Koma ka ga abin da ke ciki

Koma ga abubuwan da ke ciki

Shin Yakubu ya zama kakan Almasihu ne domin ya sayi matsayin Isuwa na ɗan fari?

Amsoshin Tambayoyin Masu Karatu

Amsoshin Tambayoyin Masu Karatu

Shin waɗanda Almasihu ya fito daga zuriyarsu a Israila ta dā ’ya’yan fari ne kawai?

Mun taɓa tattauna wannan batun a kwanan baya. Hakan ya jitu da abin da aka rubuta a Ibraniyawa 12:16. Wannan ayar ta nuna cewa Isuwa ‘marar-ibada’ ne shi ya sa ‘ya sayar wa [Yakubu] gādonsa na ɗan fari saboda akushin abinci.’ Kamar dai hakan ya nuna cewa sa’ad da Yakubu ya samu hakki na “ɗan fari” sai ya zama cikin waɗanda Almasihu zai fito daga zuriyarsu.​—Mat. 1:​2, 16; Luk. 3:​23, 34.

Amma mun bincika wasu labaran Littafi Mai Tsarki da suka nuna cewa ba sai mutum ya zama ɗan fari ba ne kafin Almasihu ya fito daga zuriyarsa. Bari mu bincika wasu abubuwan da suka sa muka ce hakan:

Alal misali, Reuben ne ɗan fari da matar Yakubu, Lai’atu ta haifa masa. Bayan wani lokaci, sai Rahila wadda Yakubu ya fi so ta haifa masa Yusufu. Amma da Reuben ya kwana da kwarkwarar mahaifinsa, sai Yusufu ya ɗauki matsayinsa na ɗan fari. (Far. 29:​31-35; 30:​22-25; 35:​22-26; 49:​22-26; 1 Laba. 5:​1, 2) Duk da haka, Almasihu bai fito daga zuriyar Reuben ko Yusufu ba. Almasihun ya fito daga zuriyar Yahuda wanda  shi ne ɗa na huɗu da Lai’atu ta haifa wa Yakubu.​—Far. 49:10.

Luka 3:32 ya lissafa sunayen mutane biyar da Almasihu ya fito daga zuriyarsu. Kuma dukansu ’ya’yan fari ne. Boaz ya haifi Obed, Obed kuma ya haifi Jesse.​—Ruth 4:​17, 20-22; 1 Laba. 2:​10-12.

Amma ɗan Jesse, wato Dauda ba shi ba ne ɗan fari, shi ne ɗan auta daga cikin yaran Jesse guda takwas. Duk da haka, Almasihun ya fito ne daga zuriyarsa. (1 Sam. 16:​10, 11; 17:12; Mat. 1:​5, 6) Haka ma yake da Sulemanu, Almasihun ya fito daga zuriyarsa ko da yake ba shi ne ɗan farin Dauda ba.​—2 Sam. 3:​2-5.

Hakan ba ya nuna cewa zama ɗan fari bai da wani muhimmanci. Domin ɗan fari shi ne babba a cikin yara kuma shi ne yake zama magaji. Ban da haka ma, gādonsa yakan fi na sauran yaran.​—Far. 43:33; K. Sha. 21:17; Josh. 17:1.

Amma za a iya ɗaukan matsayin ɗan fari a ba wani. Ibrahim ya kori ɗansa Isma’ilu kuma ya ba Ishaƙu matsayin ɗan fari. (Far. 21:​14-21; 22:2) Kuma kamar yadda muka ambata ɗazu, an ba Yusufu matsayin Reuben na ɗan fari.

Yanzu bari mu tattauna Ibraniyawa 12:16 da muka ambata ɗazu. Wurin ya ce: “Kada wani mai-fasikanci ya kasance, ko kuwa wani marar-ibada kamar Isuwa, wanda ya sayar da gādonsa na ɗan fari saboda akushin abinci.” Mene ne wannan wurin yake nufi?

A wannan ayar, manzo Bulus ba ya maganar zuriyar Almasihu. Ta yaya muka san hakan? Kafin ya yi wannan maganar, ya ƙarfafa Kiristoci su yi rayuwa da ta jitu da ƙa’idodin Allah don kada su “kāsa samun alherin Allah.” Hakan zai iya faruwa idan suka yi lalata. (Ibran. 12:​12-16, Littafi Mai Tsarki) Kuma idan suka yi hakan, za su zama kamar Isuwa “marar-ibada” wanda ya sayar da gādonsa kuma ya biɗi abin duniya.

Isuwa ya yi rayuwa a zamanin dā kuma wataƙila a wasu lokuta yakan yi wa Allah hadayu. (Far. 8:​20, 21; 12:​7, 8; Ayu. 1:​4, 5) Amma da yake Isuwa ba mai ibada ba ne, ya ba da matsayinsa na ɗan fari don ya sami jar miya. Wataƙila ya yi hakan don ya guji wahalar da aka ce zuriyar Ibrahim za ta sha. (Far. 15:13) Isuwa ya mai da hankali ga abin da bai da amfani shi ya sa bai ga muhimmancin ibada ba. Kuma ya auri mata biyu da ba sa bauta wa Jehobah kuma hakan ya sa iyayensa baƙin ciki sosai. (Far. 26:​34, 35) Amma Yakubu bai yi hakan ba shi ya sa ya auri mace da take bauta wa Jehobah.​—Far. 28:​6, 7; 29:​10-12, 18.

Don haka, me za mu iya cewa game da zuriyar da Almasihun ya fito daga ciki? Zuriyar da Yesu ya fito daga ciki ya ƙunshi ’yan fari da waɗanda ba ’yan fari ba. Yahudawa sun san da hakan kuma suka amince da shi kamar yadda suka yarda cewa Kristi ya fito ne daga zuriyar Dauda wanda shi ne ɗan autan Jesse.​—Mat. 22:42.