kasance da aminci idan ‘yan’uwanmu suka yi mana rashin adalci.Zab. 55:12-14.

6, 7. Wane rashin adalci ne aka yi ma wani ɗan’uwa a cikin ikilisiya, kuma mene ne ya taimaka masa ya bi da yanayin yadda ya dace?

6 Ka yi la’akari da labarin Willi Diehl. Ɗan’uwa Diehl ya soma hidima a Bethel da ke birnin Bern a ƙasar Siwizalan a shekara ta 1931. A shekara ta 1946, ya halarci aji na takwas na makarantar Gilead a birnin New York da ke Amirka. An tura shi hidimar mai kula da da’ira a ƙasar Siwizalan bayan ya sauke karatu. A tarihinsa, Ɗan’uwa Diehl ya ce: “A watan Mayu na shekara ta 1949, na gaya wa ‘yan’uwa da ke kula da hedkwatarmu a birnin Bern cewa ina son in yi aure.” Amsar da suka ba ni shi ne: “Za ka riƙa yin hidimar majagaba na kullum ne kawai.” Ɗan’uwa Diehl ya ci gaba: “Ba a bar ni in riƙa yin jawabai ba . . . ’Yan’uwa da yawa ba sa gai da mu, suna bi da mu kamar waɗanda aka yi musu yankan zumunci.”

7 Wane mataki ne Ɗan’uwa Diehl ya ɗauka? Ya ce: “Mun san cewa ba a hana yin aure a cikin Littafi Mai Tsarki ba, saboda haka, mun ƙarfafa bangaskiyarmu ta wajen yin addu’a da kuma dogara ga Jehobah.” Daga baya, aka canja ra’ayin nan da bai dace ba game da yin aure da ya sa aka yi wa Ɗan’uwa Diehl wannan rashin adalci, kuma ya soma hidimarsa  kamar dā. Ya sami albarka sosai don ya kasance da aminci ga Jehobah. * Saboda haka, yana da kyau mu tambayi kanmu, ‘Shin zan yi abin da wannan ɗan’uwan ya yi idan aka min rashin adalci? Shin zan dogara ga Jehobah ko kuma zan yi ƙoƙari in magance matsalar da kai na?’Mis. 11:2; karanta Mikah 7:7.

8. Me ya sa za mu iya yin kuskure wajen yin zato cewa an yi mana ko kuma wani rashin adalci?

8 Akasin haka, kana iya yin kuskure idan ka yi zaton cewa an yi maka ko kuma wani a cikin ikilisiya rashin adalci. Me ya sa? Domin mu ajizai ne kuma wataƙila ba mu fahimci yanayin da kyau ba. Ƙari ga haka, mai yiwuwa ba mu san cikakken labarin ba. Ko da mun fahimci batun ko ba mu yi hakan ba, wajibi ne mu riƙa yin addu’a ga Jehobah game da yanayin, mu dogara gare shi kuma mu kasance da aminci. Hakan zai hana mu yin “gunaguni da Ubangiji.”Karanta Misalai 19:3.

9. Waɗanne misalai ne za mu bincika a wannan talifin da kuma na gaba?

9 Za mu bincika misalai uku na waɗansu bayin Jehobah da aka musu rashin adalci a zamanin dā. A wannan talifin, za mu bincika abin da ‘yan’uwan Yusufu tattaɓa-kunnen Ibrahim suka yi masa. A talifi na gaba, za mu bincika yadda Jehobah ya bi da Sarki Ahab da kuma abin da Bitrus ya fuskanta a Suriya ta Antakiya. Yayin da muke bincika waɗannan misalai, ka nemi darussan da za su taimaka maka ka ci gaba da bauta wa Jehobah da kuma inganta dangantakarka da shi, musamman ma sa’ad da kake zato cewa an yi maka rashin adalci.

AN YI WA YUSUFU RASHIN ADALCI

10, 11. (a) Wane rashin adalci ne aka yi wa Yusufu? (b) Wane zarafi ne Yusufu ya samu a fursuna?

10 Akwai wasu mutane da suka yi ma wani bawan Allah mai suna Yusufu rashin adalci. Amma abin da ya fi sa shi baƙin ciki shi ne rashin adalci da ‘yan’uwansa suka yi masa. A lokacin da Yusufu yake shekara 17, ‘yan’uwansa sun sace shi kuma suka sayar da shi a matsayin bawa kuma aka kai shi ƙasar Masar. (Far. 37:23-28; 42:21) Bayan ya yi wasu shekaru a wannan ƙasar, sai aka zarge shi da yin fyaɗe kuma aka saka shi a fursuna ba tare da yi masa shari’a ba. (Far. 39:17-20) Yusufu ya yi shekara 13 yana shan wahala da yake bawa ne da kuma fursuna. Waɗanne darussa za mu iya koya daga abin da ya faru da Yusufu da za su taimaka mana idan ‘yan’uwa suka yi mana rashin adalci?

11 Yusufu ya sami zarafin gaya wa wani ɗan fursuna da suke tare labarinsa. Wannan fursunan a dā yana miƙa wa sarki abin sha. A lokacin da shi da Yusufu suke fursuna, sai ya yi wani mafarki kuma Yusufu ya gaya masa abin da yake nufi. Yusufu ya gaya masa cewa za a sāke shi kuma ya soma aikin da yake yi a dā a fadar Fir’auna. Ƙari ga haka, Yusufu ya yi amfani da wannan zarafin don ya bayyana masa yanayinsa. Za mu iya koyan darussa masu muhimmanci daga abin da Yusufu ya faɗa da kuma abin da bai faɗa ba.Far. 40:5-13.

12, 13. (a) Ta yaya muka sani cewa Yusufu bai amince da rashin adalci da aka yi masa ba? (b) Mene ne Yusufu bai gaya wa mai miƙa wa sarki abin sha ba?

12 Karanta Farawa 40:14, 15. Ka lura cewa Yusufu ya ce an “sato” shi ne. Hakan ya nuna cewa an yi masa rashin  adalci ne. Yusufu ya faɗa sarai cewa bai yi laifin da ya sa aka jefa shi cikin kurkuku ba. Shi ya sa ya gaya wa mai miƙa wa sarki abin sha ya yi wa Fir’auna magana game da shi. Me ya sa ya yi hakan? Ya bayyana burinsa cewa don Allah ya “fishe ni daga cikin wannan gida.”

13 Shin Yusufu ya amince da yanayinsa ba tare da ɗaukan wani mataki ba? A’a. Shi dai ya san cewa an yi masa rashin adalci sosai. Shi ya sa ya bayyana yanayinsa ga mai miƙa wa sarki abin sha, don wataƙila zai taimaka masa. Amma Littafi Mai Tsarki bai ambata cewa Yusufu ya taɓa gaya ma wani ko Fir’auna cewa ‘yan’uwansa ne suka sace shi ba. Hakika, sa’ad da ‘yan’uwan Yusufu suka zo ƙasar Masar kuma suka sulhunta da shi, Fir’auna ya marabce su kuma ya ce su zauna a wurin don su more “albarka ta ƙasar Masar duka.”Far. 45:16-20.

Gulma tana jawo matsala sosai a ikilisiya (Ka duba sakin layi na 14)

14. Mene ne zai taimaka mana mu daina baƙar magana idan aka yi mana rashin adalci a cikin ikilisiya?

14 Idan wani ɗan’uwa yana ganin an yi masa rashin adalci, ya kamata ya mai da hankali don kada ya riƙa yaɗa labarin. Ko da yake zai dace ya nemi taimakon dattawa kuma ya gaya musu game da zunubin da ɗan’uwa ya yi. (Lev. 5:1) Amma a batutuwa da yawa da ba su shafi zunubi mai tsanani ba, zai iya ya sasanta da ɗan’uwan ba tare da gaya wa wani, ko dattawa ba. (Karanta Matta 5:23, 24; 18:15.) Bari mu kasance da aminci kuma mu yi amfani da ƙa’idodin Littafi Mai Tsarki a wannan yanayin. A wasu lokatai, mukan fahimci cewa ba rashin adalci ba ne aka yi mana. Saboda haka, za mu yi farin ciki sosai idan ba mu ɓata sunan ‘yan’uwanmu ko daɗa sa yanayin ya yi muni ba. Ka tuna cewa ko mu ne ke da gaskiya ko a’a, yin baƙar magana ba zai  gyara yanayin ba. Ƙari ga haka, kasancewa da aminci ga Jehobah da kuma ‘yan’uwanmu zai hana mu yin irin wannan kuskuren. Sa’ad da marubucin wannan zabura yake magana game da “wanda” ke biyayya, ya ce mutumin “ba ya yin tsegumi da harshensa, ba ya yi wa abokinsa mugunta, ba ya amsa zargi a kan makusancinsa ba.”Zab. 15:2, 3; Yaƙ. 3:5.

KA TUNA DA DANGANTAKAR DA TA FI MUHIMMANCI

15. Ta yaya dangantaka da Yusufu ya ƙulla da Jehobah ta sa ya sami albarka?

15 Za mu iya koyan darasi mai muhimmanci daga wurin Yusufu. A duk shekara 13 da ya yi yana shan wahala, Yusufu ya nuna cewa ya amince da ra’ayin Jehobah a kan batun. (Far. 45:5-8) Bai ɗora wa Jehobah laifi don wahalar da ya sha ba. Ko da yake bai manta da rashin adalci da aka yi masa ba, hakan bai sa shi baƙin ciki ainun ba. Abin da ya fi muhimmanci shi ne, bai bar ajizancin wasu da zunubansu suka sa ya daina bauta wa Jehobah ba. Da yake Yusufu ya kasance da aminci, Jehobah ya canja yanayinsa kuma ya albarkace shi da iyalinsa.

16. Me ya sa ya kamata mu kusaci Jehobah idan aka yi mana rashin adalci a cikin ikilisiya?

16 Hakazalika, wajibi ne mu ɗauki dangantakar mu da Jehobah da tamani. Bai kamata mu bar ajizancin ‘yan’uwanmu ya sa mu daina bauta wa Allah ba. (Rom. 8:38, 39) A maimakon haka, idan aka yi mana rashin adalci a cikin ikilisiya, bari mu yi koyi da Yusufu kuma mu kusaci Jehobah ta wajen kasancewa da ra’ayinsa. Bayan mun yi iya ƙoƙarinmu don mu magance matsalar ta wajen bin ƙa’idodin Littafi Mai Tsarki, muna bukatar mu bar batun a hannun Jehobah. Kuma ya kamata mu kasance da tabbaci cewa zai canja yanayin a hanya da kuma lokacin da ya dace.

KA AMINCE DA “MAI-SHARI’ AN DUKAN DUNIYA”

17. Ta yaya za mu nuna cewa mun tabbata da “mai-shari’an dukan duniya”?

17 Babu shakka, yayin da muke zama a wannan muguwar duniya za a yi mana rashin adalci. A wasu lokatai, za a yi maka rashin adalci ko kuma ka yi zato cewa an yi ma wani hakan a ikilisiya. Amma, kada hakan ya sa ka sanyin gwiwa. (Zab. 119:165) A maimakon haka, ka kasance da aminci ga Allah, ka riƙa yin addu’a don ya taimaka maka kuma ka dogara a gare shi. Domin mu ajizai ne, wataƙila ba mu fahimci yanayin ba ko kuma ba mu da cikakken bayanin. Kamar yadda muka koya daga misalin Yusufu, bai kamata mu riƙa yin baƙar magana ba don yin hakan zai daɗa sa yanayin ya yi muni. Ƙari ga haka, maimakon mu yi ƙoƙarin magance matsalar, bari mu ƙuduri niyya mu kasance da aminci kuma mu jira har lokacin da Jehobah zai daidaita yanayin. Yin hakan zai sa Jehobah ya albarkace mu kamar yadda ya yi wa Yusufu. Hakika, muna da tabbaci cewa Jehobah “mai-shari’an dukan duniya” zai riƙa yin abin da ya dace a kowane lokaci domin “dukan tafarkunsa shari’a ne.”Far. 18:25; K. Sha. 32:4.

18. Mene ne za mu bincika a talifi na gaba?

18 A talifi na gaba, za mu bincika misalan mutane biyu da aka yi wa rashin adalci a zamanin dā. Waɗannan misalan za su taimaka mana mu ga yadda tawali’u da gafarta wa mutane za su taimaka mana mu zama da ra’ayin Jehobah a yin adalci.

^ sakin layi na 7 Ka karanta tarihin ɗan’uwa Willi Diehl, “Jehovah Is My God, in Whom I Will Trust,” a cikin fitowar Hasumiyar Tsaro na 1 ga Nuwamba, 1991 a Turanci.