Koma ka ga abin da ke ciki

Koma ga abubuwan da ke ciki

HASUMIYAR TSARO Na 1 2018 | Littafi Mai Tsarki Yana da Amfani a Yau?

LITTAFI MAI TSARKI YANA DA AMFANI A YAU?

Tun da yake muna da bayanai da yawa game da fasaha, shin shawarar da ke Littafi Mai Tsarki tana da amfani har wa yau? Littafi Mai Tsarki ya ce:

“Kowane nassi hurarre daga wurin Allah, mai-amfani ne.”​—2 Timotawus 3:16.

Wannan mujallar Hasumiyar Tsaro ta bayyana yadda shawarar Littafi Mai Tsarki za ta iya taimaka mana a duk fannin rayuwa.

 

Shawarar Littafi Mai Tsarki Tana da Amfani Har wa Yau?

Tun da yanzu akwai bayani dabam-dabam da muke bukata, me ya sa za mu nemi taimako daga littafin da ya yi kusan shekaru 2,000 da tsufa?

Koyarwar Littafi Mai Tsarki Tana da Amfani a Koyaushe

Duka koyarwar Littafi mai tsarki suna da amfani a koyaushe.

Shin Littafi Mai Tsarki Ya Tsufa Ko Kuwa Yana Fadin Abin da Zai Faru?

Ko da yake Littafi Mai Tsarki ba littafin kimiyya ba ne amma yana fada abubuwa game da kimiyya da zai ba ka mamaki.

1 Zai Sa Ka Guji Matsaloli

Ka yi la’akari da yadda shawarar da ke Littafi Mai Tsarki ta taimaka wa mutane su guji matsalolin rayuwa.

2 Zai Sa Ka Magance Matsaloli

Littafi Mai Tsarki yana ba mu shawarwari game da matsaloli na rayuwa kamar yawan damuwa da rashin nutsuwa da kuma kadaici.

3 Zai Sa Ka Jimre da Matsaloli

Me za ka yi idan kana fuskantar matsaloli kamar mutuwa ko cuta mai tsanani da ba za ka iya magancewa ba ko guje wa ba?

Littafi Mai Tsarki Zai Kyautata Rayuwarka a Nan Gaba

Kalmar Allah za ta iya taimaka mana mu magance matsalolin yau da kullum a wannan duniyar. Ban da haka ma, Littafi Mai Tsarki yana ba mu bege yin rayuwa mai kyau a nan gaba.

Mene ne Ra’ayinka?

Ka bincika abin da wasu suka yi imani da shi da kuma abin da Littafi Mai Tsarki ya ce game da wannan tambayar.