Koma ka ga abin da ke ciki

Koma ga abubuwan da ke ciki

Ku Rika Daraja “Abin da Allah Ya Hada”

Ku Rika Daraja “Abin da Allah Ya Hada”

“Abin da Allah ya haɗa, kada wani ya raba.”​—MAR. 10:9.

WAƘOƘI: 131, 132

1, 2. Mene ne ya kamata littafin Ibraniyawa 13:4 ya motsa mu mu yi?

BABU SHAKKA, dukanmu muna son daraja Jehobah. Ya cancanci mu daraja shi kuma ya ce shi ma zai daraja mu. (1 Sam. 2:30; K. Mag. 3:9; R. Yar. 4:11) Jehobah yana so mu riƙa daraja ’yan Adam, har da hukumomi. (Rom. 12:10; 13:7) Amma da akwai fannin da muke bukatar mu riƙa nuna daraja sosai. Wannan fannin shi ne a aure.

2 Manzo Bulus ya ce: “Zaman aure ya zama abin daraja a gare ku duka. Kada gadon aurenku ya ƙazantu.” (Ibran. 13:4) Ba magana ne kawai manzo Bulus yake yi ba, amma yana gaya wa Kiristoci ne cewa su riƙa daraja aure. Kana da wannan ra’ayin game da aure kuwa, musamman game da aurenka?

3. Wace shawara mai kyau ce Yesu ya bayar game da aure? (Ka duba hoton da ke shafin nan.)

3 Kana bin misali mai kyau idan kana daraja aure domin Yesu ma ya yi hakan. Sa’ad da Farisiyawa suka yi masa tambaya game da kashe aure, ya ambata abin da Allah ya ce game da aure na farko da ya ɗaura. Ya ce: “Domin haka fa, mutum zai bar babansa da mamarsa, ya manne wa matarsa su biyun kuma su zama ɗaya.” Ya ƙara da cewa: “Abin da Allah ya haɗa,  kada wani ya raba.”​—Karanta Markus 10:​2-12; Far. 2:24.

4. Mene ne manufar Allah game da aure?

4 Yesu ya tabbatar da cewa Allah ne ya shirya aure kuma bai kamata kome ya raba auren ba. Allah bai gaya wa Adamu da Hauwa’u cewa za su iya kashe aurensu ba. Manufar Allah a lambun Adnin shi ne su “biyun” su kasance tare har abada.

ABUBUWAN DA SUKA JAWO CANJI A AURE

5. Ta yaya mutuwa take shafan aure?

5 Kun san cewa zunubin da Adamu ya yi ya kawo canji a aure? Ɗaya cikin canjin shi ne cewa ’yan Adam sun soma mutuwa kuma hakan na shafan aure. Mun ga wannan bayanin a furucin manzo Bulus ga Kiristoci. Ya ce mutuwa tana raba aure, kuma mutumin na da ’yancin sake yin aure.​—Rom. 7:​1-3.

6. Ta yaya Dokar ta koya mana ra’ayin Allah game da aure?

6 Dokar da Allah ya ba Isra’ilawa tana ɗauke da bayanai da yawa game da aure. Dokar ta yarda Isra’ilawa su auri mata da yawa, kuma suna hakan kafin Allah ya ba da Dokar. Amma dokar ta hana magidanta wulaƙanta matansu da yaransu. Alal misali, idan Ba’isra’ile ya auri baiwa, sai daga baya ya sake auro wata, wajibi ne ya riƙa biyan bukatun matarsa ta farko. Allah ya ce ya riƙa kāre ta kuma ya kula da ita. (Fit. 21:​9, 10) A yau, ba ma bin dokar da Allah ya bayar ta hannun Musa, amma dokar ta nuna mana ra’ayin Allah game da aure. Babu shakka, hakan yana taimaka maka ka daraja aurenka!

7, 8. (a) Mene ne littafin Maimaitawar Shari’a 24:1 ya ce game da kashe aure? (b) Mene ne ra’ayin Allah game da kashe aure?

7 Mene ne Dokar ta ce game da kashe aure? Ko da yake Jehobah bai so ma’aurata su kashe aurensu ba, amma dokar ta yarda Ba’isra’ile ya saki matarsa idan ya ga ‘wani abu marar kyau game da ita.’ (Karanta Maimaitawar Shari’a 24:1.) Dokar ba ta faɗa irin ‘abu marar kyau’ da wurin nan ya ambata ba. Amma da alama cewa abu ne mai tsanani sosai, ba abin da bai taƙa-kara-ya-karya ba. (M. Sha. 23:14) Abin baƙin ciki ne cewa a zamanin Yesu, Yahudawa da yawa sun kashe aurensu “a kan kowane irin dalili.” (Mat. 19:3) Bai kamata mu yi koyi da halinsu ba.

8 Annabi Malakai ya bayyana ra’ayin Allah game da kashe aure. Ya yi hakan a lokacin da maza suke sakin matar da suka auro a ‘ƙuruciyarsu’ don su auro wata budurwar da ba ta bauta wa Jehobah. Amma Allah ya ce: Na ‘ƙi kisan aure.’ (Mal. 2:​14-16) Hakan ya jitu da abin da Allah ya faɗa a Kalmarsa game da aure na farko da ya ɗaura. Ya ce: “Mutum zai . . . manne wa matarsa, biyun su zama ɗaya.” (Far. 2:24) Kuma Yesu ya goyi bayan ra’ayin Ubansa sa’ad da ya ce: “Abin da Allah ya haɗa, kada wani ya raba.”​—Mat. 19:6.

HUJJA GUDA NA KASHE AURE

9. Mene ne furucin Yesu da ke Markus 10:​11, 12 yake nufi?

9 Wasu suna iya yin tambaya cewa: ‘Da akwai dalilin da zai sa Kirista ya kashe aurensa kuma ya sake yin aure?’ Yesu ya faɗi ra’ayinsa game da kashe aure, ya ce: “Duk mutumin da ya saki matarsa, ya auri wata, yana cin amanar mace ta farko da yin laifin zina ke nan. In kuma mace ta saki mijinta ta auri wani ta yi zina ke nan.” (Mar. 10:​11, 12; Luk. 16:18) A bayyane yake cewa Yesu ya daraja aure kuma yana so mu yi koyi da shi. Mijin da ya saki matarsa da ba ta yi zina ba (ko  kuma macen da ta saki mijinta da bai yi zina ba) kuma ya auri wata yana yin zina. Hakan gaskiya ne domin idan mutum ya kashe aurensa haka kawai, hakan bai raba gamin auren ba. Domin a wurin Allah, har ila su biyun “ɗaya” ne. Bugu da ƙari, Yesu ya ce mutumin da ya saki matarsa da ba ta yi zina ba yana sa ta fuskanci jarrabawar yin zina. Ta yaya? A zamanin dā, macen da aka saka za ta iya so ta sake yin aure domin ta sami biyan bukatunta. Amma idan ta sake aure, ta yi zina.

10. Me zai iya sa Kirista ya kashe aurensa kuma ya sake yin wani auren?

10 Yesu ya faɗi abin da zai iya sa mutum ya kashe aurensa. Ya ce: ‘Ina kuma gaya muku, duk wanda ya saki matarsa, idan dai ba saboda an same ta da yin zina ba, [Helenanci, por·neiʹa], ya kuma aure wata, ya yi zina.’ (Mat. 19:9) Ya yi furuci makamancin haka a Huɗubarsa a Kan Dutse. (Mat. 5:​31, 32) A waɗannan surori biyu, Yesu ya ambata “zina.” Yin zina ya ƙunshi yin karuwanci da lalata da daudanci da yin jima’i da dabbobi. Alal misali, idan mutumin da ya yi aure ya yi zina, matarsa za ta iya yanke shawarar kashe aurensu ko kuma ta yafe masa. Idan ta sake shi, auren ya mutu a wurin Allah.

11. Me zai iya sa Kirista ya ƙi kashe aurensa ko da wani cikinsu ya yi zina?

11 Ku lura cewa Yesu bai ce idan wani ya yi zina, (wato por·neiʹa) lallai sai mijin ko matar ta sake shi ba. Alal misali, mace za ta iya yanke shawarar kasancewa da maigidanta ko da ya yi zina. Wataƙila har ila tana ƙaunar sa kuma tana a shirye ta kyautata dangantakarsu. Babu shakka, idan ta saki mijinta kuma ba ta sake yin aure ba, za ta fuskanci ƙalubale. Ba za ta sami biyan bukatunta na zahiri da na jima’i ba. Za ta kaɗaita. Sakin zai shafi yaranta. Zai iya sa ya kasance da wuya yaran su koyi gaskiya. (1 Kor. 7:14) Hakika, za ta fuskanci ƙalubale sosai idan ta saki mijinta.

12, 13. (a) Mene ne ya faru a auren Hosiya? (b) Me ya sa Hosiya ya gafarta wa matarsa, kuma wane darasi ne hakan ya koya mana game da aure?

 12 Abin da ya faru da annabi Hosiya ya koya mana ra’ayin Allah game da aure. Allah ya gaya masa cewa ya auri wata mai suna Gomer. Ya ce za ta zama “karuwa” kuma za ta “haifi ’ya’yan karuwanci.” Sai Gomer ta “yi ciki ta haifa” wa Hosiya ɗa. (Hos. 1:​2, 3) Bayan haka, ta sake haifan yara biyu, namiji da ta mace kuma wataƙila sanadiyyar zina. Duk da yake Gomer ta yi zina sau da yawa, Hosiya ya gafarta mata. Daga baya, ta bar Hosiya kuma ta zama baiwa. Duk da haka, Hosiya ya dawo da ita. (Hos. 3:​1, 2) Jehobah ya yi amfani da Hosiya don ya kwatanta yadda yake gafarta wa Isra’ilawa duk da allolin ƙarya da suke bauta wa. Wane darasi ne za mu iya koya daga wannan labarin?

13 Idan Kirista ya yi zina, matarsa da ba ta yi zina ba ko kuma mijin da bai yi zina ba zai bukaci ya yanke shawara. Yesu ya ce mijin ko matar za ta iya kashe auren kuma ta sake auran wani. Amma idan mijin ko matar da ba ta yi zina ba ta so, za ta iya gafarta masa. Yin hakan ba laifi ba ne. Hosiya ya gafarta wa matarsa. Sa’ad da ta sake dawowa, Hosiya ya gaya mata cewa kada ta sake kwana da wani. Hosiya bai sake “kwana” da matarsa ba har sai bayan wani lokaci. (Hos. 3:3) Da alama cewa Hosiya ya sake soma saduwa da matarsa. Hakan yana wakiltar yadda Jehobah ya yarda ya gafarta wa mutanensa kuma ya daidaita dangantakarsa da su. (Hos. 1:11; 3:​3, 5) Wane darasi ne hakan ya koya wa ma’aurata a yau? Idan Kirista ya yi zina kuma matarsa ta yarda ta gafarta masa, sake yin jima’i da shi zai nuna cewa ta gafarta masa. (1 Kor. 7:​3, 5) Yin hakan zai soke duk hujjar da mijin ko matar take da ita na kashe auren. Bayan haka, ya kamata su biyu su ƙoƙarta don su kasance da ra’ayin Allah game da aure.

KU DARAJA AURE KO DA KUNA FUSKANTAR MATSALA

14. Mene ne littafin 1 Korintiyawa 7:​10, 11 ya ce zai iya faruwa a aure?

14 Ya kamata dukan Kiristoci su riƙa daraja aure yadda Jehobah da Yesu suke yi. Amma wasu ba sa yin hakan domin dukanmu ajizai ne. (Rom. 7:​18-23) Saboda haka, bai kamata mu yi mamaki cewa wasu Kiristoci a ƙarni na farko sun fuskanci matsaloli a aurensu ba. Manzo Bulus ya ce “kada mata ta rabu da mijinta,” amma a wasu lokuta, hakan yana faruwa.​—Karanta 1 Korintiyawa 7:​10, 11.

Me zai iya taimaka wa ma’auratan da ke fuskantar matsaloli a aurensu? (Ka duba sakin layi na 15)

15, 16. (a) Me ya kamata ma’aurata su ƙoƙarta su yi idan suna fuskantar matsala a aurensu, kuma me ya sa? (b) Yaya hakan ya shafi ma’auratan da ɗaya cikinsu ba ya bauta wa Jehobah?

15 Manzo Bulus bai faɗi yanayin da ya sa ma’auratan suka rabu ba. Amma mun san cewa matsalar ba don mijin ko matar ta yi zina ba. Bulus ya faɗi cewa kada matar da ta rabu da mijinta ta “yi aure, sai dai ta sāke shirya da mijinta.” Hakan ya nuna cewa har ila, Jehobah yana ganin su a matsayin mata da miji. Bulus ya ce ma’auratan da suka rabu da juna su sasanta muddin ba zina ba ce ta jawo rabuwar ba. Su biyun suna iya neman shawara daga wurin dattawa a ikilisiya. Kada dattawan su goyi bayan kowannensu, amma su nuna musu shawarwarin da ke cikin Littafi Mai Tsarki.

16 Yanayin zai fi tsanani idan ɗaya cikin ma’auratan ba ya bauta wa Jehobah. Idan matsaloli sun taso a irin  wannan yanayin, zai dace su rabu da juna kuwa? Kamar yadda muka tattauna, Littafi Mai Tsarki ya nuna cewa zina ce za ta iya sa ma’aurata su kashe aurensu, amma bai ambata abin da zai iya sa ma’aurata su rabu da juna ba. Manzo Bulus ya ce: “Idan kuma wata mace tana da miji marar bi, ya kuwa yarda su zauna tare, to, kada ta rabu da shi.” (1 Kor. 7:​12, 13) Shawarar nan ta shafe mu ma a yau.

17, 18. Me ya sa wasu Kiristoci ba su rabu da abokin aurensu ba duk da matsalolin da suke fuskanta?

17 Amma akwai wasu lokuta da “miji marar bi” ya ƙi shi da matarsa su “zauna tare.” Alal misali, wataƙila yana dūkan ta sosai kuma hakan ya sa tana ganin cewa rayuwarta tana cikin haɗari. Ko kuma ya ƙi biyan bukatun ta da na iyalin ko kuma ya ƙi ta bauta wa Jehobah. A irin wannan yanayin, matar tana iya yanke shawara cewa ko da mene ne maigidan ya ce, bai yarda su “zauna tare” ba kuma tana so ta rabu da shi. Amma wasu da ke irin yanayin sun ci gaba da jimrewa kuma sun nemi hanyoyin magance matsalar. Me ya sa?

18 Domin ko da sun rabu, aurensu bai mutu ba tukun kuma za su fuskanci ƙalubalen da muka ambata ɗazu. Manzo Bulus ya ambata wani dalilin da ya sa bai kamata Kiristoci su rabu ba. Ya ce: “Miji marar ba da gaskiya a tsarkake yake ta wurin zama ɗaya da matarsa, haka kuwa mace marar ba da gaskiya a tsarkake take, ta wurin zama ɗaya da mijinta. In ba haka ba ’ya’yanku za su zama ƙazamai, amma yanzu su masu tsarki ne.” (1 Kor. 7:14) Kiristoci ma’aurata da yawa sun ci gaba da zama da matarsu ko mijinsu marar bi duk da cewa suna fuskantar matsaloli sosai. Yawancinsu sun yi farin ciki cewa ba su rabu ba domin daga baya, matar ko mijin ya soma bauta wa Jehobah.​—Karanta 1 Korintiyawa 7:16; 1 Bit. 3:​1, 2.

19. Me ya sa akwai Kiristoci ma’aurata da yawa da suke jin daɗin aurensu?

19 Yesu ya yi gargaɗi game da kashe aure, manzo Bulus kuma ya ba da shawara game da rabuwa. Su biyu suna so bayin Allah su riƙa daraja aure. A yau, ikilisiyoyin Shaidun Jehobah na cike da ma’auratan da suke jin daɗin aurensu. Wataƙila akwai ma’aurata da yawa a ikilisiyarku da ke jin daɗin aurensu. Su maza ne da ke son matarsu da kuma matan da ke son mazansu sosai. Dukansu suna nuna cewa aure tana da daraja. Muna farin ciki cewa miliyoyin mutane suna bin abin da Allah ya faɗa cewa: “Saboda haka mutum zai bar mamarsa da babansa, ya manne wa matarsa, su biyu su zama jiki ɗaya.”​—Afis. 5:​31, 33.