Koma ka ga abin da ke ciki

Wane Ne Ainihi Yake Iko da Duniya?

Wane Ne Ainihi Yake Iko da Duniya?

Kana ganin . . .

  • Allah ne?

  • ’yan Adam ne?

  • ko wani halitta dabam?

ABIN DA LITTAFI MAI TSARKI YA CE

“Duniya duka kuwa tana hannun Mugun.”—1 Yohanna 5:19, Littafi Mai Tsarki.

“Dalilin bayyanar Ɗan Allah shi ne domin ya rushe aikin Iblis.”—1 Yohanna 3:8.

ABIN DA ZA KA IYA MORA IDAN KA GASKATA DA HAKAN

Za ka sami ingantaccen bayani game da abin da ya sa munanan abubuwa suke faruwa a duniya.—Ru’ya ta Yohanna 12:12.

Tabbataccen hujja na ba da gaskiya cewa za a sami canji da zai sa mutane su ji daɗin rayuwa a duniya.—1 Yohanna 2:17.

ZA MU IYA GASKATA DA LITTAFI MAI TSARKI KUWA?

Hakika, aƙalla saboda waɗannan dalilai uku:

  • Za a kawo ƙarshen mulkin Shaiɗan. Tabbas, Jehobah zai kawo ƙarshen sarautar Shaiɗan bisa ’yan Adam. Jehobah ya yi alkawari cewa zai “halakar da . . . Iblis” kuma ya gyara dukan abubuwan da Shaiɗan ya ɓata.—Ibraniyawa 2:14.

  • Allah ya zaɓi Yesu Kristi ya yi mulkin duniya. Halin Yesu ya bambanta sosai da na wannan mugun, mai son zuciya da ke mulkin duniya a yanzu. Allah ya yi alkawari game da mulkin Yesu cewa: ‘Za ya nuna tausayi ga matalauci da mai-rashi, za ya kuwa cece su . . . daga zalunci da ƙwace.’—Zabura 72:13, 14.

  • Allah ba ya ƙarya. Littafi Mai Tsarki ya bayyana ɓaro-ɓaro cewa: “Ba shi yiwuwa Allah ya yi ƙarya.” (Ibraniyawa 6:18) Idan Jehobah ya yi alkawarin yin wani abu, kamar dai an gama! (Ishaya 55:10, 11) “Za a fitar da mai-mulkin wannan duniya.”—Yohanna 12:31.

KA YI TUNANI A KAN WANNAN TAMBAYAR

Yaya duniya za ta kasance bayan an kawar da mai mulkinta?

Littafi Mai Tsarki ya ba da amsar a ZABURA 37:10, 11 da kuma RU’YA TA YOHANNA 21:3, 4.