Koma ka ga abin da ke ciki

Koma ga abubuwan da ke ciki

DARASI NA 20

Yaya Hukumar da ke Kula da Ayyukan Shaidun Jehobah Take Gudanar da Ayyukanta a Yau?

Yaya Hukumar da ke Kula da Ayyukan Shaidun Jehobah Take Gudanar da Ayyukanta a Yau?

Hukumar da ke kula da ikilsiyoyi a faɗin duniya a ƙarni na farko

Suna karanta wasiƙar da suka samu daga hukumar

A ƙarni na farko, wani ƙaramin rukuni na ‘manzanni da dattawa a Urushalima’ ne yake yanke shawarwari masu muhimmanci a madadin dukan ikilisiyoyi na shafaffun Kiristoci. (Ayyukan Manzanni 15:2) Kafin su tsai da shawara, suna tattauna abin da Nassi ya ce kuma suna bin ja-gorancin ruhun Allah. (Ayyukan Manzanni 15:25) Irin tsarin da ake bi ke nan a yau.

Allah yana amfani da ita wajen yin nufinsa. ’Yan’uwa maza shafaffu waɗanda suke hidima a matsayin Hukumar da ke Kula da Ayyukan Shaidun Jehobah suna son Kalmar Allah sosai, kuma sun ƙware wajen tsai da shawara a kan yadda za a gudanar da aikinmu da kuma amsa tambayoyi a kan batutuwan da suka shafi addini. Suna taro a kowane mako don su tattauna bukatun ’yan’uwa Kiristoci da ke faɗin duniya. Kamar yadda aka yi a ƙarni na farko, suna ba mu umurnin da suka ɗauko daga Littafi Mai Tsarki ta hanyar wasiƙu ko kuma masu kula masu ziyara da dai sauransu. Hakan yana sa mutanen Allah su kasance da haɗin kai a tunaninsu da ayyukansu. (Ayyukan Manzanni 16:4, 5) Hukumar da ke Kula da Ayyukan Shaidun Jehobah tana kula da yadda ake koya wa mutane game da Allah, tana ƙarfafa ’yan’uwa su yi wa’azin Mulki sosai kuma tana kula da yadda ake naɗa ’yan’uwan da za su yi hidima a ikilisiya.

Tana bin ja-gorancin ruhun Allah. Hukumar da ke Kula da Ayyukan Shaidun Jehobah tana bin ja-gorancin Jehobah, Mamallakin Sararin Samaniya, da kuma na Yesu, wanda shi ne Shugaban ikilisiya. (1 Korintiyawa 11:3; Afisawa 5:23) Waɗanda suke rukunin nan ba sa ɗaukan kansu a matsayin shugabannin mutanen Allah. Su da sauran Kiristoci shafaffu suna ‘bin Ɗan rago [Yesu] duk inda ya tafi.’ (Ru’ya ta Yohanna 14:4) Hukumar da ke Kula da Ayyukan Shaidun Jehobah tana godiya sosai saboda addu’o’in da muke yi a madadinsu.

  • Su wane ne hukumar da ke kula da dukan ikilisiyoyi a ƙarni na farko?

  • Ta yaya Hukumar da ke Kula da Ayyukan Shaidun Jehobah a yau take biɗar ja-gorancin Allah?