Koma ka ga abin da ke ciki

Koma ga abubuwan da ke ciki

TALIFIN NAZARI NA 6

WAƘA TA 10 Mu Yabi Jehobah Allahnmu!

Mu Yabi Sunan Jehobah

Mu Yabi Sunan Jehobah

“Yabi Yahweh! Yabi Yahweh, ya ku bayinsa! Yabi Sunan Yahweh!”ZAB. 113:1.

ABIN DA ZA MU KOYA

Za mu ga abubuwan da suke sa mu yabi sunan Jehobah mai tsarki a duk lokacin da muka sami zarafi.

1-2. Me zai taimaka mana mu san yadda Jehobah yake ji game da yadda ake ɓata masa suna?

 A CE wani da kake ƙaunar sa sosai ya faɗi wani abu marar kyau game da kai. Ka san cewa abin da ya faɗa ƙarya ne, amma wasu mutane sun yarda da abin da ya faɗa. Ban da haka, su ma sun soma yaɗa ƙaryar, kuma mutane da yawa sun yarda da hakan. Yaya za ka ji? Idan kai mai son mutane ne kuma ba ka so a ɓata maka suna, ƙaryar da suke yi game da kai zai ɓata maka rai, ko ba haka ba?—K. Mag. 22:1.

2 Wannan misalin zai taimaka mana mu fahimci yadda Jehobah ya ji saꞌad da aka ɓata masa suna. Ɗaya daga cikin malaꞌikun da ya halitta ya yi wa Hauwaꞌu ƙarya game da Jehobah. Ta yarda da ƙaryar, kuma hakan ya sa ita da Adamu sun yi wa Jehobah tawaye. Hakan ya jawo ma dukan ꞌyan Adam zunubi da kuma mutuwa. (Far. 3:​1-6; Rom. 5:12) Ƙaryar da Shaiɗan ya yi a lambun Adnin ne ya jawo dukan matsalolin da muke fuskanta a yau, kamar mutuwa da yaƙe-yaƙe da kuma baƙin ciki. Shin Jehobah yana jin zafi a ransa saboda ƙaryar nan da kuma abin da ƙaryar take jawowa? Ƙwarai kuwa. Amma duk da haka, Jehobah bai riƙe abin a ransa ba. Littafi Mai Tsarki ya kira shi “Allah mai farin ciki.”—1 Tim. 1:​11, New World Translation.

3. Me za mu iya yi?

3 Za mu iya nuna cewa ƙarya ne Shaiɗan ya yi a kan Allah ta wajen bin umurnin da ke Zabura 113 aya 1, da ta ce mu “yabi Sunan Yahweh!” Za mu yabi sunan Jehobah idan muka gaya wa mutane abubuwa masu kyau game da shi. Za ka so ka yabi sunan Jehobah? Bari mu tattauna dalilai guda uku masu muhimmanci da za su iya sa mu yabi sunan Jehobah da dukan zuciyarmu.

JEHOBAH YANA FARIN CIKI IDAN MUKA YABI SUNANSA

4. Me ya sa Jehobah yake farin ciki idan muka yabe shi? Ka ba da misali. (Ka kuma duba hoton.)

4 Za mu sa Jehobah farin ciki idan muka yabi sunansa. (Zab. 119:108) Amma hakan yana nufin cewa Jehobah yana kamar ꞌyan Adam ne da suke so a yaba musu domin su sami ƙarfafa? Aꞌa. Ka yi laꞌakari da wannan misalin. A ce wata ƙaramar yarinya ta rungumi babanta kuma ta ce masa, “Babu baba irinka a duk duniya!” Baban zai yi murmushi kuma zai ji daɗi sosai. Kana ganin mutumin yana so ꞌyarsa ta yaba masa don ya sami ƙarfafa ne? Aꞌa. Ya yi farin ciki ne domin yana ƙaunar ꞌyarsa kuma ya ji daɗi da ta nuna cewa tana ƙaunar sa kuma tana godiya. Ya san cewa halayen nan za su sa ta farin ciki yayin da take girma. Dalilin da ya sa Jehobah, Uba da babu kamar sa yake farin ciki ke nan idan muka yabe shi.

Kamar yadda Uba yakan yi farin ciki idan ꞌyarsa ta nuna masa ƙauna kuma ta yaba masa, Jehobah ma yana farin ciki idan muka yabi sunansa (Ka duba sakin layi na 4)


5. Idan muka yabi sunan Jehobah, ta yaya hakan zai ƙaryata Shaiɗan?

5 Idan muka yabi Ubanmu na sama, muna taimaka wajen nuna cewa abin da Shaiɗan ya faɗa game da mu ƙarya ne. Shaiɗan ya ce babu ɗan Adam da zai goyi bayan Jehobah da gaske. Ya ce ba ko ɗayanmu da zai riƙe amincinsa idan ya fuskanci jarrabawa. Wato idan muka ga cewa daina bauta wa Allah zai amfane mu, dukanmu za mu daina bauta masa. (Ayu. 1:​9-11; 2:4) Amma Ayuba ya nuna cewa Shaiɗan maƙaryaci ne. Kai ma za ka riƙe amincinka ga Allah kamar Ayuba? Dukanmu za mu iya ɗaukaka Ubanmu na sama kuma mu sa shi farin ciki ta wurin bauta masa da aminci. (K. Mag. 27:11) Yin hakan babban gata ne.

6. Ta yaya za mu yi koyi da Sarki Dauda da kuma Lawiyawa? (Nehemiya 9:5)

6 Waɗanda suke ƙaunar Jehobah suna so su yabi sunansa da dukan zuciyarsu. Sarki Dauda ya ce: “Yabi Yahweh, ya raina! Dukan abin da ke a cikina, yabi Sunansa mai tsarki!” (Zab. 103:1) Dauda ya fahimci cewa yabon sunan Jehobah ɗaya yake da yabon Jehobah. Idan muka ji sunan Jehobah, mukan yi tunanin halayensa masu kyau da kuma abubuwan ban mamaki da ya yi. Dauda ya ɗauki sunan Ubansa na sama da tsarki kuma ya yabi sunan. Ya ce zai yi hakan da ‘dukan abin da ke a cikinsa,’ wato da dukan zuciyarsa. Lawiyawa ma sun ja-goranci mutane wajen yabon sunan Jehobah. Sun ce kalmomin bakinsu ba su isa su yabi Jehobah yadda ya dace ba. (Karanta Nehemiya 9:5.) Babu shakka, yadda suka yabi Jehobah da dukan zuciyarsu kuma suka yi hakan da sauƙin kai, ya sa Jehobah farin ciki.

7. Ta yaya za mu yabi Jehobah saꞌad da muke waꞌazi da kuma harkokinmu na yau da kullum?

7 A yau, za mu iya yabon Jehobah ta wajen gaya wa mutane abubuwa game da shi, wato abubuwan da za su nuna cewa muna ƙaunar sa kuma muna gode masa. Yayin da muke yin waꞌazi, zai dace mu tuna cewa burinmu shi ne mu taimaka wa mutane su yi kusa da Jehobah kuma su ɗauki Ubanmu mai ƙauna yadda muke ɗaukan sa. (Yak. 4:8) Muna farin cikin gaya wa mutane bayanin da Littafi Mai Tsarki ya yi game da Jehobah, wato cewa yana da ƙauna, da adalci, da hikima, da iko, da kuma wasu halaye masu kyau. Ban da haka, za mu yabi Jehobah kuma mu faranta masa rai idan muka yi koyi da shi. (Afis. 5:1) Idan mun yi hakan, mutane za su lura cewa mun yi dabam da mutanen muguwar duniyar nan, kuma za su so su san dalilin da ya sa. (Mat. 5:​14-16) Saꞌad da muke ayyukanmu na yau da kullum, za mu iya bayyana musu dalilin da ya sa muka yi dabam. Hakan zai sa mutane masu zuciyar kirki su yi kusa da Allah. Idan muka yabi Ubanmu na sama a wannan hanyar, za mu sa shi farin ciki.—1 Tim. 2:​3, 4.

YESU YANA FARIN CIKI IDAN MUKA YABI SUNAN JEHOBAH

8. Me ya nuna cewa Yesu ya fi kowa yabon Jehobah?

8 A cikin dukan halittun da ke sama da ƙasa, babu wanda ya san Jehobah kamar Yesu. (Mat. 11:27) Yesu yana ƙaunar Ubansa kuma ya yabi sunansa fiye da kowa. (Yoh. 14:31) A dare na ƙarshe kafin ya mutu, ya yi adduꞌa kuma ya ambaci abu mafi muhimmanci da ya cim-ma a hidimarsa a nan duniya. Ya ce: “Na kuma sanar musu da sunanka.” (Yoh. 17:​26, Tsohuwar Hausa a Sauƙaƙe) Ta yaya Yesu ya yi hakan?

9. Ta yaya Yesu ya yi amfani da kwatanci don ya bayyana halaye masu kyau da Ubansa yake da su?

9 Ba sunan Jehobah ne kawai Yesu ya gaya wa mutane ba. Yahudawan da Yesu ya koyar da su, sun riga sun san sunan Allah. Amma Yesu ne “wanda . . . ya bayyana mana shi” fiye da kowa. (Yoh. 1:​17, 18) Alal misali, Nassosin Ibrananci sun nuna mana cewa Jehobah yana da jin ƙai da kuma tausayi. (Fit. 34:​5-7) Amma Yesu ya taimaka mana mu ƙara fahimtar yadda Jehobah yake nuna halayen nan ta wurin kwatancin da ya yi game da ɗa mubazzari da kuma babansa. A duk lokacin da muka karanta yadda babansa ya gan sa “tun yana daga nesa,” da yadda ya gudu ya same shi, ya rungume shi, da yadda ya yafe masa da dukan zuciyarsa, hakan yana ƙara taimaka mana mu fahimci cewa Jehobah mai jin ƙai ne da kuma tausayi. (Luk. 15:​11-32) Yesu ya taimaka wa mutane su fahimci ainihin halayen Jehobah.

10. (a) Ta yaya muka san cewa Yesu ya yi amfani da sunan Ubansa kuma yana so mutane ma su yi hakan? (Markus 5:19) (Ka kuma duba hoton.) (b) Mene ne Yesu yake so mu yi a yau?

10 Shin Yesu yana so mutane su yi amfani da sunan Ubansa? Ƙwarai kuwa. Wasu malaman addinai a zamanin Yesu sun gaskata cewa reni ne mutum ya kira Allah da sunansa. Amma Yesu ya san cewa hakan bai jitu da nassosi ba. Don haka, bai daina yabon sunan Ubansa don abin da suke faɗa ba. Ka tuna lokacin da ya warkar da wani mutum mai aljanu a yankin Garasinawa. Mutanen sun ji tsoro sosai, sai suka roƙi Yesu cewa ya bar yankinsu. Don haka, ya bar yankin. (Mar. 5:​16, 17) Duk da haka, Yesu yana so mutanen yankin su san sunan Jehobah. Don haka, ya umurci mutumin ya gaya wa mutanen yankin abin da Jehobah ya yi masa, ba abin da shi Yesu ya yi ba. (Karanta Markus 5:19.) a Yesu yana so mu ma a yau mu gaya wa mutane game da sunan Ubansa a dukan faɗin duniya! (Mat. 24:14; 28:​19, 20) Idan muka yi hakan, za mu sa Sarkinmu, Yesu Kristi farin ciki.

Yesu ya umurci mutumin da ya cire masa aljanu ya gaya wa mutane yadda Jehobah ya taimaka masa (Ka duba sakin layi na 10)


11. Wane abu ne Yesu ya gaya wa almajiransa su yi adduꞌa a kai, kuma me ya sa hakan yake da muhimmanci? (Ezekiyel 36:23)

11 Yesu ya san cewa nufin Jehobah shi ne ya tsarkake sunansa kuma ya wanke sunan daga dukan zargi. Shi ya sa Yesu ya gaya wa mabiyansa su riƙa yin adduꞌa cewa: “Ubanmu wanda yake cikin sama, a tsarkake sunanka.” (Mat. 6:​9, NWT) Yesu ya san cewa wannan shi ne batu mafi muhimmanci ga dukan halittu. (Karanta Ezekiyel 36:23.) Babu wanda ya tsarkake sunan Allah a sama da duniya kamar Yesu. Amma da maƙiyan Yesu suka kama shi, sun zarge shi da yin sāɓo ga sunan Jehobah. A gun Yesu, babu zunubin da ya kai yin sāɓo ko kuma ƙarya a kan sunan Ubansa mai tsarki. Ya damu sosai domin ya san cewa za a zarge shi da aikata wannan laifi kuma a hukunta shi. Mai yiwuwa wannan dalilin ne ya sa Yesu yake “cikin azaba mai tsanani” kafin a kama shi.—Luk. 22:​41-44.

12. Ta yaya Yesu ya tsarkake sunan Ubansa a hanya mafi muhimmanci?

12 Don ya tsarkake sunan Ubansa, Yesu ya jimre tsanantawa da zagi da kuma ƙarya da aka yi a kansa. Ya san cewa ya yi duk abin da Ubansa ya ce masa ya yi, don haka ba ya bukatar ya ji kunya. (Ibran. 12:2) Ya kuma san cewa Shaiɗan ne yake kawo masa hari a wannan mawuyacin lokacin. (Luk. 22:​2-4; 23:​33, 34) Shaiɗan ya so ya sa Yesu ya kasa riƙe amincinsa ga Jehobah. Amma bai yi nasara ba sam! A ƙarshe, Yesu ya nuna cewa Shaiɗan babban maƙaryaci ne, kuma Jehobah yana da waɗanda suke bauta masa da aminci duk da tsanantawa da suke fuskanta!

13. Ta yaya za mu sa Sarkinmu farin ciki?

13 Idan kana so ka sa Yesu Sarkinmu farin ciki, to ka ci-gaba da yabon sunan Jehobah, wato ka taimaka wa mutane su san halayensa masu kyau. In ka yi hakan, kana bin halin Yesu Kristi ke nan. (1 Bit. 2:21) Kamar yadda Yesu ya yi, kai ma za ka faranta ran Jehobah kuma za ka nuna cewa maƙiyinsa, wato Shaiɗan babban maƙaryaci ne!

YABON SUNAN JEHOBAH YANA TAIMAKA MA WASU SU SAMI CETO

14-15. Waɗanne abubuwa masu kyau ne suke faruwa yayin da muke koya wa mutane game da Jehobah?

14 Yayin da muke yabon sunan Jehobah, muna taimaka ma wasu su sami ceto. Ta yaya? Littafi Mai Tsarki ya ce Shaiɗan ya ‘makantar da zuciyar’ marasa ba da gaskiya. (2 Kor. 4:4) Don haka, sun yarda da ƙaryace-ƙaryacen da Shaiɗan yake yaɗawa. Alal misali, wasu suna cewa babu Allah, Allah yana nesa da ꞌyan Adam kuma bai damu da wahalolinsu ba, Allah mugu ne kuma zai azabtar da masu zunubi har abadan abadin. Shaiɗan yana yaɗa ƙaryace-ƙaryace kamar haka domin yana so ya ɓata wa Jehobah suna, kuma ba ya so mutane su yi kusa da Jehobah. Amma muna hana Shaiɗan cim-ma burinsa ta yin waꞌazi. Muna koya wa mutane gaskiya game da Jehobah, don haka muna yabon sunansa. Wane sakamako ne hakan yake kawowa?

15 Gaskiyar da ke Kalmar Allah tana da iko sosai. Muna shaida wani abu mai muhimmanci a duk lokacin da muka koya wa mutane game da Allah da kuma halayensa masu kyau. Wato muna ganin yadda waꞌazinmu yake buɗe idanun mutane kuma yake taimaka musu su soma fahimtar halaye masu kyau na Ubanmu. Sanin yawan iko da Jehobah yake da shi yana ba su mamaki. (Isha. 40:26) Sukan dogara gare shi domin shi mai adalci ne. (M. Sha. 32:4) Sukan ga cewa yana da hikima sosai. (Isha. 55:9; Rom. 11:33) Kuma sanin cewa shi ƙauna ne, yana kwantar musu da hankali. (1 Yoh. 4:8) Yayin da suke yin kusa da Jehobah, suna ƙara kasancewa da tabbaci cewa za su samu rai na har abada. Hakika, taimaka wa mutane su yi kusa da Jehobah babban gata ne! Idan muna yin hakan, Jehobah zai ɗauke mu a matsayin ‘abokan aikinsa.’—1 Kor. 3:​5, 9.

16. Yaya wasu suka ji da suka koyi sunan Allah? Ka ba da misali.

16 Mukan fara da gaya wa mutane cewa sunan Allah Jehobah ne. Wannan gaskiyar kawai za ta iya canja rayuwar mutum. Alal misali, wata mata mai suna Aaliyah b ta taso a iyalin da ba Kiristoci ba ne. Amma ba ta gamsu da addininta ba, domin addinin bai taimaka mata ta yi kusa da Allah ba. Da ta soma nazarin Littafi Mai Tsarki da Shaidun Jehobah, sai kome ya canja. Ta soma ɗaukan Allah a matsayin abokinta. Ta kuma yi mamaki da ta ji cewa an cire sunan Allah a juyin Littafi Mai Tsarki da yawa kuma an saka laƙabi kamar Ubangiji a maimakon Jehobah. Rayuwarta ta canja da ta koyi cewa Jehobah ne sunan Allah. Ta yi farin ciki kuma ta ce: “Babban Abokina yana da suna!” Ta yaya sanin hakan ya amfane ta? Ta ce: “A yanzu, ina farin ciki sosai domin na sami gatan sanin sunan Jehobah.” Akwai kuma wani mutum mai suna Steve, wanda iyalinsa Yahudawa ne masu tsattsauran raꞌayi. Saboda munafunci da ya gani a addinai da yawa, ya ƙi zama memban wani addini. Amma bayan rasuwar mamarsa, wani abokinsa ya gaya masa ya zo ya ji nazarin da Shaidun Jehobah suke yi da shi, kuma ya yarda. Ya yi farin ciki sosai da ya gano sunan Allah. Ya ce: “Ban taɓa sanin sunan Allah ba.” Ya kuma ƙara da cewa: “Yanzu ne na fahimci cewa akwai Allah da gaske. Na kuma gano cewa yana da halaye masu kyau. Lallai na sami aboki.”

17. Me ya sa kake so ka ci-gaba da yabon sunan Jehobah? (Ka kuma duba hoton.)

17 Saꞌad da kake waꞌazi, kana gaya wa mutane game da sunan Allah mai tsarki kuwa? Kana taimaka musu su san halaye masu kyau na Allah? Idan kana hakan, kana yabon sunan Allah ke nan. Fatanmu shi ne ka ci-gaba da yabon sunan Jehobah ta wajen taimaka wa mutane su san halayensa masu kyau. Ta yin hakan, za ka taimaka wa mutane da yawa su sami ceto. Za ka yi koyi da Sarkinmu, Yesu Kristi. Kuma abu mafi muhimmanci ma shi ne za ka faranta ran Jehobah, Ubanmu na sama. Muna fatan za ka ‘girmama Sunansa har abadan abadin.’—Zab. 145:2.

Muna yabon Jehobah a duk lokacin da muka koya wa mutane sunansa kuma muka gaya musu game da halayensa masu kyau (Ka duba sakin layi na 17)

TA YAYA YABON SUNAN ALLAH . . .

  • yake sa shi farin ciki?

  • yake sa Yesu farin ciki?

  • yake taimaka wa mutane su sami ceto?

WAƘA TA 2 Jehobah Ne Sunanka

a Akwai dalilai masu kyau na gaskata cewa Markus ya yi amfani da sunan Jehobah ne saꞌad da ya yi ƙaulin abin da Yesu ya faɗa. Don haka, an mayar da sunan Jehobah a ayar a juyin New World Translation of the Holy Scriptures.

b An canja sunayen.