Koma ka ga abin da ke ciki

Koma ga abubuwan da ke ciki

Ka Sani?

Ka Sani?

Me ya sa aka maimaita wasu kalmomi a Littafi Mai Tsarki?

AKWAI lokutan da marubutan Littafi Mai Tsarki suka maimaita wasu kalmomi. Ga dalilai uku da mai yiwuwa su ne suka sa marubutan nan suka yi hakan:

Lokacin da suka yi rubutun. A zamanin dā, yawancin Israꞌilawa ba su da Dokar da Aka Bayar ta Hannun Musa. A yawancin lokaci, saꞌad da suka taru a tentin saduwa da kuma haikali ne ake karanta musu Dokar. (M. Sha. 31:​10-12) Kuma, da yake jamaꞌar suna da yawa kuma sukan daɗe suna jin karatun, ba mamaki akwai abubuwa da yawa da ke ɗauke hankalinsu. (Neh. 8:​2, 3, 7) A waɗannan lokutan, yadda aka maimaita wasu muhimman kalmomi ya taimaka wa mutanen su tuna da nassosin kuma su bi abin da suka koya. Yadda aka maimaita wasu kalmomi, ya kuma taimaka musu su tuna wasu bayanai game da Dokokin da Jehobah ya ba su.—L. Fir. 18:​4-22; M. Sha. 5:1.

Irin abin da ake rubutawa. Wasu nassosi da ke Littafi Mai Tsarki waƙoƙi ne. Alal misali, littafin Zabura da Waƙar Waƙoƙi da littafin Makoki duk waƙoƙi ne. Kuma idan ana waƙa, wani lokaci akan maimaita wasu kalmomi don a nanata ainihin abin da waƙar take magana a kai, kuma don ya yi wa mutane sauƙi su haddace waƙar. Alal misali, ka lura da kalmomin da ke littafin Zabura 115:​9-11, wurin ya ce: “Ya ku mutanen Israꞌila, ku dogara ga Yahweh! Shi ne mai taimakonku da garkuwarku kuma. Ya ku gidan Haruna, ku dogara ga Yahweh! Shi ne mai taimakonku da garkuwarku kuma. Ya ku masu tsoronsa, ku dogara ga Yahweh! Shi ne mai taimakonku da garkuwarku kuma.” Hakika, wannan maimaicin da aka yi zai taimaka wa mawaƙan su tuna da koyarwar nan mai muhimmanci.

Don a nanata batutuwa masu muhimmanci. Wani lokaci, marubutan Littafi Mai Tsarki sukan maimaita furucin da ke da muhimmanci. Alal misali, lokacin da Jehobah ya ce wa Israꞌilawa kada su ci jini, ya sa Musa ya maimaita dalilin sau da yawa. Jehobah ya so su fahimci cewa, rai na kowace halitta yana cikin jininta ne. Wato, jini yana wakiltar rai. (L. Fir. 17:​11, 14) Daga baya, manzanni da dattawa da suke Urushalima sun sake nanata muhimmancin kiyaye jini saꞌad da suke bayyana abin da Kirista zai kiyaye don ya gamshi Allah.—A. M. 15:​20, 29.

Ko da yake an maimaita wasu kalmomi a Littafi Mai Tsarki, wannan bai nuna cewa Jehobah yana so mutanensa su dinga maimaita kalmomin Littafi Mai Tsarki babu gaira babu dalili ba. Alal misali, Yesu ya ce: “Garin yin adduꞌa kuma kada ku yi ta maimaitawa ta banza.” (Mat. 6:​7, Tsohuwar Hausa a Sauƙaƙe) Bayan haka, sai ya gaya mana abubuwan da ya kamata mu yi adduꞌa a kan su. (Mat. 6:​9-13) Don haka, Allah ba ya so mu riƙa maimaita kalmomi iri ɗaya saꞌad da muke adduꞌa. Amma za mu iya sake yin adduꞌa a kan abu guda sau da sau.—Mat. 7:​7-11.

Hakika, akwai dalilai masu kyau da suka sa aka yi ta maimaita wasu kalmomi ko furuci a Littafi Mai Tsarki. Wannan maimaicin wata hanya ce da Malaminmu yake koyar da mu domin amfanin mu.—Isha. 48:​17, 18.