Koma ka ga abin da ke ciki

Koma ga abubuwan da ke ciki

DARASI NA 26

Yaya Za Mu Taimaka Wajen Kula da Majami’ar Mulki?

Yaya Za Mu Taimaka Wajen Kula da Majami’ar Mulki?

Estoniya

Zimbabwe

Mongoliya

Puerto Rico

Kowace Majami’ar Mulki na Shaidun Jehobah tana amsa suna mai tsarki na Allah. Saboda haka, a wajen mu, gata ne mu kula da ginin kuma mu share shi don ya kasance da tsabta, domin hakan sashe ne mai muhimmanci na bautarmu. Dukan waɗanda suke cikin ikilisiya za su iya yin waɗannan ayyukan.

Ka taimaka ka yi shara bayan taro. Bayan kowane taro, ’yan’uwa maza da mata suna share Majami’ar Mulki don ta kasance da tsabta, kuma suna yin hakan da farin ciki. Amma, a lokaci-lokaci, suna tsabtace wurin sosai. Dattijo ko bawa mai hidima ne yake kula da aikin, kuma a yawancin lokaci, yana bin tsarin da aka rubuta ne na abubuwan da za a yi. Daidai da bukatun da ake da shi, ’yan’uwa suna taimakawa wajen yin shara kuma suna goge daɓe tare da tagogi da kujeru, suna kuma wanke ban ɗaki su zubar da shara, ko kuma su tsabtace dukan mahallin. Aƙalla a kowace shekara, ana keɓe rana guda don tsabtace Majami’ar Mulki gabaki ɗaya. Sa’ad da yaranmu suka yi wasu daga cikin ayyukan nan, muna koya musu su daraja wurin bautarmu.—Mai-Wa’azi 5:1.

Ka taimaka sa’ad da ake duk wani gyare-gyare. A kowace shekara, ana bincika Majami’ar Mulki, ciki da waje. Bisa ga wannan binciken ne ake yin gyare-gyaren da ake bukata saboda majami’ar ta ci gaba da kasancewa da kyaun gani, kuma hakan zai rage yawan kuɗin da ake kashewa wajen yin gyara. (2 Labarbaru 24:13; 34:10) Ya cancanta mu bauta wa Allah a Majami’ar Mulki mai tsabta, wadda ake kula da ita sosai. Idan muka taimaka wajen yin wannan aikin, muna nuna cewa muna ƙaunar Jehobah kuma muna daraja wurin da muke bauta masa. (Zabura 122:1) Ƙari ga haka, mutane a yankinmu za su daraja Jehobah.—2 Korintiyawa 6:3.

  • Me ya sa bai kamata mu yi sakaci da wurin da muke bauta ba?

  • Wane tsari ne aka shimfiɗa don tsabtace Majami’ar Mulki?