Koma ka ga abin da ke ciki

Koma ga abubuwan da ke ciki

DARASI NA 9

Ta Yaya Za Mu Yi Shiri Sosai Kafin Mu Halarci Taro?

Ta Yaya Za Mu Yi Shiri Sosai Kafin Mu Halarci Taro?

Kambodiya

Yukiren

Idan kana nazarin Littafi Mai Tsarki da Shaidun Jehobah, mai yiwuwa kana yin shiri kafin kowane nazari. Hakazalika, idan kana so ka amfana sa’ad da ka halarci taro a Majami’ar Mulki, zai dace ka yi shiri kafin ka halarci taron. Amma za mu amfana sosai idan muna da tsari mai kyau da muke bi a kai a kai.

Ka zaɓi lokaci da kuma wurin da za ka yi nazari. A wane lokaci ne za ka fi mai da hankali wuri ɗaya sa’ad da kake nazari? Da sassafe ne kafin ka fara aiki, ko kuma can da yamma bayan yaranka sun yi barci? Ko da ba zai yiwu ka ɗauki lokaci mai tsawo ba kana nazari, ka ayyana yawan lokacin da za ka yi kana nazarin, kuma kada ka bari wani abu ya hana ka yin hakan da zarar ka fara. Ka zaɓi wurin da babu surutu, kuma ka kashe abubuwa da za su iya ɗauke hankalinka, kamar su rediyo da talabijin da kuma wayar tarho. Yin addu’a kafin ka soma nazari zai taimaka maka ka rage tunanin abubuwan da ke damunka don ka mai da hankali sosai ga Kalmar Allah da kake son ka karanta.—Filibiyawa 4:6, 7.

Ka ja layi a ƙarƙashin amsar kuma ka yi shirin yin furuci. Ka fahimci batun da ake son a tattauna sosai. Ka yi tunani a kan jigon talifin ko kuma babin, ka lura da alaƙar da ke tsakanin kowane ƙaramin jigo da ainihin jigon talifin, kuma ka bincika hotunan da ke talifin da kuma tambayoyin bita da suke nuna muhimman darussa. Ka karanta duk wani nassin da aka ambata a talifin, kuma ka yi tunani a kan yadda suka goyi bayan abin da ake tattaunawa. (Ayyukan Manzanni 17:11) Sa’ad da ka gano amsar tambayar, ka ja layi a ƙarƙashin kalmomin da za su taimaka maka ka tuna amsar da kake son ka bayar. Sa’an nan a taro, kana iya ɗaga hannu don ka yi furuci bisa abin da ka fahimta daga talifin.

Idan kana bincika batutuwa dabam-dabam da ake tattaunawa a taro a kowane mako, iliminka na Littafi Mai Tsarki zai ƙaru.—Matta 13:51, 52.

  • Wane irin tsari ne za ka bi don ka shirya abubuwan da za a tattauna a taro?

  • Ta yaya za ka yi shiri don ka yi furuci a taro?