Koma ka ga abin da ke ciki

Koma ga abubuwan da ke ciki

DARASI NA 13

Wane Ne Majagaba?

Wane Ne Majagaba?

Kanada

Suna wa’azi gida-gida

Nazarin Littafi Mai Tsarki

Nazarin Littafi Mai Tsarki na kai

“Majagaba” yana nufin mutumin da ya soma wani abu. Yesu yana kama ne da majagaba, domin an aiko shi ne zuwa duniya ya yi hidimar da za ta sa mutane su samu rai kuma ya buɗe hanyar da za su bi don su samu ceto. (Matta 20:28) A yau, mabiyansa suna bin misalinsa ta wajen ‘almajirtar da’ mutane sosai. (Matta 28:19, 20) Wasu sun shiga hidimar majagaba.

Majagaba shi ne mutumin da ke yawan yin wa’azi. Dukan Shaidun Jehobah suna fita yin bishara. Amma, akwai wasu daga cikinsu da suka tsara ayyukansu don su yi hidimar majagaba na kullum, kuma suna awoyi 70 a kowace wata suna wa’azi. Don su cim ma hakan, yawancinsu suna aikin da zai ba su isashen lokaci. Akwai kuma waɗanda ake naɗawa su zama majagaba na musamman don su je su yi hidima a inda ake bukatar masu wa’azi sosai, kuma suna awoyi 130 ko kuma sama da hakan suna wa’azi a kowace wata. Majagaba sun gamsu da irin rayuwa mai sauƙi da suke yi, domin suna da gaba gaɗi cewa Jehobah zai biya bukatunsu. (Matta 6:31-33; 1 Timotawus 6:6-8) Waɗanda ba za su iya yin hidimar majagaba na cikakken lokaci ba suna iya zama majagaba na ɗan lokaci, kuma suna awoyi 30 ko 50 a wata suna wa’azi.

Ƙaunar da majagaba yake yi wa Allah da mutane ce ta sa yake wannan hidimar. Kamar Yesu, mun lura cewa mutane da yawa suna so su san Allah da kuma nufinsa, ruwa a jallo. (Markus 6:34) Amma muna da ilimin da zai taimaka musu yanzu, wanda zai sa su kasance da tabbataccen bege game da nan gaba. Ƙaunar da majagaba yake yi wa maƙwabcinsa ce take sa ya ba da lokacinsa da kuma kuzarinsa don ya taimaka wa mutane su ji bishara. (Matta 22:39; 1 Tasalonikawa 2:8) A sakamakon haka, bangaskiyarsa tana ƙara ƙarfi, zai kusaci Allah kuma farin cikinsa zai ƙaru.—Ayyukan Manzanni 20:35.

  • Wane ne majagaba?

  • Mece ce take motsa wasu su shiga hidimar majagaba ta cikakken lokaci?