Koma ka ga abin da ke ciki

Koma ga abubuwan da ke ciki

DARASI NA 14

Wace Makaranta Ce Aka Shirya don Majagaba?

Wace Makaranta Ce Aka Shirya don Majagaba?

Amirka

Makarantar Gilead, a Patterson, New York

Panama

Shaidun Jehobah sun daɗe suna samun koyarwa daga Allah. Ana koyar da masu wa’azi na cikkaken lokaci a hanya ta musamman don su ‘cika hidimarsu.’—2 Timotawus 4:5.

Makarantar Hidima ta Majagaba. Ana gayyatar majagaban da ya yi shekara ɗaya yana hidimar majagaba zuwa wannan makarantar na tsawon kwana shida. Ana iya yin wannan makarantar a Majami’ar Mulki da ke yankinsu. An kafa makarantar ne don a taimaka wa majagaba ya daɗa kusantar Jehobah, ya ƙware sosai a dukan fannonin yin wa’azi kuma ya ci gaba da hidimarsa.

Makarantar Masu Yaɗa Bisharar Mulki. Makarantar tana ɗaukan watanni biyu, kuma an tsara ta ne don a horar da ƙwararrun majagaba waɗanda za su yarda su bar yankinsu kuma su je hidima a duk inda ake da bukata. Waɗannan majagaban suna yin koyi da Yesu Kristi, Mai Bishara mafi girma kuma suna cewa, “Ga ni; ka aike ni.” (Ishaya 6:8; Yohanna 7:29) Barin gida zai iya sa ya wajaba su sauƙaƙa salon rayuwarsu. Al’adar wurin da yanayin garin da abincinsu zai iya bambanta da wanda suka saba da shi. Wataƙila za su bukaci koyon sabon yare. Makarantar tana taimaka wa ’yan’uwa maza da mata marasa aure da ma’aurata masu shekaru 23 zuwa 65 su sami halaye masu kyau da za su taimaka musu a hidimarsu. Kuma hakan zai sa Jehobah da ƙungiyarsa su yi amfani da su sosai.

Makarantar Littafi Mai Tsarki na Gilead. A Ibrananci, kalmar nan “Gilead” tana nufin “Shaidu Masu Yawa.” Tun daga lokacin da aka kafa makarantar Gilead a shekara ta 1943, an tura sama da ɗalibai 8,000 da suka sauke karatu daga makarantar zuwa ‘iyakar duniya’ don yin wa’azi kuma an sami sakamako mai kyau. (Ayyukan manzanni 13:47) Sa’ad da ɗaliban da suka sauke karatu suka je ƙasar Peru, babu ikilisiyoyi a wurin. Amma a yau, akwai shaidu sama da 1,000. Sa’ad da aka tura masu wa’azi a ƙasashen waje zuwa ƙasar Jafan, Shaidu ba su kai goma ba a ƙasar baki ɗaya. Amma, akwai shaidu sama da 200,000 a ƙasar a yau. Ana yin nazarin Littafi Mai Tsarki dalla-dalla a cikin watanni biyar da ake gudanar da makarantar. ’Yan’uwan da ake gayyata zuwa makaranta su ne majagaba na musamman da masu wa’azi a ƙasashen waje da ba su halarta ba tukun da masu hidima a Bethel da kuma masu kula masu ziyara. Ana koyar da su domin su taimaka wajen kyautata da kuma ƙarfafa aikin da ake yi a faɗin duniya.

  • Mene ne manufar Makarantar Hidima ta Majagaba?

  • Su waye ne za su iya halartar Makarantar Masu Yaɗa Bisharar Mulki?