Koma ka ga abin da ke ciki

Koma ga abubuwan da ke ciki

Yadda Za Ka Amfana Idan Ka Koya Game da Allah

Yadda Za Ka Amfana Idan Ka Koya Game da Allah

Tun daga farkon mujallar nan, mun koyi abubuwa da suka amsa tambayar nan, Zai Yiwu Ka San Allah Kuwa? Mun fara da sanin sunansa a cikin Littafi Mai Tsarki da kuma halinsa mafi muhimmanci, wato ƙauna. Mun kuma koyi abubuwan da ya yi a dā da waɗanda zai yi a nan gaba don mutane su amfana. Ko da yake akwai abubuwa da yawa da za ka koya game da Allah, amma kana iya tunanin wane amfani za ka samu idan ka koya game da shi.

Jehobah ya ce “Idan ka neme shi, zai sa ka same shi.” (1 Tarihi 28:9) Idan ka koyi abubuwa game da Allah, za ka kasance da dangataka mai kyau da shi kuma zai “amince” da kai, hakan babban gata ne! (Zabura 25:​14, Littafi Mai Tsarki) Ta yaya za ka amfana daga hakan?

Za ka yi farin ciki sosai. Littafi Mai Tsarki ya ce Jehobah “Allah mai albarka” ko kuma mai farin ciki ne. (1 Timoti 1:11) Za ka yi farin ciki sosai a rayuwa idan ka kusace shi kuma ka koyi halayensa. (Zabura 33:12) Za ka guji yin abubuwan da za su ɓata rayuwarka, ka kuma kasance da halaye masu kyau da kuma dangantaka mai kyau da mutane. Za ka amince da abin da marubucin Zabura ya faɗa cewa: “A gare ni, ya fi mini kyau, in kasance kusa da Allah.”​—Zabura 73:​28, LMT.

Zai kula da kai sosai. Jehobah ya yi alkawari ga duk wanda yake bauta masa cewa: “Zan ba ka shawara, ba zan cire idona a kanka ba.” (Zabura 32:8) Hakan na nufin cewa Jehobah yana kula da bayinsa sosai kuma yana biyan bukatun kowannensu. (Zabura 139:​1, 2) Jehobah zai kasance tare da kai idan har ka soma ƙulla dangantaka mai kyau da shi.

Za ka kasance da bege mai kyau. Ban da farin ciki da kuma rayuwa mai kyau da za ka yi a yanzu, za ka kasance da bege mai kyau a nan gaba. (Ishaya 48:​17, 18) Littafi Mai Tsarki ya ce: “Rai na har abada kuwa shi ne, mutane su san ka, kai da kake Allah makaɗaici na gaskiya, su kuma san Yesu Almasihu wanda ka aiko.” (Yohanna 17:3) A wannan zamani mai wuya da muke ciki, begen da Allah ya ba mu zai taimaka mana kada mu ‘ji tsoro ko mu yi shakka.’​—Ibraniyawa 6:19.

Waɗannan abubuwan da muka ambata kaɗan ne daga cikin muhimman dalilai da suka sa ya kamata mu san Allah kuma mu zama aminansa. Za ka iya tattaunawa da duk Mashaidin Jehobah da ka haɗu da shi ko kuma ka shiga dandalinmu na jw.org/ha don ka samu ƙarin bayani.