Koma ka ga abin da ke ciki

Koma ga abubuwan da ke ciki

Kusan dukan addinai sun yi imani cewa kurwar ‘yan Adam ba ta mutuwa

 ABIN DA KE SHAFIN FARKO | ME LITTAFI MAI TSARKI YA CE GAME DA RAI DA MUTUWA?

Tambaya Mai Ban Mamaki

Tambaya Mai Ban Mamaki

MUTANE suna da ra’ayoyi da yawa game da rayuwar ʼyan Adam da kuma mutuwa. Wasu sun yi imani cewa bayan sun mutu, za su ci gaba da rayuwa a wani wuri ko kuma su zama wani abu dabam. Wasu sun ce za a sake haifansu don su sake rayuwa. Wasu kuma sun ce mutuwa ce ƙarshen ʼyan Adam.

Wataƙila abin da ka yi imani da shi dabam ne saboda al’adarka. Tun da mutane suna da ra’ayoyi dabam-dabam a kan wannan batun, shin da akwai abin da zai taimaka mana mu san gaskiyar al’amarin?

Limaman addinai sun daɗe sosai suna koya wa mutane cewa wani abu a jikin mutum yana ci gaba da rayuwa bayan mutuwa. Kusan dukan addinai kamar Kiristoci da Hindu da Yahudawa da Musulmai da dai sauransu sun yi imani da hakan. Amma ’yan Buddha sun yi imani cewa za a ci gaba da haifan mutum har sai tunaninsa ko kuma motsin ransa ya koma wani wurin da ake kira Nirvana.

Waɗannan koyarwar sun sa yawancin mutane a duniya sun yi imani cewa idan mutum ya mutu, zai ci gaba da rayuwa a wani wuri. Mutane da yawa sun yi imani cewa mutuwa tana da muhimmanci sosai a rayuwar ’yan Adam. Sun kuma ce mutuwa nufin Allah ne. Amma mene ne Littafi Mai Tsarki ya ce game da wannan batun? Don Allah, ka karanta talifi na gaba. Abin da ke ciki yana da ban mamaki.