HASUMIYAR TSARO—NA NAZARI Afrilu 2017

Wannan fitowar tana dauke da talifofin nazari da za a yi daga ranar 29 ga Mayu zuwa 2 ga Yuli, 2017.

‘Ka Biya Abin da Ka Yi Wa’adi’ ko Alkawarinsa

Mene ne alkawari ko wa’adi? Mene ne Littafi Mai Tsarki ya fada game da yin wa’adi ko alkawari ga Allah?

Mene ne Mulkin Allah Zai Kawar?

Littafi Mai Tsarki ya ce, “duniya ma tana wucewa.” Mene ne wannan “duniyar” ta kunsa?

TARIHI

Na Ƙuduri Aniyar Zama Sojan Kristi

An saka Demetrius Psarras a kurkuku don ya ki shiga aikin soja. Amma ya ci gaba da rike amincinsa duk da wahalar da ya sha.

“Mai-Shari’an Dukan Duniya” Yana Yin Abin da Ya Dace a Kowane Lokaci

Me ya sa muka tabbata cewa Allah ba zai yi rashin adalci ba? Kuma me ya sa hakan yake da muhimmanci ga Kiristoci a yau?

Kana da Ra’ayin Jehobah Game da Yin Adalci?

Muna bukatar mu zama masu tawali’u da kuma masu gafartawa idan muna da irin ra’ayin Jehobah game da yin adalci. Me ya sa?

Ta Yaya Ba da Kai Yake Sa a Yabi Jehobah?

Allah yana daukan kwazon da muke saka wa a hidimarsa da muhimmanci