Koma ka ga abin da ke ciki

Koma ga abubuwan da ke ciki

DARASI NA 17

Yaya Masu Kula Masu Ziyara Suke Taimaka Mana?

Yaya Masu Kula Masu Ziyara Suke Taimaka Mana?

Malawi

Rukunin fita wa’azi

Yin wa’azi

Taron dattawa

Sau da yawa, Nassin Helenanci na Kirista ya ambaci sunan Barnaba da manzo Bulus. Mutanen nan masu kula masu ziyara ne kuma sun ziyarce ikilisiyoyi a ƙarni na farko. Me ya sa? Sun damu sosai da zaman lafiyar ’yan’uwansu masu bi. Bulus ya ce yana so ya ‘koma ya ziyarci ’yan’uwa’ domin ya ga yadda suke. Ya yi tafiya ta ɗarurruwan mil ko kilomita domin ya ƙarfafa su. (Ayyukan Manzanni 15:36) Abin da masu kula masu ziyara da muke da su a yau suke yi ke nan.

Suna kawo ziyara ne don su ƙarfafa mu. Kowane mai kula da da’ira yana ziyartar ikilisiyoyi wajen 20 a shekara, kuma yana ziyartar kowace ikilisiya sau biyu a shekara. Za mu amfana sosai daga labaran waɗannan ’yan’uwan da na matansu idan suna da aure. Suna ƙoƙartawa su san tsofaffi da matasan da ke cikin ikilisiya kuma suna ɗokin fita tare da mu zuwa wa’azi da kuma gudanar da nazarin Littafi Mai Tsarki da mutane. Waɗannan masu kula suna kai ziyarar ƙarfafawa tare da dattawa kuma suna ƙarfafa mu da jawaban da suke ba da wa a ikilisiyoyi da manyan taro.—Ayyukan Manzanni 15:35.

Suna kula da kowa a cikin ikilisiya. Masu kula da da’ira suna son dukan waɗanda suke cikin ikilisiya su kasance da dangantaka mai kyau da Jehobah. Suna yin taro da dattawa da bayi masu hidima domin su tattauna ci gabar da aka samu kuma su shawarce su a kan yadda za su cika hakkokin da aka ba su. Suna taimaka wa majagaba su yi nasara a hidimarsu, kuma suna murnar sanin sababbi a cikin ikilisiya da kuma ci gaban da suke samu a bautarsu ga Jehobah. ’Yan’uwan nan sun ba da kansu a matsayin ‘abokan aiki’ don su taimaka mana. (2 Korintiyawa 8:23) Ya kamata mu yi koyi da bangaskiyarsu da kuma yadda suke bauta wa Allah.—Ibraniyawa 13:7.

  • Me ya sa masu kula da da’ira suke ziyartar ikilisiyoyi?

  • Ta yaya za ka amfana daga ziyararsu?