Koma ka ga abin da ke ciki

Koma ga abubuwan da ke ciki

Yaya Kake Daukan Kurakurai

Yaya Kake Daukan Kurakurai

Wani mai suna Don da matarsa Margaret * sun ji daɗi sosai sa’ad da ’yarsu ta ziyarce su tare da iyalinta. Da za su ci abincin ƙarshe kafin su koma, sai Margaret wadda ta ƙware a yin dafe-dafe ta dafa musu taliya da miyar mān shanu, kuma shi ne abincin da jikokinta suke so sosai.

Dukansu sun zauna a kujera suna jiran abincin. Sai Margaret ta kawo abincin a cikin babban kwano ta ajiye a kan teburi. Da ta buɗe kwanon, sai ta yi mamaki cewa miyar mān shanu ne kawai a cikin kwanon! Margaret ta manta ta saka taliyar.

Dukanmu mukan yi kuskure ko da yaya yawan shekarunmu ko kuma iliminmu yake. Muna iya yi wa wani baƙar magana ko mu yi wani abu a lokacin da bai dace ba ko kuma mu yi mantuwa. Amma me ya sa muke yin kuskure? Ta yaya za mu bi da kuskure? Zai yiwu mu guji yin kuskure? Bari mu ga yadda ya kamata mu riƙa ɗaukan kuskure, don hakan zai taimaka mana mu amsa tambayoyin nan.

RA’AYINMU DA NA ALLAH GAME DA YIN KUSKURE

Idan muka yi abin da ya dace kuma mutane suka yaba mana, muna farin ciki sosai. Hakazalika, idan muka yi kuskure ko da ba da saninmu ba ko idan wasu ba su san cewa mun yi hakan ba, zai dace mu amince da kuskurenmu. Amma yin hakan na bukatar tawali’u.

Idan muna yawan ɗaukan kanmu da muhimmanci sosai, za mu soma ba da hujja don kuskurenmu ko mu ɗora wa wani laifin ko kuma mu ƙi amincewa da kuskurenmu. Irin wannan hali yakan janyo sakamako marar kyau, domin ba za a iya magance matsalar ba kuma za a ɗora laifin a kan wani da bai san abin da ya faru ba. Ko da mun iya kauce wa kuskuren da muka yi a yanzu, ya kamata mu san cewa a ƙarshe ‘kowane ɗayanmu za ya kawo lissafin kansa ga Allah.’​—Romawa 14:12.

Allah yana ɗaukan kuskure yadda ya dace. A cikin littafin Zabura, an ambata cewa shi Ubangiji ‘mai jinƙai ne, mai ƙauna, ba ya tsautawa kullum, ba ya jin haushi har abada.’ Ya san cewa mu ’yan Adam ajizai ne kuma a kullum “yakan tuna, da ƙura aka yi mu.”​—Zabura 103:​8, 9, 14, Littafi Mai Tsarki.

Ƙari ga haka, kamar yadda uba mai jinƙai yake, Allah yana son ’ya’yansa su riƙa kasancewa da ra’ayinsa idan wani ya yi kuskure. (Zabura 130:3) Kalmarsa tana ɗauke da shawarwari masu kyau da za su taimaka mana a duk lokacin da muka yi kuskure ko kuma wasu suka yi kuskure.

YADDA ZA MU BI DA KUSKURE

Idan mutum ya yi kuskure, zai yi ƙoƙarin ɗora wa wani laifin ko kuma ya yi ƙoƙarin ba da hujja. A maimakon haka, idan ka ɓata wa wani rai, zai dace ka nemi gafara, ka magance matsalar kuma ka ci gaba da abotarku. Shin ka taɓa yin kuskure, ko ka yi abin da ya ɓata wa wani rai? Idan hakan  ya faru, maimakon ka yi fushi da kanka, ko kuma ka zargi wasu, zai dace ka yi iya ƙoƙarinka don ka magance matsalar. Idan ka nace cewa ba kai ne da laifi ba, hakan zai daɗa sa matsalar ta yi muni. Ka koyi darasi daga abin da ya faru, ka magance matsalar, kuma ka ɗauki matakin da ya dace.

Idan wani ya yi kuskure, mukan yi saurin nuna ɓacin ranmu. Amma yana da kyau mu bi shawarar da Yesu ya ba mu cewa: “Duk abin da kuke so mutane su yi muku, ku ma sai ku yi musu.” (Matta 7:12) Idan ka yi laifi ko da ba mai tsanani ba ne, za ka so mutane su tausaya maka kuma a yafe maka laifin gaba ɗaya. To me zai hana kai ma ka tausaya wa wasu?​—Afisawa 4:32.

ƘA’IDODIN DA ZA SU TAIMAKA MANA MU RAGE YIN KUSKURE

Wani kamus ya bayyana cewa abubuwan da suke sa mutum ya yi kuskure su ne, “rashin ingantaccen ilimi da rashin mai da hankali sosai ko kuma yanke hukuncin da bai dace ba.” Dukanmu a wasu lokuta mukan aikata aƙalla ɗaya daga cikin waɗannan abubuwan da aka ambata. Amma muna iya rage yawan kuskuren da muke yi idan muna yin la’akari da wasu ƙa’idodin Littafi Mai Tsarki.

Ɗaya daga cikin ƙa’idar ita ce wanda ke littafin Misalai 18:​13, da ta ce: “Wanda ya mayar da magana tun ba ya ji ba, wauta ce gareshi da kunya.” Idan ka ɗauki ɗan lokaci don ka fahimci batun kuma ka yi tunani a kan amsar da za ka bayar, hakan zai sa ka guji yin baƙar magana ko kuma yin abin da bai dace ba. Idan ka saurara kuma ka fahimci batun da kyau, za ka yanke hukunci mai kyau kuma ka guji yin kuskure.

Wata ƙa’ida kuma ta ce: “Idan ya yiwu, ku zauna lafiya da dukan mutane, gwargwadon iyawarku.” (Romawa 12:18) Ka yi iya ƙoƙarinka don ku zauna lafiya kuma ku kasance da haɗin kai. Idan kana aiki tare da wasu, kada ka fi mai da hankali ga kanka kawai. A maimakon haka, ka riƙa daraja su, ka yaba musu kuma ka ƙarfafa su. Hakan zai sa ku riƙa yafe wa juna idan wani ya yi wa wani baƙar magana ko kuma ya yi masa wani laifi.

Ka yi ƙoƙari ka koyi darasi mai kyau daga kuskuren. Maimakon ka ba da hujja don abin da ka yi, zai dace ka yi amfani da zarafin wajen koyan hali mai kyau. Wataƙila, a yanayin kana bukatar ka nuna halaye kamar haƙuri ko kirki ko kamun kai ko salama ko ƙauna ko kuma tawali’u. (Galatiyawa 5:​22, 23) Ƙari ga haka, kana iya sanin abin da bai kamata ka yi ba a nan gaba. Kada ka riƙa ɗaukan kanka da muhimmanci fiye da kowa. Yawan wasa da dariya zai sa ku guji rashin fahimtar juna.

ALBARKAR DA ZA KA SAMU

Idan muna ɗaukan kuskure yadda ya dace, zai taimaka mana mu iya jimrewa sa’ad da hakan ya faru. Zai sa mu riƙa gafartawa kanmu da kuma wasu. Idan muka koyi darasi daga kuskuren da muka yi, za mu yi wayo kuma mutane za su so mu. Ba za mu yi fushi da wasu ko da kanmu ba. Sanin cewa wasu ma suna fama da nasu kuskuren zai sa mu kusace su. Mafi muhimmanci ma, za mu amfana idan muka yi koyi da yadda Allah yake nuna ƙauna da kuma gafarta wa mutane.​—Kolosiyawa 3:13.

Shin kuskuren Margaret wadda muka ambata da farko ya sa iyalin ba su ji daɗin ziyarar ba? A’a. A maimakon haka, sun yi dariya kuma sun ci abincin ba tare da taliyar ba! Bayan wasu shekaru, jikokin Margaret biyun sun gaya wa yaransu labarin da kuma yadda suka ji daɗin ziyarar da suka kai wa kakaninsu. Domin abin da ta yi kuskure ne kawai!

^ sakin layi na 2 An canja sunayen.