Koma ka ga abin da ke ciki

Koma ga abubuwan da ke ciki

Baƙaƙe huɗu da ke wakiltar sunan Allah, Jehobah. A Ibrananci ana karanta shi daga hannun dama zuwa hagu

Baki ta Ibrananci Mai Ban Karfafa

Baki ta Ibrananci Mai Ban Karfafa

Shin za mu iya kasancewa da tabbaci cewa dukan alkawuran Allah za su cika? Yesu ma ya tabbata da hakan kuma koyarwarsa ta taimaka wa mabiyansa su gaskata da hakan. Ka yi la’akari da misalin da ya bayar sa’ad da yake Huɗuba a kan Dutse da aka rubuta a Matta 5:18. Ya ce: “Gaskiya fa nike faɗa maku, har sama da duniya su shuɗe, ko wasali ɗaya ko ɗigo ɗaya ba za ya shuɗe daga Attaurat ba, sai dukan abu ya cika.”

Harafi mafi ƙanƙanta a cikin baƙaƙen Ibrananci shi ne י (yod), kuma shi ne harafi na farko a cikin baƙaƙe huɗu da ke wakiltar sunan Allah, wato Jehobah. * Ban da asalin kalamai da kuma harufan da ke cikin Dokar Allah, marubuta da Farisiyawa suna ɗaukan kowane “ɗigo” da muhimmanci sosai.

Yesu yana nufin cewa sama da ƙasa za su iya shuɗewa, amma alkawuran Allah ba za su taɓa ƙin cika ba. Littafi Mai Tsarki ya tabbatar mana da cewa sama da kuma duniya za su dawwama har abada. (Zabura 78:69) Saboda haka, kalaman nan sun nuna cewa dukan alkawuran da ke cikin Dokar da aka ba Musa za su cika.

Jehobah yana ɗaukan ƙananan bayanai da muhimmanci kuwa? Ƙwarai kuwa. Alal misali, an umurci Isra’ilawa cewa kada su karya ƙashin ragon da za su yanka a Idin Ƙetarewa. (Fitowa 12:46) Ko da yake wannan ƙaramin bayani ne, amma shin Isra’ilawan sun san dalilin da ya sa aka ce su yi hakan? Da kyar. Amma Jehobah ya san cewa hakan na nuna cewa ba za a karya ƙashin Almasihu ba sa’ad da aka kashe shi a kan gungumen azaba.​—Zabura 34:20; Yohanna 19:​31-33, 36.

Mene ne kalaman Yesu suka koya mana? Mu ma za mu iya gaskata cewa Allah zai cika dukan alkawuran da ya yi. Hakika harafi mafi ƙanƙanta a cikin baƙaƙen Ibranancin nan abin ban ƙarfafa ne!

^ sakin layi na 3 A cikin baƙaƙen Helenanci, harafi mafi ƙanƙanta shi ne iota kuma yana nufin abu ɗaya da na Ibrananci nan י (yod). Tun da yake da Ibrananci ne aka rubuta Dokar da aka ba Musa, wataƙila Yesu yana magana ne a kan harafi na Ibrananci.