Koma ka ga abin da ke ciki

Koma ga abubuwan da ke ciki

DARASI NA 21

Wane Irin Wuri Ne Bethel?

Wane Irin Wuri Ne Bethel?

Sashen Yin Zane, a Amirka

Jamus

Kenya

Kolombiya

Kalmar nan ta Ibrananci, Bethel, tana nufin “Gidan Allah.” (Farawa 28:17, 19) Wannan sunan ya dace sosai da gine-ginen da Shaidun Jehobah suke amfani da su a faɗin duniya, inda ake tallafa wa da kuma tsara aikin wa’azi. Hukumar da ke Kula da Ayyukan Shaidun Jehobah tana da zama ne a hedkwatar da ke Birnin New York, a Amirka, kuma daga can ne take lura da ayyukan da ake yi a ofisoshin reshe da ke ƙasashe da yawa. A matsayin rukuni, ana kiran waɗanda suke hidima a waɗannan wuraren, iyalin Bethel. Kamar iyali, suna zaune wuri ɗaya kuma suna aiki tare, suna cin abinci tare, kuma suna yin nazarin Littafi Mai Tsarki tare cikin haɗin kai.—Zabura 133:1.

Wuri ne na musamman da ake aiki tare kamar iyali kuma da sadaukarwa. A duk inda Bethel yake, akwai Kiristoci maza da mata waɗanda suka ba da kansu don su yi nufin Allah kuma suna biɗar Mulkinsa farko a rayuwarsu. (Matta 6:33) Ba a biyan su albashi, amma suna da wurin kwanciya mai kyau da lafiyayyen abinci kuma ana ba su ɗan ƙaramin alawus don su biya wa kansu ƙananan bukatun da suke da shi. Duk wani mutumin da ke Bethel yana da aikin yi, wataƙila a ofishi ko wurin dafa abinci ko kuma a wurin da ake cin abinci. Wasu suna aiki a inda ake buga littattafai, wasu suna share ɗakuna, wasu suna wanki da guga, wasu suna gyara, da dai sauran su.

Wuri ne da ake aiki tuƙuru don tallafa wa aikin wa’azi. Ainihin aikin da ake yi a kowane Bethel shi ne taimaka wa mutane da yawa su san gaskiyar da ke cikin Littafi Mai Tsarki. Wannan ƙasidar tana ɗaya daga cikin hanyoyin da ake yin hakan. An rubuta ta ne a ƙarƙashin ja-gorancin Hukumar da ke Kula da Ayyukan Shaidun Jehobah, kuma an aika ta zuwa ɗarurruwan rukunonin mafassara da ke faɗin duniya ta hanyar kwamfuta, an buga ta a maɗaba’o’i a Bethel dabam-dabam, kuma an tura ta zuwa ikilisiyoyi sama da 110,000. A dukan sassan nan, waɗanda suke hidima a Bethel suna tallafa wa aiki mafi gaggawa a yau, wato, wa’azin bishara.—Markus 13:10.

  • Su wane ne suke hidima a Bethel kuma ta yaya ake kula da su?

  • Wane aiki mafi gaggawa ne ake tallafa wa a kowane Bethel?