Koma ka ga abin da ke ciki

Koma ga abubuwan da ke ciki

TALIFIN NAZARI NA 5

WAƘA TA 27 Allah Zai Bayyana ꞌYaꞌyansa

“Ba Zan Yar da Kai Ba”!

“Ba Zan Yar da Kai Ba”!

“Allah ya ce, ‘Har abada ba zan bar ka ba, sam sam ba zan yar da kai ba.’”IBRAN. 13:5b.

ABIN DA ZA MU KOYA

Wannan talifin zai tabbatar wa bayin Allah cewa, idan aka ɗauke sauran shafaffu zuwa sama, Jehobah ba zai bar su ba.

1. Yaushe ne za a ɗauki shafaffu zuwa sama?

 SHEKARU da yawa da suka shige, Shaidun Jehobah sun yi ta tunanin cewa, ‘Yaushe ne za a ɗauki sauran shafaffu zuwa sama?’ A dā, mun ɗauka cewa wasu shafaffu za su kasance tare da mu a nan duniya saꞌad da za a soma yaƙin Armageddon. Amma a Hasumiyar Tsaro ta 15 ga Yuli, 2013, mun koyi cewa za a ɗauki dukan shafaffu da suka rage a nan duniya zuwa sama, kafin a soma yaƙin Armageddon.—Mat. 24:31.

2. Waɗanne tambayoyi ne za mu iya yi, kuma mene ne za mu tattauna a talifin nan?

2 Amma muna iya yin tambayar nan: Me zai faru da “waɗansu tumaki” da suke bauta wa Allah da aminci a lokacin ƙunci mai girma? (Yoh. 10:16; Mat. 24:21) Wasu ꞌyanꞌuwa sun damu kuma suna ganin cewa za su rasa na yi bayan an ɗauke shafaffun Kiristoci zuwa sama. Bari mu tattauna labarai guda biyu a Littafi Mai Tsarki da mai yiwuwa suka sa ꞌyanꞌuwan nan su yi tunanin hakan. Bayan haka, sai mu tattauna wasu dalilan da suka sa bai kamata mu damu ba.

ABIN DA BA ZAI FARU BA

3-4. Mene ne wasu suke ganin zai faru, kuma me ya sa?

3 Wasu suna ganin cewa waɗansu tumaki a nan duniya za su daina bauta wa Jehobah tun da babu Hukumar da Ke Kula da Ayyukanmu da za ta yi musu ja-goranci. Ƙila akwai wasu labarai a Littafi Mai Tsarki da suka karanta da ya sa suke jin hakan. Bari mu ga wasu misalai daga cikin labaran. Na farko shi ne labarin Yehoyida Babban Firist. Shi mutum ne da ke ƙaunar Allah sosai. Shi da matarsa Yehosheba sun kāre wani yaro mai suna Yowash, kuma suka taimaka masa ya zama sarki da ke tsoron Allah. Yowash ya bauta wa Jehobah da aminci saꞌad da Yehoyida yake da rai. Amma bayan mutuwar Yehoyida, Yowash ya soma aikata mugunta. Ya saurari dattawansa, waɗanda mugaye ne kuma ya daina bauta wa Jehobah.—2 Tar. 24:​2, 15-19.

4 Wani misali kuma shi ne na Kiristoci a ƙarni na biyu. Manzo Yohanna shi ne manzo na ƙarshe da ke rayuwa a lokacin, kuma ya taimaka wa Kiristoci da yawa su ci-gaba da bauta wa Jehobah duk da matsaloli. (3 Yoh. 4) Kamar yadda sauran manzannin Yesu suka yi, Yohanna ya yi iya ƙoƙarinsa ya kāre ꞌyanꞌuwa a ikilisiyoyi daga koyarwar ƙarya, da kuma halaye marasa kyau. (1 Yoh. 2:18; 2 Tas. 2:7) Amma bayan mutuwarsa, koyarwar ƙarya ta zama ruwan dare gama gari. Bayan wasu shekaru, masu koyarwar ƙarya sun yaɗa koyarwar nan a dukan ikilisiyoyi, kuma suna ƙyale masu halaye marasa kyau a cikin ikilisiya.

5. Mene ne labarai biyun nan ba sa nufi?

5 Shin waɗannan labaran sun nuna abin da zai faru da waɗansu tumaki ne bayan an ɗauke shafaffu zuwa sama? Shin Kiristoci masu aminci a lokacin za su daina bauta wa Jehobah kamar Yowash, ko kuma su soma bin koyarwar ƙarya kamar yadda Kiristoci suka yi bayan mutuwar manzannin Yesu? Aꞌa, ba za su taɓa yin hakan ba. Muna da tabbaci cewa bayan shafaffu sun bar duniya, waɗansu tumaki za su ci-gaba da bauta wa Allah yadda ya kamata, kuma Jehobah zai ci-gaba da kula da su. Me ya sa muke da wannan tabbacin?

BA ZA A ƁATA BAUTA TA GASKIYA BA

6. Waɗanne abubuwa guda uku ne za mu tattauna?

6 Me ya tabbatar mana da cewa ba za a ɓata bauta ta gaskiya ba ko a lokacin ƙunci mai girma? Muna da wannan tabbacin ne, domin abin da Littafi Mai Tsarki ya gaya mana game da lokacin da muke rayuwa yanzu. Zamaninmu ya yi dabam da na Israꞌilawa da kuma na Kiristoci a ƙarni na biyu. Don haka, bari mu yi laꞌakari da abubuwa ukun nan: (1) Zamanin Israꞌilawa, (2) zamanin Kiristoci a ƙarni na biyu, da kuma (3) zamaninmu, wato “lokacin da za a mai da dukan abubuwa sabo.”—A. M. 3:21.

7. Me ya sa Israꞌilawa masu aminci ba su yi mamaki ba saꞌad da sarakunansu da alꞌummar suka daina bauta wa Jehobah?

7 Zamanin Israꞌilawa. Jim kaɗan kafin Musa ya mutu, ya gaya wa Israꞌilawa cewa: “Na sani bayan mutuwata, lallai za ku ƙazantar da kanku, za ku juya daga hanyar da na umarce ku.” (M. Sha. 31:29) Musa ya gargaɗi Israꞌilawan cewa, idan suka yi wa Allah tawaye, za a ci su da yaƙi kuma a kai su zaman bauta. (M. Sha. 28:​35, 36) Shin hakan ya faru da gaske? Ƙwarai kuwa. Sarakunan Israꞌila da yawa sun yi ɗaruruwan shekaru suna aikata mugunta kuma suna sa mutanen su bauta wa allolin ƙarya. Don haka, Jehobah ya bar mutanensa su sha wahala saboda muguntarsu, kuma ya ƙyale mutanen da ba Israꞌilawa ba su mulke su. (Ezek. 21:​25-27) Amma da Israꞌilawa masu aminci suka ga yadda maganar Jehobah ta cika, hakan ya ƙarfafa su.—Isha. 55:​10, 11.

8. Ya kamata mu yi mamaki cewa Kiristoci da yawa a ƙarni na biyu sun daina bauta ta gaskiya? Ka bayyana.

8 Zamanin Kiristoci a ƙarni na biyu. Ya kamata mu yi mamaki cewa Kiristoci da yawa a ƙarni na biyu sun daina bauta ta gaskiya ne? Aꞌa, domin Yesu ya riga ya faɗi cewa wasu Kiristoci za su soma yaɗa koyarwar ƙarya. (Mat. 7:​21-23; 13:​24-30, 36-43) Manzo Bulus da Bitrus da Yohanna sun nuna cewa annabcin da Yesu ya yi ya riga ya soma cika a ƙarni na farko. (2 Tas. 2:​3, 7; 2 Bit. 2:​1-3, 17-19; 1 Yoh. 2:18) A ƙarni na biyu, koyarwar ƙarya ta yaɗu sosai har cikin ikilisiyar Kirista. Bayan da manzo na ƙarshe ya mutu, masu yaɗa koyarwar ƙaryar nan sun zama membobin Babila Babba, wato daular addinin ƙarya. Wannan ma ya sake cika wani annabcin da Yesu ya yi.

9. Ta yaya zamanin da muke ciki ya yi dabam da zamanin Israꞌilawa da kuma na Kiristoci a ƙarni na biyu?

9 “Lokacin da za a mai da dukan abubuwa sabo.” Zamanin da muke ciki ya yi dabam da zamanin Israꞌilawa, da kuma lokacin da koyarwar ƙarya ta yaɗu a ƙarni na biyu. Mene ne ake kiran zamanin da muke ciki yanzu? Muna kiran sa “kwanakin ƙarshe.” (2 Tim. 3:1) Littafi Mai Tsarki ya nuna cewa, mun shiga wani lokaci mai muhimmanci a zamanin nan, kuma zai ci-gaba har sai Yesu ya mai da duniyar nan aljanna, kuma ya mai da mu kamilai. Ana kiran wannan lokacin, “lokacin da za a mai da dukan abubuwa sabo.” (A. M. 3:21) Lokacin nan ya soma ne a shekara ta 1914. Mene ne aka maido a 1914? An naɗa Yesu ya zama Sarki a sama. Hakan ya sa an sake samun sarki wanda yake wakiltar Jehobah, kuma ya fito daga zuriyar Dauda. Amma ba sarautar ce kawai abin da Jehobah ya maido ba. Bayan haka, ya soma maido da bauta ta gaskiya. (Isha. 2:​2-4; Ezek. 11:​17-20) Shin za a sake ɓata bauta ta gaskiya ne?

10. (a) Waɗanne annabce-annabce ne Littafi Mai Tsarki ya yi game da bauta ta gaskiya a zamaninmu? (Ishaya 54:17) (b) Me ya sa annabce-annabce kamar haka suke da ban-ƙarfafa?

10 Karanta Ishaya 54:17. Ka yi tunani game da annabcin nan: ‘Babu kayan yaƙin da aka ƙera domin a yaƙe ki wanda zai yi nasara.’ Wannan annabcin yana cika a yau. Wani annabci kuma da ya shafe mu a yau shi ne wanda ya ce: “Dukan ꞌyaꞌyanki kuwa, ni Yahweh ne zan koyar da su, za su kuwa yalwata cikin salama. Cikin yin adalci da gaskiya za ki kafu. . . . Ba za ki ji tsoron kome ba, barazana za ta yi nesa da ke.” (Isha. 54:​13, 14) Ko “allah na zamanin nan” wato Shaiɗan, ba zai iya hana bayin Allah yin waꞌazin da aka ce su yi ba. (2 Kor. 4:4) An riga an maido da bauta ta gaskiya kuma ba za a sake ɓata ta ba. Za a ci-gaba da bauta ta gaskiya har abada. Babu wani kayan yaƙi da aka ƙera domin mu da zai yi nasara.

MENE NE ZAI FARU?

11. Bayan an ɗauke shafaffu zuwa sama, mene ne ya tabbatar mana da cewa ba za a yasar da waɗansu tumaki ba?

11 Mene ne zai faru bayan an ɗauke sauran shafaffu zuwa sama? Ka tuna cewa, Yesu shi ne Makiyayinmu. Shi ne Shugaban ikilisiyar Kirista. Yesu da kansa ya gaya mana cewa: “Shugaba ɗaya gare ku, wato Almasihu.” (Mat. 23:10) Sarkinmu Yesu, wanda yake mulki a sama ba zai daina kula da mabiyansa ba. Da yake Yesu ne yake ja-goranci, mabiyansa a duniya ba sa bukatar su ji tsoro. Ba mu san dukan hanyoyin da Yesu zai yi amfani da su don ya ja-goranci mabiyansa a lokacin ba. Amma, bari mu bincika wasu misalai a Littafi Mai Tsarki da za su ƙarfafa mu.

12. Ta yaya Jehobah ya kula da mutanensa (a) bayan mutuwar Musa? (b) bayan an ba wa Iliya sabuwar hidima? (Ka kuma duba hoton.)

12 Musa ya mutu kafin Israꞌilawa su shiga Ƙasar Alkawari. To mene ne ya faru da bayin Allah bayan da wannan mutum mai aminci ya mutu? Shin Jehobah ya daina taimaka wa mutanensa ne? Aꞌa. Jehobah ya yi musu tanadi muddin sun riƙe amincinsu gare shi. Kafin Musa ya mutu, Jehobah ya gaya masa ya naɗa Joshua ya ja-gorance su. Musa ya riga ya yi shekaru da yawa yana horar da Joshua. (Fit. 33:11; M. Sha. 34:9) Ƙari ga haka, akwai wasu mutane da suke ja-goranci. Wasu cikinsu shugabanni ne a kan dubu-dubu, wasu a kan ɗari-ɗari, wasu a kan hamsin-hamsin, wasu kuma a kan goma-goma. (M. Sha. 1:15) Jehobah ya tanada wa mutanensa abin da suke bukata. Haka ma yake a zamanin Iliya. Iliya ya yi shekaru da yawa yana taimaka wa Israꞌilawa su riƙa yin bauta ta gaskiya. Sai Jehobah ya ba shi wata hidima dabam a Kudancin Israꞌila, wato Yahuda. (2 Sar. 2:1; 2 Tar. 21:12) Shin hakan na nufin cewa Jehobah ya yasar da waɗanda suke bauta masa da aminci a ƙabilu goma na Israꞌila ne? Aꞌa, domin Iliya ya yi shekaru da yawa yana horar da Elisha. Akwai kuma wasu “ƙungiyar annabawa” da aka horar da su don su yi ja-goranci. (2 Sar. 2:7) Don haka, akwai mutane masu aminci da yawa da za su taimaka wa bayin Allah. Jehobah ya ci-gaba da cika nufinsa da kuma taimaka wa bayinsa masu aminci.

Musa (a hoto na hagu) da Iliya, (a hoto na dama) kowannensu ya horar da wanda zai gaje shi (Ka duba sakin layi na 12)


13. Wane abu mai ban ƙarfafa ne muka gani a Ibraniyawa 13:5b? (Ka kuma duba hoton.)

13 Yanzu da muka tattauna waɗannan misalan, mene ne kake ganin zai faru bayan an ɗauke sauran shafaffu zuwa sama? Ba ma bukatar mu yi ta tunani. Littafi Mai Tsarki ya gaya mana wani abu mai ban-ƙarfafa. Abin shi ne, Jehobah ba zai taɓa yar da mutanensa a nan duniya ba. (Karanta Ibraniyawa 13:5b.) Kamar yadda Musa da Iliya suka yi, ꞌyanꞌuwa shafaffu da suke ja-goranci a yau suna horar da mutane sosai. Hukumar da Ke Kula da Ayyukanmu ta yi shekaru da yawa tana horar da ꞌyanꞌuwa daga cikin waɗansu tumaki don su iya yin ja-goranci. Alal misali, ta shirya makarantu da yawa don ta horar da dattawa, da masu kula da daꞌira, da membobin Kwamitin da Ke Kula da Ofisoshinmu, da masu ja-goranci a Bethel da dai sauransu. Ban da haka, tana horar da waɗanda suke taimaka wa kwamitoci dabam-dabam na Hukumar. Yanzu waɗannan mataimakan suna kula da ayyuka da yawa a ƙungiyar Jehobah. An koyar da su sosai don su ci-gaba da kula da tumakin Kristi.

Hukumar da Ke Kula da Ayyukanmu ta yi iya ƙoƙarinta don ta koyar da mataimakanta, kuma ta shirya makarantu don dattawa, da masu kula da daꞌira, da membobin Kwamitin da Ke Kula da Ofisoshinmu da masu ja-goranci a Bethel, da masu waꞌazi a ƙasashen waje (Ka duba sakin layi na 13)


14. Wane darasi mafi muhimmanci ne muka tattauna a talifin nan?

14 Darasi mafi muhimmanci da muka koya a talifin nan shi ne: Dab da ƙarshen ƙunci mai girma, za a ɗauki sauran shafaffu da suka rage zuwa sama, amma ba za a daina bauta ta gaskiya a nan duniya ba. Shugabanmu Yesu Kristi zai tabbatar da cewa bayin Allah sun ci-gaba da bauta wa Jehobah. A lokacin, ƙasashen da suka haɗa kai, wato Gog na Magog, za su kawo mana hari. (Ezek. 38:​18-20) Amma ba za su yi nasara ba, ba za su iya hana bayin Allah bauta masa ba. Hakika, Jehobah zai cece mu. A wahayin da aka nuna wa Yohanna, ya ga wani “babban taro,” wato waɗansu tumaki. An gaya wa Yohanna cewa wannan “babban taro” ko kuma taro mai girma, sun fito ne daga “azabar nan mai zafi.” (R. Yar. 7:​9, 14) Don haka, muna da tabbaci cewa Jehobah zai cece su.

15-16. Mene ne Ruꞌuyar da Aka Yi wa Yohanna 17:14 ta ce shafaffun Kiristoci za su yi a lokacin yaƙin Armageddon, kuma me ya sa hakan yake da ban-ƙarfafa?

15 Duk da haka, wasu suna iya cewa: ‘Kiristoci shafaffu fa? Mene ne za su yi idan suka bar duniya?’ Littafi Mai Tsarki ya gaya mana amsar tambayar nan. Ya faɗi cewa shugabanin duniya za su yi “yaƙi da Ɗan Ragon.” Hakika ba za su yi nasara ba. Littafi Mai Tsarki ya ce, “Ɗan Ragon kuwa zai ci nasara a kan sarakunan nan.” Su wane ne za su taimaka masa? Ayar ta ce waɗanda aka “kira, aka zaɓa, aka kuma amince da su” za su taimaka masa. (Karanta Ruꞌuyar da Aka Yi wa Yohanna 17:14.) Su waye ke nan? Su ne shafaffun Kiristoci da aka ta da su. Don haka, bayan an ɗauke sauran shafaffu da suka rage a duniya, aiki na farko da za su yi shi ne yaƙi. Wannan ba ƙaramin aiki ba ne. Wasu shafaffun Kiristoci mayaƙa ne kafin su zama Shaidun Jehobah. Wasu ma sojoji ne a dā, sai suka koyi gaskiya kuma suka koyi zaman lafiya da mutane. (Gal. 5:22; 2 Tas. 3:16) Sun daina yaƙi, amma bayan an ɗauke su zuwa sama, za su haɗa kai da Yesu da malaꞌikunsa don su yaƙi maƙiyan Allah. Kuma wannan shi ne yaƙi na ƙarshe da Allah zai yi.

16 A nan duniya, wasu shafaffu sun tsufa kuma ba su da ƙarfi. Amma da zarar an ta da su zuwa sama, za su zama halittu na ruhu masu ƙarfi da ba sa mutuwa, kuma za su yi yaƙi tare da Sarkinmu Yesu Kristi. Bayan an gama yaƙin Armageddon, za su yi aiki tare da Yesu don su taimaka wa ꞌyan Adam su zama kamiltattu. Babu shakka, za su fi taimaka mana a lokacin fiye da yadda suka yi saꞌad da suke duniya.

17. Ta yaya muka san cewa duka bayin Allah za su tsira a lokacin yaƙin Armageddon?

17 Kana cikin waɗansu tumaki? Idan haka ne, mene ne kake bukatar ka yi saꞌad da aka soma yaƙin Armageddon? Abin da kawai kake bukatar ka yi shi ne, ka dogara ga Jehobah kuma ka bi umurnansa. Waɗanne umurnai ne wataƙila zai ba mu? Littafi Mai Tsarki ya gaya mana cewa: “Ku tafi ku shiga ɗakunanku, ku rufe ƙofofinku ku ɓoye kanku, sai fushina ya wuce.” (Isha. 26:20) Duka bayin Jehobah masu aminci a sama da kuma duniya za su tsira a lokacin. Kamar yadda manzo Bulus ya faɗa, muna da tabbaci cewa ‘ko halin yanzu ko na nan gaba, ko ikoki iri-iri, . . . ba su isa ba sam su raba mu da ƙaunar da Allah yake yi mana.’ (Rom. 8:​38, 39) A kowane lokaci, ka riƙa tuna cewa Jehobah yana ƙaunar ka kuma ba zai taɓa yashe ka ba!

BAYAN AN ƊAUKE SAURAN SHAFAFFU ZUWA SAMA,

  • mene ne ba zai faru ba?

  • me ya sa za mu iya kasancewa da tabbaci cewa ba za a sake ɓata bauta ta gaskiya ba?

  • me ya sa muke da tabbaci cewa Jehobah zai kula da mutanensa?

WAƘA TA 8 Jehobah Ne Mafakarmu