Koma ka ga abin da ke ciki

Koma ga abubuwan da ke ciki

Iyaye​—Ku Taimaki Yaranku Su Yi ‘Hikima’ don Su Sami Ceto

Iyaye​—Ku Taimaki Yaranku Su Yi ‘Hikima’ don Su Sami Ceto

“Tun kana jariri fa ka san littattafai masu-tsarki, waɗanda ke da iko su hikimtar da kai zuwa ceto.”​—2 TIM. 3:15.

WAƘOƘI: 141, 134

1, 2. Me ya sa wasu iyaye suke damuwa sa’ad da yaransu suke son su keɓe kansu ga Jehobah kuma su yi baftisma?

MUTANE dubbai sun yi nazarin Littafi Mai Tsarki kuma sun yi alkawarin bauta wa Jehobah bayan haka suka yi baftisma. Da yawa a cikinsu matasa ne da iyayensu suke bauta wa Jehobah kuma sun zaɓi salon rayuwa mafi kyau. (Zab. 1:​1-3) Babu shakka, iyaye suna farin cikin ganin ranar da ɗansu ko ’yarsu za ta yi baftisma.​—Gwada 3 Yohanna 4.

2 Duk da haka, akwai wasu abubuwa da ke damun iyaye. Wataƙila sun ga wasu matasa da suka yi baftisma amma bayan wasu shekaru sai suka soma shakkar amfanin bin ƙa’idodin Allah. Da yawa a cikinsu sun daina bauta wa Jehobah. Saboda haka, kana iya damuwa cewa yaronka zai soma bauta wa Jehobah amma bayan wasu shekaru, sai ya canja ra’ayinsa kuma ya daina ƙaunar Jehobah. Yaron yana iya zama kamar waɗanda suke ikilisiyar Afisa a ƙarni na farko da Yesu ya ce game da su: ‘Kun bar ƙaunarku ta fari.’ (R. Yoh. 2:4) Ta yaya za ka taimaka  wa yaronka ya ci gaba da ƙaunar Jehobah kuma ya “yi girma zuwa ceto?” (1 Bit. 2:2) Bari mu bincika misalin Timotawus.

“KA SAN LITTATTAFAI MASU-TSARKI”

3. (a) A wane yanayi ne Timotawus ya zama Kirista, kuma wane ra’ayi ne ya kasance da shi game da koyarwar Jehobah? (b) Waɗanne abubuwa uku ne Bulus ya ce Timotawus ya mai da hankali a kansu?

3 Wataƙila a shekara ta 47 bayan haihuwar Yesu ne Timotawus ya koyi gaskiya a lokacin da manzo Bulus ya kai ziyararsa ta farko zuwa Lystra. Ko da yake a lokacin Timotawus matashi ne, yana da halin kirki. Ƙari ga haka, bayan shekara biyu sai ya zama abokin tafiyar Bulus, kuma bayan shekara 16 sai Bulus ya rubuta wa Timotawus wasiƙa cewa: “Ka lizima kai a cikin al’amuran da ka koyo, waɗanda ka tabbata da su kuma, ka sani wurin ko waɗannene ka koye su; tun kana jariri fa ka san littattafai masu-tsarki [Nassosin Ibrananci], waɗanda ke da iko su hikimtar da kai zuwa ceto ta wurin bangaskiya wanda ke cikin Kristi Yesu.” (2 Tim. 3:​14, 15) Ka lura cewa Bulus ya ambata (1) sanin littattafai masu tsarki, (2) tabbata da abubuwan da ya koya, da kuma (3) zama mai hikima don samun ceto ta wurin yin imani da Yesu Kristi.

4. Waɗanne abubuwa ne suka taimaka maka sa’ad da kake koya wa yaranka game da Jehobah? (Ka duba hoton da ke shafi na 18.)

4 Iyaye suna son yaransu su san littattafai masu tsarki, wato Nassosin Ibrananci da na Helenanci. Bisa ga shekarunsu, har yara ƙanana suna iya koyon wasu abubuwa game da mutane da labaran da ke cikin Littafi Mai Tsarki. Ƙungiyar Jehobah ta wallafa abubuwa da yawa da iyaye za su iya amfani da su don su taimaka wa yaransu. Waɗanne ne kuke da su a yarenku? Ka tuna cewa sanin Nassosi ne zai taimaka wa mutum ya ƙulla dangantaka ta kud da kud da Jehobah.

“KA TABBATA DA SU”

5. (a) Mene ne Bulus yake nufi sa’ad da ya ce Timotawus ya tabbata da abin da ya yi imani da shi? (b) Ta yaya muka sani cewa an sa Timotawus ya tabbata da bishara game da Yesu?

5 Sanin littattafai masu tsarki yana da muhimmanci. Amma, da akwai wasu abubuwan da za a iya yi ban da koya wa yara kawai game da mutane da kuma labaran Littafi Mai Tsarki. An taimaka wa Timotawus ya “tabbata” da abin da ya yi imani da shi. A yare na asali, “wannan yana nufin amincewa da wani batu.” Timotawus ya san Nassosin Ibrananci tun daga jariri. Amma akwai lokacin da wasu abubuwa suka tabbatar wa Timotawus cewa Yesu ne Almasihu kuma hakan ya ƙara ƙarfafa bangaskiyarsa. Timotawus yana da tabbaci sosai game da bishara kuma hakan ya sa ya zama almajiri da ya yi baftisma kuma ya bi Bulus yin wa’azi a ƙasar waje.

6. Ta yaya za ka taimaka wa yaranka su tabbata da abin da suke koya daga Kalmar Allah?

6 Ta yaya za ka taimaka wa yaranka su tabbata da abin da suka yi imani da shi kamar Timotawus? Da farko, ka zama mai haƙuri. Ba a sa mutum ya tabbata da abu nan da nan, saboda haka yaranka ba za su kasance da wannan tabbacin domin ka gaya musu su gaskata da hakan ba. Kowane yaro yana bukatar ya yi amfani da hankalinsa don ya bambanta “nagarta da mugunta” kuma ya tabbata da koyarwar Littafi Mai Tsarki. (Karanta Ibraniyawa 5:14.) Iyaye suna da aiki mai muhimmanci da za su yi a wannan batun, musamman ma sa’ad da yaransu suka yi tambaya. Ga wani misali.

7, 8. (a) Ta yaya wani mahaifi ya kasance da haƙuri sa’ad da yake koyar da ’yarsa? (b) A wane lokaci ne ka bukaci ka zama mai haƙuri?

7 Wani mahaifi mai suna Thomas, da  yake da yarinya ’yar shekara 11 ya ce: “A wasu lokuta ’yata tana tambaya na cewa, ‘Shin Jehobah ya halicci abubuwa masu rai a duniya ta juyin halitta?’ ko kuma, ‘Me ya sa ba ma haɗa kai da mutane don mu zaɓi wanda zai iya magance matsalolinmu? Wani lokaci, nakan yi ƙoƙari sosai don kada ya zama kamar ina cusa mata ra’ayina ne. Ballantana ma, taimaka wa mutum ya kasance da tabbaci ba ya nufin faɗin wani abu na musamman. Amma kana iya yin amfani da wasu misalai don ka tabbatar masa da wani batu.”

8 Kamar Thomas, mutum yana bukatar ya zama mai haƙuri kafin ya koyar da wani abu. Kuma yana da muhimmanci dukan Kiristoci su zama masu haƙuri. (Kol. 3:12) Thomas ya fahimci cewa zai bukaci ya riƙa tattaunawa da ’yarsa a kai a kai kafin ta fahimci batun. Yana bukatar ya sa ta yi tunani a kan wasu Nassosi don ta tabbata da abin da take koya. Thomas ya ce: “Musamman a kan batutuwa masu muhimmanci, ni da matata muna son mu san ko ’yarmu ta gaskata da abin da take koya kuma ta fahimce su. Kuma yana da kyau ta riƙa tambayoyi, don ba zan yi farin ciki ba idan ta gaskata da wani abu ba tare da yin tambayoyi ba.”

9. Ta yaya za ka taimaka wa yaranka su gaskata da Kalmar Allah?

9 Idan iyaye suna da haƙuri, a hankali yaransu za su soma fahimtar yadda za su zama masu bangaskiya sosai. (Afis. 3:18) Ya kamata mu riƙa koya musu abubuwan da za su iya fahimta da ya yi daidai da shekarunsu da kuma iyawarsu. Kuma yayin da suka zama masu bangaskiya sosai, zai yi musu sauƙi su kāre imaninsu a gaban wasu, har da abokan makarantarsu. (1 Bit. 3:15) Alal misali, shin yaranka za su iya yin amfani da Littafi Mai Tsarki su bayyana wa mutane abin da ke faruwa sa’ad da mutum ya mutu? Shin sun fahimci abin da Littafi Mai Tsarki ya faɗa game da batun? * Hakika, kana bukatar ka zama mai haƙuri don ka taimaka wa yaronka ya gaskata da Kalmar Allah, kuma za ka yi farin ciki idan ka yi iya ƙoƙarinka don ka yi hakan.​—K. Sha. 6:​6, 7.

10. Me ya kamata ya kasance da muhimmanci sa’ad da kake koyar da yaranka?

10 Hakika, yana da muhimmanci ka kafa misali mai kyau don ka taimaka wa yaranka su kasance da bangaskiya. Wata mahaifiya mai suna Stephanie da take da yara mata uku ta ce: “Tun yarana suna ƙanana, nakan tambayi kaina, ‘Shin ina gaya wa yarana dalilin da ya sa na yi imani cewa Jehobah yana wanzuwa kuma yana ƙaunarmu da yin adalci a kowane lokaci? Shin yarana suna ganin cewa ina ƙaunar Jehobah da gaske?’ Yarana ba za su kasance da tabbaci ba idan ban yi hakan ba.”

‘HIKIMA’ DON SAMUN CETO

11, 12. Mece ce hikima, kuma ta yaya muka sani cewa ba yawan shekarun mutum ba ne yake nuna cewa shi mai hikima ne?

11 Mun koya cewa Timotawus ya (1) san Nassosi kuma (2) ya tabbata da abin da ya yi imani da shi. Amma mene ne Bulus yake nufi sa’ad da ya ce littattafai masu tsarki za su iya sa Timotawus ya zama mai ‘hikima’ don samun ceto?

12 A Littafi na 2 na Insight on the Scriptures, an bayyana cewa hikima tana nufin “iya yin amfani da abin da mutum ya sani kuma fahimta da kyau don ya magance matsaloli. Ƙari ga haka, zai guje  wa haɗarurruka kuma ya cim ma wasu makasudai ko kuma ya ba wasu shawara a yin hakan. Mai hikima ba ya wawanci.” Littafi Mai Tsarki ya ce “wauta tana nan ƙunshe a zuciyar yaro.” (Mis. 22:15) Mutum mai hikima ba ya wauta, amma hikimarsa tana nuna cewa ya manyanta. Ban da haka ma, ba yawan shekarun mutum ba ne yake nuna cewa ya manyanta amma tsoron Jehobah ne da kuma son ya yi masa biyayya.​—Karanta Zabura 111:10.

13. Ta yaya matashi zai nuna cewa yana da hikima don samun ceto?

13 Sha’awoyin duniya da kuma matsi daga tsaransu ba za su iya sa matasa da suka manyanta su yi abin da bai dace ba. (Afis. 4:14) A maimakon haka, za su iya zama masu ibada sosai idan suka koyar da kansu don su iya sanin “nagarta da mugunta.” (Ibran. 5:14) Suna tsai da shawarwari masu kyau a lokacin da iyayensu ko wasu ba sa tare da su. (Filib. 2:12) Suna bukatar kasancewa da irin wannan hikima don su sami ceto. (Karanta Misalai 24:14.) Ta yaya za ka taimaka wa yaranka su kasance da hikima haka? Kana bukatar ka koya musu ƙa’idodin Littafi Mai Tsarki. Ƙari ga haka, ya kamata su ga cewa kana iya ƙoƙarinka don ka bi ƙa’idodin Kalmar Allah ta furucinka da yadda kake abubuwa.​—Rom. 2:​21-23.

Me ya sa yake da muhimmanci iyaye su riƙa koyar da yaransu? (Ka duba sakin layi na 14-18)

14, 15. (a) Mene ne ya kamata matashin da yake son ya yi baftisma ya yi tunani a kai? (b) Ta yaya za ka taimaka ma yaranka su yi tunani a kan albarkar da za su samu idan suka bi dokokin Allah?

14 Amma don ka taimaka wa yaranka su kasance da bangaskiya, ba za ka riƙa gaya musu abin da ke nagarta da mugunta kawai ba. Kana bukatar ka taimaka musu su yi tunani a kan waɗannan tambayoyi: ‘Me ya sa Littafi Mai Tsarki ya hana yin wasu abubuwan da muke so? Mene ne ya tabbatar min cewa bin ƙa’idodin Littafi Mai Tsarki ya fi kyau?’​—Isha. 48:​17, 18.

15 Idan yaronka yana son ya yi baftisma, ka taimaka masa ya yi tunani sosai a kan hakkin da ke tattare da yin baftisma.  Wace albarka mutum zai samu idan ya yi baftisma? Wace sadaukarwa ce zai yi? Me ya sa albarkar yin hakan ta fi sadaukarwar? (Mar. 10:​29, 30) Saboda haka, yana da muhimmanci mutum ya yi tunani sosai a kan waɗannan tambayoyin kafin ya yi baftisma. Yara za su tabbata da abin da suka yi imani da shi idan aka taimaka musu su yi bimbini sosai a kan albarkar yin biyayya da kuma mugun sakamakon rashin biyayya. Hakan zai taimaka musu su ga cewa bin ƙa’idodin Littafi Mai Tsarki ya fi kyau a kowane lokaci.​K. Sha. 30:​19, 20.

SA’AD DA MATASHIN DA YA YI BAFTISMA YAKE FAMA

16. Mene ne iyaye za su yi idan yaronsu da ya yi baftisma ya soma yin sanyi a bautarsa ga Jehobah?

16 Mene ne za ka yi idan yaronka ya soma shakkar koyarwar Littafi Mai Tsarki bayan ya yi baftisma? Alal misali, yaronka yana iya soma sha’awar abin duniya ko kuma ya daina ganin muhimmancin bin ƙa’idodin Littafi Mai Tsarki. (Zab. 73:​1-3, 12, 13) Yadda iyaye suka bi da yanayin zai iya sa yaron ya ci gaba da bauta wa Jehobah ko kuma ya ƙi yin hakan. Ka yi ƙoƙari kada ka yi wa yaronka faɗa a kan wannan batun. Maimakon haka, ka tabbatar masa da cewa kana ƙaunarsa kuma kana son ka taimaka masa.

17, 18. Idan matashi yana shakka, ta yaya iyaye za su taimaka masa?

17 Hakika, kafin matashi ya yi baftisma, ya yi alkawarin bauta wa Jehobah. Ta yin hakan ya yi alkawari cewa zai riƙa ƙaunar Allah kuma ya sa hidimarsa ga Jehobah a kan gaba. (Karanta Markus 12:30.) Jehobah yana ɗaukan hakan da muhimmanci sosai kuma ya kamata mu ma mu ɗauke shi hakan. (M. Wa. 5:​4, 5) A lokacin da ya dace kuma a hankali, ka tuna wa yaronka waɗannan abubuwan. Amma kafin ka yi hakan, ka yi amfani da abubuwan da ƙungiyar Jehobah ta yi tanadinsu don ka taimaka wa yaronka ya san cewa yin alkawarin bauta wa Jehobah da kuma baftisma suna da muhimmanci sosai. Ban da haka, wannan matakin zai sa ya sami albarka ba kaɗan ba.

18 Alal misali, za ka samu shawara mai kyau a fihirisa mai jigo “Questions Parents Ask,” a bangon baya na Littafi na 1 na Questions Young People Ask​—Answers That Work. A wurin an ce: “Kada ka yi saurin kammala cewa yaronka ya ƙi bauta wa Jehobah. A yawancin lokaci, akwai dalilin da ya sa ya yi hakan.” Yana iya zama cewa abokansa suna matsa masa ya yi abubuwan da ba su dace ba. Wataƙila yana ganin ya kaɗaita ko kuma yana jin cewa wasu matasa sun fi shi ƙwazo. An kuma bayyana a fihirisar cewa waɗannan abubuwan ba sa nufin cewa yaronka ya ƙi imaninka. Maimakon haka, yana yin hakan ne don wasu matsaloli da yake fuskanta. A fihirisar an ba da shawarwari a kan yadda iyaye za su taimaka wa matashin da yake shakkar koyarwar Littafi Mai Tsarki.

19. Ta yaya iyaye za su taimaka wa yaransu su zama masu ‘hikima’ don samun ceto?

19 Iyaye suna da hakki da gata mai muhimmanci na renon yaransu cikin “horon Ubangiji da gargaɗinsa.” (Afis. 6:4) Kamar yadda muka koya, hakan ya ƙunshi koya musu abin da ke cikin Littafi Mai Tsarki da kuma taimaka musu su tabbata da abin da suka yi imani da shi. Idan suna da bangaskiya sosai, hakan zai sa su yi alkawarin bauta wa Jehobah da dukan zuciyarsu. Bari Kalmar Jehobah da ruhunsa da ƙoƙarce-ƙoƙarcen iyaye su iya taimaka wa yara su zama masu ‘hikima’ don samun ceto.

^ sakin layi na 9 Umurni don nazari da ke “Mene ne Littafi Mai Tsarki Yake Koyarwa?” zai taimaka wa matasa da manya su fahimci kuma su iya bayyana ma wasu koyarwar Littafi Mai Tsarki. Za ka ga wannan a harsuna da yawa a dandalin jw.org/ha. Ka duba KOYARWAR LITTAFI MAI TSARKI > ABUBUWAN NAZARIN LITTAFI MAI TSARKI.