Koma ka ga abin da ke ciki

Koma ga abubuwan da ke ciki

 ABIN DA KE SHAFIN FARKO | WACE KYAUTA CE TA FI TAMANI?

Yadda Za Ka San Kyauta Mafi Tamani

Yadda Za Ka San Kyauta Mafi Tamani

Ba shi da sauƙi a san kyautar da za ta dace da wani. Ban da haka ma, wanda ya karɓi kyautar ne zai iya sanin ko tana da tamani ko a’a. Ƙari ga haka, abin da yake da daraja ga wani, ba zai zama da daraja ga wani ba.

Alal misali, wani matashi yana iya ganin cewa kyautar wayar selula da ake yayi ce ta fi dacewa da shi. A wani ɓangare kuma, babba zai fi daraja kyautar da iyalinsa suka adana shekaru da yawa. A wasu al’adu, mutane suna ganin kyautar kuɗi ta fi daraja, domin wanda aka ba kyautar zai iya sayan duk abin da yake so.

Duk da cewa ba shi da sauƙi a san kyautar da za ta dace da wani, mutane da dama sun ci gaba da neman kyautar da za ta kasance da tamani ga wanda suke ƙauna. Ko da yake ba a koyaushe ne ake samun irin wannan kyautar ba, amma akwai abubuwan da za su taimaka mana mu san kyautar da take da tamani. Bari mu yi la’akari da abubuwa guda huɗu da za su sa kyautarmu ta kasance da tamani ga wanda muke so mu ba kyautar.

Abin da mai karɓan yake so. Wani mutum da ke zama a birnin Belfast, a Arewacin Ireland ya ce keken da aka ba shi sa’ad da yake shekara 10 ko 11 ce kyauta mafi daraja da aka taɓa ba shi. Me ya sa? Ya ce: “Domin ina matuƙar son keken.” Abin da ya faɗa ya nuna cewa idan aka ba mutum kyautar abin da yake so, za ta kasance da daraja a wurinsa. Don haka, zai dace ka yi tunani sosai a kan mutumin da kake so ka ba kyauta. Ka yi ƙoƙarin sanin abin da yake so, don hakan zai sa ya daraja kyautar. Alal misali, tsofaffi suna jin daɗin kasancewa tare da jikokinsu. Suna son su riƙa ganin yaransu da kuma jikokinsu a kowane lokaci. Saboda haka, tsofaffi za su fi daraja kasancewa tare da yaransu da kuma jikokinsu a lokacin hutu fiye da kowace irin kyauta.

Idan kana saurarar mutumin da kake so ka ba kyauta yayin da yake magana, za ka iya sanin abin da yake so. Littafi Mai Tsarki ya ce mu riƙa ‘hanzarin ji, mu yi jinkirin yin magana.’ (Yaƙub 1:19) Saboda haka, a duk lokacin da kake tattaunawa da abokanka ko kuma ’yan’uwanka, ka saurare su da kyau don ka san abubuwan da suke so da  waɗanda ba sa so. Hakan zai taimaka maka ka iya ba su kyautar abin da suke so.

Bukatun mai karɓa. Kome ƙanƙantar kyauta, tana iya kasancewa da tamani ga wanda ya karɓa idan kyautar ta biya masa wata bukata ta musamman. Amma ta yaya za ka iya sanin abin da wani yake bukata?

Kana iya tunanin cewa zai fi maka sauƙi ka san bukatun wani idan ka tambaye shi abin da yake so. Amma ga yawancin mutanen da suke ba da kyauta, yin hakan ba zai sa su farin ciki sosai ba, domin sun fi so su sa mai karɓan mamaki ta wajen ba shi daidai abin da yake bukata. Ƙari ga haka, wasu mutane suna faɗin abin da suke so da abin da ba sa so, amma ba za su taɓa gaya maka bukatunsu ba.

Don haka, ka riƙa lura da yanayin mutumin. Ka lura ko mutumin matashi ne ko tsoho ko mijin aure ko marar aure ko gwauro ko wanda suka kashe aure ko yana da aiki ko kuma ya yi ritaya. Ka yi tunani a kan abin da zai iya biyan bukatar mutumin a irin yanayin da yake ciki.

Don ka iya sanin bukatun wanda kake so ka ba kyauta, zai dace ka tuntuɓi waɗanda suka taɓa yin hakan. Za su iya gaya maka wasu abubuwan da mutane suke bukata da yawanci ba su sani ba. Yin haka zai taimaka maka ka iya ba da kyautar abin da mutane ba su sani ba sosai kuma kyautar za ta biya bukatar mutumin.

Lokacin da aka ba da kyautar. Littafi Mai Tsarki ya ce: “Magana a kan kari, ina misalin kyaunta!” (Misalai 15:23) Wannan ayar ta nuna cewa yin magana a lokacin da ya dace yana da muhimmanci sosai. Haka yake da ayyukanmu. Kamar yadda yin magana a lokacin da ya dace yake da daɗi ga mai sauraro, kyauta ma idan aka ba da ita a lokacin da ya dace, za ta sa mai karɓa farin ciki sosai.

Abokinka zai yi aure. Wani matashi ya kusan sauke karatu. Wasu ma’aurata sun kusan haihuwa. Waɗannan kaɗan ne daga cikin lokutan da ake yawan ba da kyauta. Wasu sukan rubuta kwanakin watan aukuwar da aka ambata a sama. Hakan zai sa su iya shirya kyautar da za ta dace da kowane lokaci. *

Ba sai a lokacin bukukuwa ne kawai za ka riƙa ba da kyauta ba. Kana iya ba da kyauta a kowane lokaci. Amma akwai abin da ya dace ka yi hankali da shi. Alal misali, idan namiji ya ba mace kyauta ba tare da wani ƙwaƙƙwarar dalili ba, tana iya ɗauka cewa yana son ta. Idan ba sonta yake yi ba kuma ya ba da kyauta, hakan zai iya janyo matsala a tsakaninsu. Don haka, ya dace mu yi la’akari da dalilin da ya sa muke ba da kyauta.

Dalilin da ya sa aka ba da kyautar. Kamar yadda misalin da muka ambata ɗazu ya nuna, zai dace mu yi tunanin ko kyautarmu za ta sa mai karɓa ya yi wani tunanin da bai dace ba. A wani ɓangaren kuma, yana da kyau wanda yake so ya ba da kyautar ya bincika dalilin da ya sa yake so ya ba da kyautar. Wasu mutane suna ganin suna da dalili mai kyau na ba da kyauta. Wasu kuma suna ba da kyauta a wasu ranaku a kowace shekara, amma ba da son ransu ba. Har ila, wasu suna ba da kyauta kuma su sa ran cewa wanda suka ba kyautar ma zai ba su wani abu.

Mene ne za ka yi don ka tabbata cewa kana da dalili mai kyau na ba da kyauta? Littafi Mai Tsarki ya ce: “Duk abin da za ku yi, ku yi shi da ƙauna.” (1 Korintiyawa 16:​14, Littafi Mai Tsarki) Idan ka ba da kyauta domin kana ƙaunar mutumin da gaske ko kuma don kana son ka taimaka masa, hakan zai sa kai da wanda ya karɓi kyautar farin ciki. Ubanmu na sama ma zai ji daɗi idan ka ba da kyauta daga cikin zuciyarka. Manzo Bulus ya yaba ma Kiristocin da ke Koranti sa’ad da suka ba  ’yan’uwansu Kiristoci da ke Yahuda kayan agaji. Ya ce: “Allah yana son mai-bayarwa da daɗin rai.”​—⁠2 Korintiyawa 9:⁠7.

Idan ka yi tunani sosai a kan abubuwa huɗu da muka tattauna, zai taimaka maka ka ba da kyauta da za ta sa mutane farin ciki. Waɗannan dalilai da kuma wasu da dama ne suka sa kyautar da Allah ya ba ’yan Adam ta zama mafi daraja. Don Allah, ka karanta talifi na gaba don ka san wannan kyautar da ta fi kowace kyauta daraja.

^ sakin layi na 13 Wasu mutane sukan ba da kyauta a lokacin bukukuwan ranar haihuwa da dai sauransu. Amma, ana yawan yin abubuwan da Littafi Mai Tsarki ya haramta a bukukuwan nan. Ka duba talifin nan “Masu Karatu Sun Yi Tambaya​—Ya Kamata Kiristoci Su Yi Bikin Kirsimati Ne?” da ke wannan mujallar.