Koma ka ga abin da ke ciki

Koma ga abubuwan da ke ciki

Koyarwar Littafi Mai Tsarki Tana da Amfani a Koyaushe

Koyarwar Littafi Mai Tsarki Tana da Amfani a Koyaushe

KA YI TUNANI: A ce ka je yawon buɗe ido a ma’adanar kayayyakin tarihi. Yawancin kayayyakin sun tsufa, wasu ma sun lalace. Har ila wasu siffofin gaɓaɓuwansu sun ɓalle. Amma akwai wanda gaɓaɓuwarsa ba su ɓalle ba, yana nan da kyaunsa. Sai ka tambayi wanda yake kai ka zagaya cewa: “Wannan bai daɗe kamar sauran ba ko?” Sai ya ce maka: “Ya fi sauran jimawa kuma ba a taɓa masa kwaskwarima ba.” Sai ka ce: “An rufe shi da wani abu ne don kada ya lalace?” Mai zagayan ya ce: “Ai wannan da kake gani ya sha kura sosai har da ruwan sama. Kuma mutane da yawa sun so su lalatar da shi, amma yana nan da kyansa.” Wataƙila ka yi mamaki sosai kuma kana ta tunani, ‘Wai da me aka yi wannan sifar?’

Hakazalika, Littafi Mai Tsarki yana kama da wannan siffar. Littafi ne da ya daɗe sosai kuma ya fi yawancin littattafai shekaru. Ko da yake akwai wasu littattafai da aka rubuta a dā, yawancinsu sun lalace kuma abin da yake ciki ba su da amfani kamar yadda aka lalatar da wasu siffofin da muka ambata a baya. Abin da littattafan suka faɗa game da kimiyya bai jitu da abubuwan da masana suka gano a yanzu ba. Kuma idan aka bi shawarar da suka bayar game da jinya a yawancin lokaci, hakan zai zama da haɗari. Ban da haka ma, wasu shafuffukan littattafan dā da yawa sun lalace sosai.

Amma Littafi Mai Tsarki ya bambanta da sauran littattafai. An soma rubuta shi ƙarnuka 35 da suka shige, amma har ila Littafi Mai Tsarki yana nan yadda yake. A shekarun baya, mutane sun yi ƙoƙarin su ƙona shi, su hana karanta shi kuma su ɓoye muhimmancinsa, amma ba su yi nasara ba sam. Ƙari ga haka, Littafi Mai Tsarki ya faɗi wasu abubuwan da za su faru a nan gaba.​—Ka duba akwatin nan “Shin Littafi Mai Tsarki Ya Tsufa Ko Kuwa Yana Faɗin Abin da Zai Faru?

ƘA’IDODIN DA MUKE BUKATA

Amma za ka iya yin tunani, ‘Shin shawarar Littafi Mai Tsarki tana da amfani a wannan zamanin?’ Don ka sami amsar, yanzu ka tambayi kanka: ‘Waɗanne irin matsaloli ne mutane suke fuskanta a duniya yanzu? Wanne ne ya fi sa mutane tsoro?’ Wataƙila kana tunanin yaƙi ko gurɓatar mahalli ko ta’addanci ko kuma cin hanci da rashawa. Yanzu bari mu bincika wasu ƙa’idodin Littafi Mai Tsarki. Yayin da muke yin hakan, ka tambayi kanka, ‘Idan mutane suka bi waɗannan ƙa’idodin, shin ba za a yi zaman lafiya a duniya ba?’

SON ZAMAN LAFIYA

“Albarka tā tabbata ga masu ƙulla zumunci, domin za a ce da su ’ya’yan Allah.” (Matta 5:​9, Littafi Mai Tsarki) ‘Idan ya yiwu, ku zauna lafiya da dukan mutane, gwargwadon iyawarku.’​—Romawa 12:18.

JIN ƘAI DA GAFARTAWA

“Masu-albarka ne masu-jinƙai: gama su za su sami jinƙai.” (Matta 5:7) ‘Ku riƙa haƙuri da juna, kuna gafarta ma juna, idan kowane mutum yana da maganar ƙara game da wani; kamar yadda Jehobah * ya gafarta maku, haka nan kuma sai ku yi.’​—Kolosiyawa 3:13.

HAƊIN KAI

Allah “ya yi dukan al’umman mutane da za su zauna bisa . . . duniya.” (Ayyukan Manzanni 17:26) “Allah ba ya tara, amma a kowace al’umma duk mai tsoronsa, mai kuma aikata adalci, abin karɓuwa ne a gare shi.”​—Ayyukan Manzanni 10:​34, 35.

DARAJA DUNIYA

“Ubangiji ya ɗauki mutumin ya zaunar da shi cikin gonar Aidan ya noma ta, ya kiyaye ta.” (Farawa 2:​15, LMT) Allah zai “hallaka waɗanda ke hallaka duniya.”​—Ru’ya ta Yohanna 11:18.

ƘIN HAƊAMA DA LALATA

“Ku yi lura, ku tsare kanku daga dukan ƙyashi: gama ba da yalwar dukiya da mutum yake da ita ransa ke tsayawa ba.” (Luka 12:15) “Amma fasikanci, da dukan ƙazanta, ko sha’awa, kada a ko ambata a cikinku, gama haka ya kamata ga tsarkaka.”​—Afisawa 5:3.

FAƊIN GASKIYA DA KUMA AIKI

“Muna kuwa so mu tafiyar da al’amuranmu da [“gaskiya,” NW ].” (Ibraniyawa 13:​18, LMT) “Mai yin sata kada ya ƙara yin sata: amma gwamma ya yi aiki.”​—Afisawa 4:28.

MUHIMMANCIN TAIMAKA MA WAƊANDA SUKE BUKATAR TAIMAKO

“Ku ƙarfafa masu-raunanan zukata, ku tokare marasa-ƙarfi, ku yi haƙuri da kowa.” (1 Tasalonikawa 5:14) “Mutum ya ziyarci marayu da gwauraye cikin ƙuncinsu.”​—Yaƙub 1:27.

Ba wai kawai Littafi Mai Tsarki ya ambaci waɗannan ƙa’idodin ba. Amma yana son mu bi waɗannan ƙa’idodin a harkokinmu na yau da kullum. Idan mutane suka yi amfani da waɗannan abubuwan da muka ambata, matsalolin duniya ba za su ragu ba? Babu shakka, shawarar Littafi Mai Tsarki tana da muhimmanci yanzu fiye da dā! To, ta yaya koyarwar Littafi Mai Tsarki za ta iya taimaka maka?

YADDA KOYARWAR LITTAFI MAI TSARKI ZA TA TAIMAKA MAKA

Wani mai hikima ya ce: ‘Hikima ta aikinta ne ake tabbatar da gaskiyarta.’ (Matta 11:​19, LMT) Ka amince da hakan? Za a san mutum mai hikima idan ya yi ayyukan da suka nuna hakan. Don haka, za ka iya tunani, Idan Littafi Mai Tsarki yana da amfani har yanzu, shin ba zan amfana ba idan na bi shawarar da ke ciki? Ta yaya zai taimaka mini in shawo kan matsalolin da nake fuskanta? Bari mu bincika wani labari.

Wata mata mai suna Delphine, * tana aiki kuma tana jin daɗin rayuwa. Sai kwatsam, ta yi hasarar duka abin da take da shi kuma ta soma shan wahala. ’Yarta matashiya ta rasu kuma ita da mijinta sun rabu. Bayan haka, sai ta talauce. Ta ce: “Rayuwata ta dāgule gabaki ɗaya. Na rasa ’ya, ba ni da miji da kuma gida. Na ji kamar ba ni da wani amfani don na yi sanyin gwiwa kuma ba ni da wani bege.”

A wannan lokacin ne Delphine ta ga muhimmancin furucin nan: “Tsawon kwanakin ranmu duka aƙalla shekara ce saba’in, in kuwa muna da ƙarfi, shekara tamanin ne. Duk da haka iyakar abin da waɗannan shekaru suke kawo mana, damuwa ce da wahala, nan da nan sukan wuce, tamu ta ƙare.”​—Zabura 90:​10, LMT.

Ƙa’idodin Littafi Mai Tsarki sun taimaka wa Delphine sosai a lokacin da take bukatar ƙarfafawa. Kamar yadda za mu bincika a talifofi uku na gaba, ƙa’idodin Littafi Mai Tsarki sun taimaka wa mutane da yawa sa’ad da suka yi amfani da su a lokacin da suke fuskantar matsaloli. Sun fahimci cewa Littafi Mai Tsarki yana kama da siffar da muka ambata a baya da ta daɗe amma ba ta lalace ba. Littafi Mai Tsarki ba kamar wasu littattafai da yawa da suka tsufa kuma suka zama tsohon yayi ba ne. Shin littafin ya daɗe don an yi shi da wani irin abu na musamman ne? Da gaske Kalmar Allah ce a ciki ba ra’ayoyin mutane ba?​—1 Tasalonikawa 2:13.

Wataƙila kai ma ka gane cewa rayuwa ba ta da tsawo kuma mutane suna fama da matsaloli. Idan kana fama da matsaloli sosai, a ina za ka sami ƙarfafa da taimako da kuma shawarar da ta dace?

Bari mu bincika hanyoyi uku masu muhimmanci da Littafi Mai Tsarki zai taimaka mana a rayuwa. Zai koya maka yadda za ka

  1. guji matsaloli idan da hali.

  2. magance matsalolin da kake fuskanta.

  3. jimre matsalolin da ba za ka iya magance wa ba.

Talifofin da za mu bincika a gaba za su tattauna waɗannan hanyoyi ukun.

^ sakin layi na 10 Littafi Mai Tsarki ya koyar da cewa Jehobah shi ne sunan Allah.​—Zabura 83:18.

^ sakin layi na 24 An canja sunaye a wannan talifin da kuma talifofi uku na gaba.