Koma ka ga abin da ke ciki

Koma ga abubuwan da ke ciki

TALIFIN NAZARI NA 7

WAƘA TA 51 Mun Yi Alkawarin Zama Bayin Allah

Me Za Mu Iya Koya Daga Rayuwar Ba-nazari?

Me Za Mu Iya Koya Daga Rayuwar Ba-nazari?

“Dukan kwanakin ɗaukar rantsuwa cewa zai [zama Ba-nazari], zai kasance da tsarki ga Yahweh.”L. ƘID. 6:8.

ABIN DA ZA MU KOYA

Za mu ga yadda bin halin Ba-nazari zai taimaka mana mu zama masu yin sadaukarwa da ƙarfin zuciya yayin da muke bauta wa Jehobah.

1. Wane hali mai kyau ne bayin Jehobah suka yi ta nunawa tun zamanin dā?

 KANA ƙaunar Jehobah sosai? Ba shakka kana ƙaunar sa. Kuma ba kai kaɗai ne kake ƙaunar Jehobah sosai haka ba. Tun zamanin dā, akwai mutane da yawa da su ma suka ƙaunaci Jehobah. (Zab. 104:​33, 34) Da yawa daga cikinsu sun yi sadaukarwa don su bauta ma Jehobah, kuma abin da kowane Ba-nazari a zamanin dā ya yi ke nan. Wane ne ake kira Ba-nazari, kuma me za mu iya koya daga wurin sa?

2. (a) Wane ne ake kira Ba-nazari? (Littafin Ƙidaya 6:​1, 2) (b) Me ya sa wasu Israꞌilawa suka yi alkawarin zama Ba-nazari?

2 A Ibrananci, idan aka ce “Nazirit” wato Ba-nazari, ana nufin mutumin da aka “keɓe” shi don ya yi wata hidima ta musamman. Shi ma Ba-israꞌile ne da ya yi wasu sadaukarwa don ya bauta wa Jehobah a hanya ta musamman. A Dokar Musa, an ba wa Israꞌilawa maza da mata, damar yi wa Jehobah alkawarin zama Ba-nazari na wasu lokuta. a (Karanta Littafin Ƙidaya 6:​1, 2.) Idan suka yi wannan alkawarin, za su bi wasu dokoki da ba kowane mutumin Israꞌila ne yake bi ba. Amma me ke sa mutumin Israꞌila ya ce yana so ya zama Ba-nazari? Da alama yawan ƙaunar da yake yi ma Jehobah da kuma godiya don alherinsa ne suke sa ya yi wannan zaɓin.—M. Sha. 6:5; 16:17.

3. Me ya sa za mu iya cewa bayin Allah suna kama da Ba-nazari?

3 A lokacin da “koyarwar Almasihu” ta ɗauki matsayin “Koyarwar Musa” ne aka daina yin alkawarin zama Ba-nazari. (Gal. 6:2; Rom. 10:4) Amma har yau, mutanen Jehobah suna nuna cewa suna so su bauta masa da dukan zuciyarsu, da hankalinsu, da kuma ƙarfinsu, kamar yadda masu hidimar Ba-nazari suka yi. (Mar. 12:30) Mu ma mun yi alkawarin bauta ma Jehobah a dukan rayuwarmu. Don mu cika wannan alkawarin, dole mu sa yin nufin Jehobah farko a rayuwarmu kuma mu riƙa yin sadaukarwa. Idan muka bincika yadda kowane Ba-nazari ya cika alkawarinsa, hakan zai koya mana yadda mu ma za mu cika namu alkawarin. b (Mat. 16:24) Bari mu ga wasu hanyoyi da suka cika alkawarinsu.

KA ZAMA MAI YIN SADAUKARWA

4. Bisa ga Littafin Ƙidaya 6:​3, 4, wace sadaukarwa ce kowane Ba-nazari ya yi?

4 Karanta Littafin Ƙidaya 6:​3, 4. An dokace su kada su sha giya da duk wani abin da aka samu daga itacen inabi, har da ꞌyaꞌyansa ɗanye da busassu. Waɗannan abubuwa kayan ci da sha ne masu kyau, don haka ba shakka sauran Israꞌilawan sun ji daɗin su. Littafi Mai Tsarki ya ce ruwan inabi yana “faranta wa mutum zuciya” kuma kyauta ne da Allah ya ba mu. (Zab. 104:​14, 15) Ko da yake abubuwan nan za su iya sa mutum ya ji daɗin rayuwa, kowane Ba-nazari ya yarda cewa ba zai yi amfani da su ba. c

Shin, ka yi shirin yin sadaukarwa kamar yadda kowane Ba-nazari ya yi? (Ka duba sakin layi na 4-6)


5. Wace sadaukarwa ce Madián da Marcela suka yi, kuma me ya sa?

5 Kamar yadda suka yi, mu ma muna yin sadaukarwa don mu bauta ma Jehobah sosai. Abin da wani ɗanꞌuwa mai suna Madián da matarsa Marcela suka yi ke nan. d A dā ba abin da suka rasa. Madián yana da aiki da ake biyan sa albashi mai tsoka kuma suna zama a babban gida. Amma sun so su ƙara ƙwazo a hidimarsu ga Jehobah, don haka, sun sauƙaƙa rayuwarsu. Sun ce, “Mun soma rage yawan kuɗi da muke kashewa, muka koma wani ƙaramin gida kuma muka sayar da motarmu.” Ba dole ba ne su yi waɗannan sadaukarwa. Su ne suka zaɓi hakan don su ƙara ƙwazo a hidimarsu. Yanzu suna gamsuwa da ɗan abin da suke da shi kuma suna farin ciki don matakan nan da suka ɗauka.

6. Me ya sa Kiristoci a zamaninmu suke yin sadaukarwa? (Ka kuma duba hoton.)

6 A yau ma mutanen Jehobah suna yin sadaukarwa don su ƙara samun lokacin yin ayyukan ibada, kuma hakan yana sa su farin ciki sosai. (1 Kor. 9:​3-6) Jehobah bai ce lallai sai mun yi sadaukarwar nan ba. Kuma moran abubuwan nan da muke sadaukarwa ba laifi ba ne. Alal misali, wasu sukan bar aiki da suke so ko gidansu. Akwai kuma da yawa da suka ce ba za su yi aure ko su haifi yara yanzu ba. Wasu kuma sun zaɓi yin hidima a inda akwai bukata, ko da hakan zai nisanta su daga abokansu da iyalinsu. Da yawa daga cikinmu muna yin waɗannan sadaukarwar ne da son ranmu, don muna so mu bauta ma Jehobah iya ƙarfinmu. Tabbas, Jehobah yana ɗaukan duk wata sadaukarwa da ka yi domin sa da muhimmanci sosai, ko da sadaukarwar babba ce ko ƙarama.—Ibran. 6:10.

KA YI SHIRIN FITA DABAM DA SAURAN MUTANE

7. Me zai iya sa ya yi wa Ba-nazari wuya ya cika alkawarin da ya yi? (Littafin Ƙidaya 6:5) (Ka kuma duba hoton.)

7 Karanta Littafin Ƙidaya 6:5. Kowane Ba-nazari yakan yi alkawari cewa ba zai aske kansa ba. Gashin yana nuna cewa sun miƙa kansu ga yin nufin Jehobah. Idan mutum ya daɗe yana yin wannan hidimar, gashin kansa zai yi girma sosai kuma mutane za su yi saurin lura da gashin. Idan mutane suna daraja shi kuma suna ƙarfafa shi ya cika alkawarinsa, yadda ya yi dabam ba zai dame shi ba. Amma damuwar ita ce, akwai lokutan da Israꞌilawa ba su ƙarfafa masu hidimar nan ba kuma ba su goyi bayansu ba. A lokacin annabi Amos, Israꞌilawa da suka daina bauta wa Jehobah sun yi ta sa “Nazirit su . . . sha ruwan inabi.” Kuma da alama sun yi hakan ne don su sa su su ƙarya alkawarin da suka yi cewa ba za su sha giya ba. (Amos 2:12) A wasu lokuta, Ba-nazari yana bukatar ƙarfin zuciya don ya iya cika alkawarin da ya yi kuma ya fita dabam da sauran mutane.

Ba-nazari da yake so ya cika alkawarinsa ba ya damuwa ko da ya fita dabam da sauran mutane (Ka duba sakin layi na 7)


8. Me ka koya daga yadda Benjamin ya yi ƙarfin zuciya?

8 Da taimakon Jehobah, mu ma za mu iya yin ƙarfin zuciya kuma mu fita dabam, ko da mu masu kunya ne. Alal misali, akwai wani ɗanꞌuwa mai suna Benjamin daga ƙasar Nowe wanda shekarunsa goma ne. Saboda yaƙi da ake yi a ƙasar Yukuren, makarantarsu ta shirya yadda za su nuna cewa suna goyon bayan Yukuren. Sai aka ce ma ꞌyan makarantar su saka kaya masu kalar tutar Yukuren, kuma su yi wata waƙa. Da yake Benjamin ba ya so ya yi hakan, ya tsaya a wani wuri da ke da ɗan nesa da inda za a yi waƙar. Amma sai wata malama ta gan shi kuma ta ɗaga murya tana cewa: “Ka zo ka same mu yanzu. Muna jiranka!” Sai Benjamin ya yi ƙarfin zuciya kuma ya je ya ce mata: “Ba na goyon bayan wani bangare a irin wannan rikicin. Kuma akwai Shaidun Jehobah da yawa da aka kulle su don sun ƙi yin yaƙi.” Malamar ta gamsu da abin da ya gaya mata kuma ta bar shi. Amma sai ꞌyan ajinsu suka soma tambayar sa abin da ya sa ya ƙi yin waƙar. Benjamin ya ji tsoro sosai, har saura kaɗan ya yi kuka. Amma sai ya yi ƙarfin zuciya kuma ya gaya musu daidai abin da ya gaya wa malamarsa. Daga baya, Benjamin ya gaya wa iyayensa cewa, Jehobah ne ya taimaka masa ya iya bayyana imaninsa.

9. Ta yaya za mu sa Jehobah farin ciki?

9 Da yake mun miƙa kanmu ga yin nufin Jehobah, mu ma mukan yi dabam da sauran mutane. Sai da ƙarfin zuciya za mu iya nuna wa mutane cewa mu Shaidun Jehobah ne a wurin aiki ko kuma a makaranta. Kuma yayin da halin mutane a duniyar nan take ƙara lalacewa, bin abin da Littafi Mai Tsarki ya ce da yin waꞌazi zai ƙara yi mana wuya. (2 Tim. 1:8; 3:13) Amma a ko-da-yaushe, za mu sa Jehobah ya ji daɗi idan muka yi ƙarfin zuciya kuma muka fita dabam da mutanen da ba sa bauta masa.—K. Mag. 27:11; Mal. 3:18.

KA SA YIN NUFIN JEHOBAH FARKO A RAYUWARKA

10. Me ya sa bin umurnin da ke Littafin Ƙidaya 6:​6, 7 bai yi wa kowane Ba-nazari sauƙi ba?

10 Karanta Littafin Ƙidaya 6:​6, 7. An hana Ba-nazari zuwa kusa da gawa. Idan ba ka yi tunani ba, za ka ce wannan ƙaramin abu ne. Amma a zamanin dā, bai yi wa Ba-nazari sauƙi ya bi wannan dokar ba, musamman idan ɗan iyalinsa ne ya rasu. Domin a lokacin, mutane sukan yi kusa da gawa saꞌad da ake janaꞌiza. (Yoh. 19:​39, 40; A. M. 9:​36-40) Ba-nazari ba zai iya yin hakan ba don alkawarin da ya yi. Har a lokacin da Ba-nazari yake makokin wani a iyalinsu da ya rasu, yakan nuna bangaskiya sosai ta wajen riƙe alkawarin da ya yi. Ba shakka, Jehobah ya ƙarfafa waɗannan bayinsa masu aminci don su iya jimre wannan yanayi mai wuya.

11. Mene ne Kirista yake bukatar ya sa a zuciyarsa idan yana shaꞌani da ꞌyan iyalinsa? (Ka kuma duba hoton.)

11 Mu Shaidun Jehobah ba ma wasa da alkawarin bauta wa Jehobah da muka yi. Kuma wannan alkawarin yana shafan matakan da muke ɗaukawa saꞌad da muke shaꞌani da ꞌyan iyalinmu. Muna aiki sosai don mu biya bukatun iyalinmu. Amma idan suna so mu yi abin da Jehobah ba ya so, ba za mu yarda musu ba. (Mat. 10:​35-37; 1 Tim. 5:8) A wasu lokuta, dole mu yi abin da ꞌyan iyalinmu ba sa so idan dai abin da zai faranta ran Jehobah ke nan.

Shin, za ka sa yin nufin Jehobah farko ko da ka shiga hali mai wuya sosai? (Ka duba sakin layi na 11) e


12. Da matsala ta taso a iyalin Alexandru, mene ne ya yi, kuma mene ne bai yi ba?

12 Abin da ya faru tsakanin ɗanꞌuwa Alexandru da matarsa Dorina ke nan. Bayan an yi shekara ɗaya ana nazarin Littafi Mai Tsarki da su biyun, sai Dorina ta daina nazarin, kuma ta so Alexandru shi ma ya daina. Amma bai yi fushi ba, kuma cikin basira ya ce mata shi zai ci-gaba. Dorina ba ta ji daɗi ba kuma ta yi ƙoƙarin sa shi dole ya daina. Abin bai yi ma Alexandru sauƙi ba. Wani lokaci idan Dorina ta yi masa baƙar magana, yakan ji kamar ya daina nazarin kawai. Duk da haka, Alexandru ya ci-gaba da sa yin nufin Jehobah farko a rayuwarsa, yana nuna wa matarsa ƙauna sosai kuma yana daraja ta. Ƙarshenta, halinsa ya sa matarsa ta sake soma yin nazari kuma daga baya ta yi baftisma.—Ka kalli bidiyon nan, Alexandru da Dorina Vacar: “Ƙauna Tana da Haƙuri da Kirki” da ke jerin bidiyoyin nan “Gaskiya ta Canja Rayuka,” a jw.org/ha.

13. Ta yaya za mu nuna ƙaunarmu ga Jehobah da kuma ꞌyan iyalinmu?

13 Jehobah ne ya shirya zaman iyali, kuma yana so kowa a iyali ya ji daɗi. (Afis. 3:​14, 15) Don haka, idan muna so mu yi farin ciki a rayuwa, muna bukatar mu bi abin da Jehobah ya ce. A kullum, ka kasance da tabbaci cewa Jehobah yana ƙaunar ka sosai domin sadaukarwa da kake yi, da yadda kake kula da iyalinka, da nuna musu ƙauna da daraja.—Rom. 12:10.

MU ƘARFAFA JUNA DON MU BI HALIN BA-NAZARI

14. Su waye ne musamman muke bukatar mu ƙarfafa su ta furucinmu?

14 Dukan waɗanda suka yi alkawarin bauta ma Jehobah a yau suna bukatar su zama masu yin sadaukarwa don ƙaunar da suke wa Jehobah. Amma yin hakan bai da sauƙi a wasu lokuta. Ta yaya za mu ƙarfafa juna mu zama masu yin sadaukarwa? Ta yin maganganu masu ban ƙarfafa. (Ayu. 16:5) Akwai wasu a ikilisiyarku da suke ƙoƙarin sauƙaƙa rayuwarsu don su ƙara yin ƙwazo a hidimar Jehobah? Ka san wasu matasa da suke yin ƙarfin zuciya kuma suna fita dabam da sauran ꞌyan makarantarsu duk da cewa hakan ba ya musu sauƙi? Ka san wasu ɗaliban Littafi Mai Tsarki ko ꞌyanꞌuwa da ba ya yi musu sauƙi su riƙe amincinsu domin ꞌyan iyalinsu suna tsananta musu? Zai yi kyau mu yi amfani da kowane zarafi da muka samu, mu yi maganganun da za su ƙarfafa waɗannan ꞌyanꞌuwanmu. Mu gaya musu yadda suke burge mu don ƙarfin zuciya da suke da shi da kuma sadaukarwa da suke yi.—Fil. 4, 5, 7

15. Mene ne wasu suka yi don su taimaka ma waɗanda suke hidima ta cikakken lokaci?

15 Wani lokaci, zai yi kyau mu yi wani abu don mu ƙarfafa ꞌyanꞌuwanmu da suke hidima ta cikakken lokaci. (K. Mag. 19:17; Ibran. 13:16) Abin da wata ꞌyarꞌuwa da ta tsufa a ƙasar Sri Lanka ta yi niyyar yi ke nan. Da aka ƙara mata kuɗin fensho, sai ta ce za ta tallafa ma wasu majagaba biyu su iya ci-gaba da yin hidimarsu don suna fuskantar matsalar kuɗi. Majagaban mata ne guda biyu, kuma matasa ne. Don ta taimaka musu, ta ce za ta dinga biyan kuɗin da suke kashewa a kan waya kowane wata. Wannan ꞌyarꞌuwar ta nuna hali mai kyau!

16. Mene ne muka koya daga rayuwar Ba-nazari?

16 Hakika akwai darussa da yawa da za mu iya koya daga wurin masu hidimar Ba-nazari! Amma alkawarin da suka yi ya kuma koya mana wani abu game da Jehobah. Ya nuna cewa Jehobah ba ya shakkar cewa muna so mu yi nufinsa. kuma idan da bukatar yin sadaukarwa, za mu yi shi don mu cika alkawari da muka yi cewa za mu bauta masa. Ƙari ga haka, yana girmama mu shi ya sa ya ba mu zarafin nuna masa cewa muna ƙaunar sa da son ranmu. (K. Mag. 23:​15, 16; Mar. 10:​28-30; 1 Yoh. 4:19) Rayuwar Ba-nazari ya nuna cewa Jehobah yana ganin sadaukarwar da muke yi dominsa, kuma hakan yana sa ya ƙaunace mu. Don haka, bari mu kasance da niyyar ci-gaba da bauta ma Jehobah, kuma mu yi hakan da dukan ƙarfinmu.

MECE CE AMSARKA?

  • A waɗanne hanyoyi ne kowane Ba-nazari ya nuna halin sadaukarwa da ƙarfin zuciya?

  • Ta yaya za mu ƙarfafa juna don mu bi halin masu hidimar Ba-nazari kuma mu riƙa yin sadaukarwa domin Jehobah?

  • Ta yaya hidimar Ba-nazari ya koya mana cewa Jehobah ya yarda da bayinsa?

WAƘA TA 124 Mu Kasance da Aminci

a Ko da yake akwai mutane ƙalila da Jehobah ne ya naɗa su su yi hidimar Ba-nazari, da alama yawancinsu Israꞌilawa ne da suka ba da kansu don yin wannan hidima.—Ka duba akwatin nan “ Ba-nazari da Jehobah Ne Ya Naɗa.”

b A wasu lokuta, littattafanmu sukan nuna cewa waɗanda suke hidima ta cikakken lokaci suna bin misalin Ba-nazari, amma a wannan talifin, za mu mai da hankali ga yadda dukan waɗanda suka yi alkawarin bauta ma Jehobah za su bi halin Ba-nazari.

c Ba abin da ya nuna cewa masu hidimar Ba-nazari suna da wani aiki da Jehobah ya ba su don su cika hidimarsu.

d Ka duba talifin nan, “Mun Yanke Shawarar Sauƙaƙa Rayuwarmu” a jerin talifofin nan, “Labaran Shaidun Jehobah,” a jw.org/ha.

e BAYANI A KAN HOTO: Wani Ba-nazari yana a saman gidansa yana kallon mutane za su je janaꞌizar wani a iyalinsa da ya rasu. Saboda alkawarin da ya yi, ba zai iya bin su ba.