Koma ka ga abin da ke ciki

Koma ga abubuwan da ke ciki

DARASI NA 6

Yaya Yin Tarayya da ’Yan’uwanmu Kiristoci Zai Amfane Mu?

Yaya Yin Tarayya da ’Yan’uwanmu Kiristoci Zai Amfane Mu?

Madagaska

Norway

Labanan

Italiya

Muna halartan taron Kirista babu fashi, ko da za mu bi kurmi ne don mu isa wurin, ko ana ruwa ko ana rana. Amma, me ya sa Shaidun Jehobah suke ƙoƙartawa sosai su kasance tare da ’yan’uwansu masu bi a taro, duk da matsaloli na rayuwa da kuma gajiyar aiki?

Yana taimaka mana mu jimre da matsaloli. Sa’ad da Bulus yake magana game da waɗanda muke cuɗanya da su a cikin ikilisiya, ya ce “mu lura da juna.” (Ibraniyawa 10:24) Abin da wannan furucin yake nufi shi ne, muna bukatar mu san juna sosai. Saboda haka, kalmomin manzon nan suna ƙarfafa mu ne mu riƙa kula da ’yan’uwanmu masu bi. Idan muka ƙoƙarta muka san sauran ’yan’uwanmu Kiristoci da ke cikin ikilisiya, hakan zai sa mu ga cewa wasu daga cikinsu sun taɓa fama da irin matsalar da muke fuskanta, kuma za su iya taimaka mana mu warware namu matsalolin.

Yana ƙarfafa abotar da ke tsakaninmu. Waɗanda muke cuɗanya da su a wajen taronmu, ba waɗanda muka yi wa sanin shanu ba ne, amma abokanmu ne na kud da kud. A wasu lokatai, muna yin nishaɗi mai kyau tare. Wane amfani ne muke samu daga irin wannan cuɗanyar? Tana sa mu ƙara riƙe juna hannu bibiyu, kuma hakan yana ƙarfafa ƙaunar da ke tsakaninmu. Sa’ad da ’yan’uwanmu maza da mata suke fuskantar matsaloli, muna taimaka musu nan da nan saboda abota mai kyau da ke tsakaninmu. (Misalai 17:17) Domin muna tarayya da dukan waɗanda suke cikin ikilisiyarmu, mu nuna cewa muna yi “wa juna tattali ɗaya.”—1 Korintiyawa 12:25, 26.

Muna ƙarfafa ka ka ƙulla abota da waɗanda suke yin nufin Allah. Za ka samu irin waɗannan abokan a tsakanin Shaidun Jehobah. Don Allah kada ka bari wani abu ya hana ka yin tarayya da mu.

  • Me ya sa yake da muhimmanci mu halarci taro tare da ’yan’uwanmu?

  • A yaushe ne za ka so ka halarci taro don ka san Shaidun da ke cikin ikilisiyarmu sosai?