Koma ka ga abin da ke ciki

Koma ga abubuwan da ke ciki

DARASI NA 23

Yaya Ake Rubuta da Fassara Littattafanmu?

Yaya Ake Rubuta da Fassara Littattafanmu?

Sashen Rubuce-Rubuce, a Amirka

Koriya ta Kudu

Armeniya

Burundi

Sri Lanka

Muna buga littattafai a harsuna wajen 750, kuma muna ƙoƙartawa mu yi wa’azin “bishara” ga ‘kowane irin mutum da ƙabila da harshe da al’umma.’ (Ru’ya ta Yohanna 14:6) Ta yaya muke cim ma wannan gagarumin aikin? Muna yin hakan ne da taimakon wasu marubuta da ke faɗin duniya da kuma rukunin mafassara masu ƙwazo kuma Shaidun Jehobah ne dukansu.

Ana rubutun ne ainihi a Turanci. Hukumar da ke Kula da Ayyukan Shaidun Jehobah ce take kula da Sashen Rubuce-Rubuce da ke hedkwatarmu. Wannan sashen ne ke kula da aikin marubutan da ke hedkwata da kuma wasu ofisoshin reshe. Marubutan da muke da su a wurare dabam-dabam ne ya sa muke rubuta batutuwan da suka shafi mutane daga al’adu dabam-dabam, don mutane a ko’ina su so karanta littattafanmu.

Ana aika rubutun ga mafassara. Bayan an tabbatar da cewa abin da aka rubuta daidai ne, kuma an ba da izinin buga shi, sai a aika rubutun ta hanyar na’urar kwamfuta zuwa mafassara da ke faɗin duniya don su fassara ta, kuma su tabbatar da cewa fassarar ta yi daidai. Suna ƙoƙartawa su yi amfani da “kalmomin gaskiya” waɗanda za su bayyana ainihin abin da aka ce a Turanci zuwa harshensu.—Mai-Wa’azi 12:10.

Na’urorin kwamfuta suna hanzarta aikin. Na’urar kwamfuta ba za ta yi aikin masu rubutu da mafassara ba. Amma, aikinsu zai fi sauri idan suka yi amfani da kwamfuta da kuma littattafan binciken da ke cikinta. Shaidun Jehobah sun tsara abin ake kira Multilanguage Electronic Publishing System (MEPS). Wannan fasaha ce da take iya ɗaukan rubutu a harsuna dabam-dabam tare da hotunan da ke cikinsu, sa’an nan ta haɗa su tare don a buga su.

Me ya sa muke irin wannan yunƙurin, har ma a harsunan da ’yan dubbai ne kawai suke yin su? Muna yin hakan ne domin nufin Jehobah shi ne, “dukan mutane su tsira, kuma su kawo ga sanin gaskiya.”—1 Timotawus 2:3, 4.

  • Yaya ake rubuta littattafanmu?

  • Me ya sa muke fassara littattafanmu zuwa harsuna da yawa?