Koma ka ga abin da ke ciki

Koma ga abubuwan da ke ciki

Za ka so ka yi nufin Jehobah?

Za ka so ka yi nufin Jehobah?

Muna godiya saboda bincika wannan ƙasidar da ka yi don ka san ko su wane ne Shaidun Jehobah, da yadda muke gudanar da ayyukanmu, kuma ka ga yadda ƙungiyarmu take cika aiki. Muna fatan cewa wannan ƙasidar ta sa ka fahimci cewa mu ne muke yin nufin Jehobah a yau. Muna ƙarfafa ka ka ci gaba da koya game da Allah, ka gaya wa iyalinka da sauran abokanka abubuwan da kake koya, kuma ka ci gaba da yin tarayya da mu a taronmu na Kirista.—Ibraniyawa 10:23-25.

Idan ka ci gaba da koya game da Jehobah, za ka ga cewa yana ƙaunarka da gaske. Hakan zai motsa ka ka yi iya ƙoƙarinka ka nuna masa cewa kana ƙaunarsa. (1 Yohanna 4:8-10, 19) Amma ta yaya za ka nuna hakan a rayuwarka ta yau da kullum? Ta yaya yin biyayya ga ƙa’idodin Allah game da ɗabi’a zai amfane ka? Mene ne zai taimaka maka ka yi nufin Allah tare da mu? Malamin da ke koya maka Littafi Mai Tsarki zai yi farin cikin bayyana maka amsoshin tambayoyin nan saboda kai da iyalinka “ku tsare kanku cikin ƙaunar Allah, . . . zuwa rai na har abada.”—Yahuda 21.

Muna ƙarfafa ka kada ka yi sanyin gwiwa amma ka samu ci gaba a gaskiyar da kake koya ta wajen yin nazarin littafin nan “Ku Tsare Kanku Cikin Ƙaunar Allah”.