Koma ka ga abin da ke ciki

Koma ga abubuwan da ke ciki

Yaya Halayen Allah Suke?

Yaya Halayen Allah Suke?

Idan muka san halayen mutum, za mu kusace shi sosai kuma abokantakarmu za ta yi ƙarfi. Haka ma yake da Jehobah, idan muka san halayensa, za mu ƙarfafa dangantakarmu da shi. Halayen Allah guda huɗu da suka fi muhimmanci su ne, iko da hikima da adalci da kuma ƙauna.

ALLAH YANA DA IKO

“Ya Ubangiji Yahweh, kai ne ka yi sama da duniya ta wurin hannunka mai iko.”​IRMIYA 32:17.

Muna ganin tabbacin cewa Allah yana da iko ta wurin halittunsa. Alal misali, idan ka tsaya a rana, za ka ji zafi, ko ba haka ba? Hakan ya nuna cewa kana ganin tabbacin ikon Jehobah a halittunsa. Yaya zafin rana yake? Idan ruwa ya tafasa, zafinsa yana kai maki 100 a ma’aunin salshiyas. Amma idan rana ta yi zafi sosai, za ta ninka zafin tafasashen ruwa har sau dubu ɗari da hamsin. A kowace sakan, rana tana fid da zafi da ya yi daidai da miliyoyin boma-boman nukiliya.

Duk da haka, rana ƙarama ce idan aka gwada ta da miliyoyin taurarin da muke da su a sararin samaniya. Masanan kimiyya sun ce ɗaya daga cikin tauraruwa mafi girma mai suna UY Scuti tana da girman da ta ninka rana wajen sau 1,700. Idan UY Scuti ta maye gurbin rana, za ta rufe duniyarmu har ta wuce duniya ta biyar da ake kira Jufita. Wataƙila hakan zai taimaka mana mu fahimci abin da Irmiya ya faɗa cewa Jehobah ne ya halicci sama da ƙasa da girman ikonsa.

Ta yaya muke amfana daga ikon Allah? Rayuwarmu ta dangana ne ga halittun Allah da muke gani, kamar su rana da dukan wasu abubuwa masu ban mamaki. Ƙari ga haka, Allah yana amfani da ikonsa don ’yan Adam su amfana. Ta yaya? A ƙarni na farko, Allah ya ba wa Yesu iko don ya yi ayyuka masu ban al’ajabi. Littafi Mai Tsarki ya ce: “Makafi suna samun gani, guragu suna tafiya, masu cutar fatar jiki suna samun tsabtacewa, kurame suna jin magana, ana ta da waɗanda suka mutu.” (Matiyu 11:5) A yau kuma fa? Littafi Mai Tsarki ya ce: “Ga mai gajiya, yana ƙarfafa shi.” Kuma ya ƙara da cewa: “Masu sa zuciya ga Yahweh za a sabonta ƙarfinsu.” (Ishaya 40:​29, 31) Allah zai ba mu “cikakken ikon da ya fi duka” don ya taimaka mana mu iya jimre matsalolin rayuwa. (2 Korintiyawa 4:7) Shin ba za ka so ka kusace Allah da yake amfani da ikonsa don ya taimaka mana ba?

ALLAH YANA DA HIKIMA

“Ya Yahweh, ina misalin yawan ayyukanka, cikin hikima ka yi su duka!”​ZABURA 104:24.

Idan muka bincika abubuwan da Allah ya halitta, za mu yi mamaki sosai saboda hikimarsa. Akwai wani bincike da ’yan kimiyya suke yi da ake kira, biomimetics ko biomimicry, da a kan bincika abubuwan da Allah ya halitta, sai a bi tsarin kuma a ƙera abubuwa masu sauƙi da masu wuya kamar su jirgin sama da dai sauransu.

Yadda aka tsara idon mutum yana nuna irin hikimar da Allah yake da shi

Inda ake ganin hikimar Allah sosai shi ne yadda aka tsara jikin ’yan Adam. Ka yi la’akari da yadda ake haifan mutum. Hakan na somawa ne da ƙwayar halitta guda ɗaya, kuma wannan ƙwayar halittar tana ɗauke da dukan bayanai game da halin mutum. Ƙwayar takan raba kanta zuwa ƙwayoyi da yawa da suka yi kama da juna. Amma a lokacin da ya dace, sai ƙwayoyin jikin su soma raba kansu zuwa ɗarurruwan ƙwayoyi na musamman kamar su ƙwayoyin jini da na jijiyoyi da kuma na ƙashi. Nan da nan sai gaɓoɓin jiki su soma fitowa kuma su soma aiki. A cikin wata tara, sai wannan ƙwayar ta zama jariri da ya ƙunshi biliyoyin ƙwayoyin halitta. Irin wannan hikimar ce ta sa mutane da yawa suka amince da marubucin Littafi Mai Tsarki da ya ce: “Ina yabonka, domin yadda ka harhaɗa ni abin tsoro da ban mamaki ne.”​—Zabura 139:14.

Ta yaya muke amfana daga hikimar Allah? Mahaliccinmu ya san abin da muke bukata don mu ji daɗin rayuwa. Daga cikin hikimarsa da fahiminsa ne yake ba mu shawara a Kalmarsa Littafi Mai Tsarki. Alal misali, Littafi Mai Tsarki ya ce: “Kuna . . . gafarta wa juna.” (Kolosiyawa 3:13) Shin hakan shawara ce mai kyau? Hakika. Likitoci sun gano cewa idan muna gafarta wa juna, za mu riƙa barci da kyau kuma ba za mu kamu da hawan jini ba. Hakan yakan rage ciwon ɓacin zuciya da dai sauransu. Allah yana kama da aboki mai hikima da a kullum yakan ba da shawara mai kyau. (2 Timoti 3:​16, 17) Shin ba za ka so ka samu irin wannan aminin ba?

ALLAH MAI ADALCI NE

“Yahweh yana ƙaunar shari’ar gaskiya.”​ZABURA 37:28.

A kullum, Allah yana yin abin da ya dace. Hakika, “Allah ba zai taɓa aikata mugunta ba! A wurin Mai Iko Duka babu kuskure!” (Ayuba 34:10) Jehobah yana shari’a da adalci kamar yadda wani marubucin zabura ya ce: ‘Yana yi wa kabilu shari’ar gaskiya.’ (Zabura 67:4) Da yake “Yahweh yakan dubi zuciya ne,” ba za mu iya yaudararsa ba domin shi ya san gaskiyar kuma zai iya yin shari’a da adalci. (1 Sama’ila 16:7) Ban da haka ma, Allah yana sane da dukan rashin adalci da cin hanci da mutane suke yi a duniya kuma ya yi alkawari cewa nan ba da daɗewa ba, zai “kawar da mugaye daga ƙasar.”​—Karin Magana 2:22.

Amma hakan ba ya nuna cewa Allah mugu ne da yake son ya riƙa hukunta mutane. Yakan ji tausayin mutane a lokacin da ya dace. Littafi Mai Tsarki ya ce: “Yahweh mai jinƙai ne, mai alheri kuma,” har ga masu zunubi da suka tuba da gaske. Hakan bai nuna cewa shi mai adalci ba ne?​—Zabura 103:8; 2 Bitrus 3:9.

Ta yaya muke amfana daga adalcin Allah? Manzo Bitrus ya ce: “Allah ba ya nuna bambanci, amma yana karɓar duk mai tsoronsa da kuma mai aikata adalci a kowace al’umma.” (Ayyukan Manzanni 10:​34, 35) Muna amfana daga adalcin Allah don ba ya nuna son kai. Za mu iya kusantar Allah kuma mu bauta masa ko daga wace al’umma ko ƙasa muka fito. Ƙari ga haka, ko muna da kuɗi da ilimi ko ba mu da shi, za mu iya kusantar sa.

Da yake Allah ba ya son kai, muna iya kusantar sa ko daga wacce al’umma muka fito ko muna da kuɗi ko ba mu da kuɗi

Da yake Allah yana son mu fahimci adalcinsa kuma mu amfana daga hakan, ya ba mu lamiri. Nassosi sun kwatanta lamiri da doka da ke ‘rubuce cikin zukatanmu,’ da ke “shaida” ko abin da muke yi ya dace ko bai dace ba. (Romawa 2:15) Ta yaya muke amfana daga hakan? Idan muka horar da lamirinmu da kyau, za mu iya guje ma wasu abubuwan da ba su dace ba. Kuma idan muka yi kuskure, lamirinmu zai iya sa mu tuba kuma mu gyara halayenmu. Hakika, sanin adalcin Allah yana taimaka mana mu kusace shi, ko ba haka ba?

ALLAH ƘAUNA NE

“Allah ƙauna ne.”​1 YOHANNA 4:8.

Allah yana da iko da hikima da kuma adalci, amma Littafi Mai Tsarki bai ce Allah iko ne ko hikima ko kuma adalci ba. Abin da ya faɗa shi ne, Allah ƙauna ne. Me ya sa? Domin ikon Allah ne yake sa ya yi wani abu, adalcinsa da hikimarsa ne suke ja-goranci yadda yake yin abin. Amma ƙauna ce take motsa shi ya ɗauki matakin yin abin tun daga farko. Hakika, ƙauna ce take motsa Allah ya yi duk wani abin da yake so ya yi.

Ko da yake Jehobah bai rasa kome ba, amma ƙauna ce ta motsa shi ya yi halittu masu basira da ke sama da duniya don su ji daɗin rayuwa da kuma kulawarsa. Ya shirya duniyar nan don mutane su ji daɗin rayuwa a cikinta. Kuma ya ci gaba da kula da dukan mutane, shi ya sa “yake sa rana ta yi haske a kan masu kirki da marasa kirki ma, ya kuma aiko ruwan sama a kan masu adalci da marasa adalci.”​—Matiyu 5:45.

Ƙari ga haka, “Ubangiji mai jinƙai ne, mai yawan tausayi.” (Yaƙub 5:11) Yana ƙaunar waɗanda suka ɗauki matakin koya game shi da kuma kusace shi. Allah yana lura da kowanne ɗayansu. Babu shakka, ‘shi ne mai lura da kai.’​1 Bitrus 5:7.

Ta yaya muke amfana daga ƙaunar Allah? Muna ganin kyan halittun Allah idan yamma ta yi. Kuma muna jin daɗin ganin yadda jarirai suke dariya. Ban da haka ma, muna jin daɗin zumunci da danginmu na kurkusa. Za mu iya ganin cewa waɗannan abubuwan ba su da muhimmanci, amma suna sa mu ji daɗin rayuwa.

Muna kuma amfana daga addu’a wadda ita ma wata hanya ce da Jehobah yake nuna mana ƙauna. Littafi Mai Tsarki ya ce: “Kada ku damu da kome, sai dai a cikin kome ku faɗa wa Allah bukatunku ta wurin addu’a da roƙo, tare da godiya.” Kamar yadda mahaifi mai ƙauna yake yi, Jehobah yana son mu nemi taimakonsa idan muna cikin matsala. Don ya yi alkawari cewa zai tanadar mana da ‘salama irin wadda ta wuce dukan ganewar ɗan Adam.’​—Filibiyawa 4:​6, 7.

Shin wannan tattaunawar da muka yi game da halayen Allah, wato ikonsa da hikimarsa da adalcinsa da kuma ƙaunarsa ba su taimaka maka ka fahimci yadda Allah yake ba? Don ka ƙara sanin halayen Allah, muna son ka koyi abubuwan da ya yi da kuma waɗanda zai yi da za su amfane ka.

YAYA HALAYEN ALLAH SUKE? Jehobah mai iko ne da hikima da kuma adalci. Amma ƙauna ce ta fi muhimmanci a cikin halayensa duka