Koma ka ga abin da ke ciki

Koma ga abubuwan da ke ciki

DARASI NA 11

Me Ya Sa Muke Halartan Manyan Taro?

Me Ya Sa Muke Halartan Manyan Taro?

Meziko

Jamus

Botswana

Nicaragua

Italiya

Me ya sa mutanen nan suke cike da farin ciki? Suna farin ciki ne domin sun halarci ɗaya daga cikin manyan taronmu. Kamar bayin Allah na dā, da aka ba umurni cewa su riƙa taruwa sau uku a shekara, muna farin cikin halartan manyan taro tare da ’yan’uwanmu. (Kubawar Shari’a 16:16) A kowace shekara, muna halartan manyan taro guda uku: taron da’ira na kwana ɗaya guda biyu da kuma taron yanki na kwana uku. Ta yaya muke amfana daga waɗannan manyan taron?

Suna ƙarfafa haɗin kan da ke tsakanin Kiristoci na gaskiya. Kamar yadda Isra’ilawa suka yi farin ciki sa’ad da suke yabon Jehobah a “cikin taron jama’a,” mu ma muna farin cikin bauta masa tare da ’yan’uwanmu a irin waɗannan manyan taro na musamman. (Zabura 26:12; 111:1) Waɗannan taron suna ba mu zarafin yin zumunta da ’yan’uwanmu Shaidu da suke zuwa daga ikilisiyoyi da jihohi dabam-dabam ko kuma wasu ƙasashe. Da rana, muna murnar cin abinci tare da ’yan’uwanmu a wurin taron, kuma hakan yana ba mu zarafin yin abokai. (Ayyukan Manzanni 2:42) A waɗannan manyan taron ne muke shaida ƙaunar da take sa ‘’yan’uwanmu’ a faɗin duniya su kasance da haɗin kai.—1 Bitrus 2:17.

Suna taimaka mana mu kyautata dangantakarmu da Jehobah. Isra’ilawa sun amfana sa’ad da suka “fahimci zantattukan” da ke cikin Nassin da aka bayyana musu. (Nehemiya 8:8, 12) Mu ma muna amfana sosai daga abubuwan da aka koya mana daga Littafi Mai Tsarki a waɗannan manyan taron. Ana ɗauko kowane jigo ne daga Nassi. Jawabai masu daɗi da magana daki-daki da kuma sake nuna abubuwan da suke faruwa a rayuwa ta yau da kullum suna koya mana yadda za mu yi nufin Allah. Muna samun ƙarfafawa sa’ad da muka ji labaran ’yan’uwanmu da suka sha kan ƙalubale don su riƙe bangaskiyarsu a matsayin Kiristoci a waɗannan lokatai masu wuya. A taron yanki, wasan kwaikwayo yana sa mu fahimci labaran Littafi Mai Tsarki sosai kuma hakan yana koya mana darussa masu amfani. A kowane babban taro, ana yi wa waɗanda suka keɓe kansu ga Allah baftisma.

  • Me ya sa muke farin ciki sa’ad da muka halarci manyan taro?

  • Ta yaya za ka amfana daga halartan babban taro?