Koma ka ga abin da ke ciki

Koma ga abubuwan da ke ciki

Sa’ad da Ka Gaji da Rayuwa

Sa’ad da Ka Gaji da Rayuwa

Adriana daga ƙasar Birazil ta ce: “Na yi ta tunani a kan irin wahalar da nake sha, hakan ya sa na so in kashe kaina don in huta.”

KA TAƁA yin baƙin ciki sosai har ka yi tunanin cewa gwamma ka mutu don ka huta? Idan haka ne, za ka fahimci yadda Adriana ta ji. Ta yi fama da ciwon ɓacin zuciya. Don haka, a kullum ba ta farin ciki balle ta kasance da bege.

Ka yi la’akari kuma da Kaoru daga ƙasar Jafan wadda ya kula da iyayensa tsofaffi da suke ciwo. Ya ce: “Akwai lokacin da nake aiki tuƙuru kuma ba na iya cin abinci sosai balle ma in sami isashen barci. Na gaji da rayuwa, sai na soma tunanin cewa idan na mutu, zan huta da kome.”

Wani mutum mai suna Ojebode a Najeriya ya ce: “Ina baƙin ciki a kullum har in riƙa zub da hawaye. Don haka, na yi ƙoƙarin kashe kaina don in huta.” Abin farin ciki shi ne Ojebode da Kaoru da kuma Adriana ba su kashe kansu ba. Amma a kowace shekara, dubban mutane sukan kashe kansu.

ABIN DA ZAI TAIMAKA MANA

Yawancin mutanen da suke kashe kansu mazaje ne da suke jin kunyar neman taimako. Yesu ya ce marasa lafiya suna bukatar jinya. (Luka 5:31) Don haka, idan kana baƙin ciki sosai kuma kana tunanin kashe kanka, don Allah kar ka ji kunya, ka nemi taimakon wasu. Mutane da yawa da suke fama da ciwon ɓacin zuciya sun gano cewa zuwa asibiti don neman magani ya taimaka musu sosai. Mutanen da muka ambata a baya wato, Ojebode da Kaoru da kuma Adriana sun je asibiti don neman magani kuma yanzu sun sami sauƙi.

Likitoci suna iya ba ka magani ko kuma su tattauna da kai don ka sami sauƙi. Waɗanda suke fama da ciwon ɓacin zuciya suna bukatar haƙuri da kulawa daga iyalinsu da kuma abokansu. Babban amininmu shi ne Jehobah kuma yana taimaka mana ta wurin Kalmarsa Littafi Mai Tsarki.

ZA A DAINA BAƘIN CIKI HAR ABADA KUWA?

Waɗanda suke fama da ciwon ɓacin zuciya suna bukatar jinya na dogon lokaci. Kuma don su iya jimrewa, suna bukatar su yi wasu gyara a salon rayuwarsu. Idan kana fama da ciwon ɓacin zuciya, za ka iya sa zuciya a kan abubuwa masu kyau da suke jiranmu a nan gaba kamar yadda Ojebode ya yi. Ya ce: “Ina marmarin ganin lokacin da littafin Ishaya 33:24 zai cika, da ya ce wanda yake zaune a ƙasar ba zai ‘ƙara yin kukan yana ciwo’ ba.” Kamar Ojebode, muna son mu sami ƙarfafa daga alkawarin Allah na “sabuwar ƙasa,” wurin da babu “azaba.” (Ru’uyar da Aka Yi wa Yohanna 21:​1, 4) Wannan alkawarin ya nuna cewa ba za a sake yin wani baƙin ciki ko ɓacin zuciya ba. Ba za ka ƙara shan wahala ba. Ƙari ga haka, ba za ka ƙara “tunawa da abubuwan dā ba tunaninsu ma ba zai zo” zuciyarka ba.​—Ishaya 65:17.