Koma ka ga abin da ke ciki

Koma ga abubuwan da ke ciki

DARASI NA 7

Yaya Ake Gudanar da Taronmu?

Yaya Ake Gudanar da Taronmu?

New Zealand

Jafan

Yuganda

Lithuania

A dukan taron da Kiristoci na farko suka yi, sun yi waƙoƙi da addu’o’i, sun karanta Nassi kuma sun tattauna shi. (1 Korintiyawa 14:26) Irin abin da muke yi a wajen taronmu a yau ke nan.

An ɗauko abin da ake koyarwa a taron ne daga Littafi Mai Tsarki kuma hakan yana da amfani. A ƙarshen mako, ’yan’uwanmu a kowace ikilisiya suna yin taro don su saurari jawabin da aka ɗauko daga Littafi Mai Tsarki na minti 30, a kan yadda Nassi ya shafi rayuwarmu da kuma zamanin da muke ciki a yau. Ana ƙarfafa dukanmu mu buɗe namu Littafi Mai Tsarki sa’ad da ake karantawa. Bayan an kammala jawabin, ana yin Nazarin “Hasumiyar Tsaro” na tsawon awa guda, kuma ana ba masu sauraro damar yin furuci sa’ad da ake tattauna talifin da aka ɗauko daga Hasumiyar Tsaro. Wannan tattaunawar tana taimaka mana mu yi amfani da shawarar da ke cikin Littafi Mai Tsarki a rayuwarmu. Ana nazarin talifi iri ɗaya a ikilisiyoyi sama da 110,000 a faɗin duniya.

Ana taimaka mana mu kyautata yadda muke koyarwa. Muna kuma gudanar da taro mai sassa uku da yamma a tsakiyar mako mai jigo Rayuwa ta Kirista da Hidimarmu da ke Littafin Taro don Rayuwa ta Kirista da Hidimarmu. Sashe na farko, wato Darussa Daga Kalmar Allah yana taimaka mana mu tattauna wasu surorin Littafi Mai Tsarki waɗanda ’yan’uwa sun riga sun karanta kafin su zo taron. Sashe na biyu kuma shi ne, Ka Yi Wa’azi da Ƙwazo, kuma a wannan sashen za a yi gwaji da suke taimaka mana mu kyautata yadda muke wa mutane wa’azi. Akwai mashawarci da zai ba mu shawara da za ta taimaka mana mu kyautata yadda muke karatu da kuma ba da jawabi. (1 Timotawus 4:13) Sashe na ƙarshe shi ne Rayuwar Kirista, wannan sashen na taimaka mana mu san yadda za mu yi amfani da ƙa’idodin Littafi Mai Tsarki a rayuwarmu na yau da kullum. Kuma ana tattauna wasu tambayoyi da amsoshi da suke taimaka mana mu fahimci Littafi Mai Tsarki sosai.

Babu shakka, idan ka halarci taronmu, za ka ji daɗin koyarwa mai kyau da muke yi daga Littafi Mai Tsarki.—Ishaya 54:13.

  • Mene ne za ji sa’ad da ka halarci taron Shaidun Jehobah?

  • Wanne cikin taronmu na mako-mako za ka so ka halarta a nan gaba?