Koma ka ga abin da ke ciki

Koma ga abubuwan da ke ciki

DARASI NA 28

Waɗanne Bayanai Ne Za Ka Iya Samu a Yanar Gizonmu?

Waɗanne Bayanai Ne Za Ka Iya Samu a Yanar Gizonmu?

Faransa

Poland

Rasha

Yesu Kristi ya gaya wa mabiyansa: “Ku bari haskenku shi haskaka a gaban mutane, domin su ga ayyukanku masu-kyau, su girmama Ubanku wanda ke cikin sama.” (Matta 5:16) Shi ya sa muke amfani sosai da fasaha ta zamani, har da Intane. Yanar Gizonmu, jw.org ne ainihin dandanlin da za a iya samun bayanai game da imani da kuma ayyukan Shaidun Jehobah. Waɗanne abubuwa ne za a iya samu a dandalin?

Amsoshi daga Littafi Mai Tsarki na tambayoyin da mutane suke yi a yau da kullum. Za ka iya samun amsoshin tambayoyi masu muhimmanci waɗanda mutane suka taɓa yi. Alal misali, za a iya samun warƙoƙin nan Wahala Za Ta Kare Kuwa? da kuma Matattu Za Su Sake Rayuwa Kuwa? a harsuna sama da 600 a dandalinmu. Za ka samu fassarar Littafi Mai Tsarki na New World Translation of the Holy Scriptures a harsuna sama da 130 da kuma littattafan da suka bayyana Littafi Mai Tsarki, har da littafin nan Menene Ainihi Littafi Mai Tsarki Yake Koyarwa? tare da Hasumiyar Tsaro da Awake! na kwanan nan. Za a iya karanta ko kuma a saurari karatun da dama daga cikin waɗannan littattafan ta hanyar Intane ko kuma a MP3 ko PDF ko kuma EPUB. Kana iya buga wasu shafuffuka don ka nuna wa mutumin da ke son gaskiya a harshensa! Ana samun bidiyo a yaren kurame da dama. Za ka iya sauko da wasan kwaikwayon da aka ɗauko daga Littafi Mai Tsarki, da kuma waƙoƙi masu daɗi.

Bayani na gaskiya game da Shaidun Jehobah. Har ila, akwai labarai da ɗimi-ɗiminsu tare da bidiyo game da aikinmu a faɗin duniya, da abubuwan da suke shafan Shaidun Jehobah da kuma ƙoƙarin da muke yi don mu taimaka wa waɗanda bala’i ya shafa. Za ka iya samun bayani game da taron gundumarmu da ke tafe da kuma adireshin ofisoshinmu na reshe.

Ta waɗannan hanyoyin ne muke haskaka gaskiyar da ke cikin Littafi Mai Tsarki a duk faɗin duniya. Mutane a dukan nahiyoyin duniya, har da Antarctica, suna amfana daga wannan shirin. Fatarmu ita ce ‘maganar Ubangiji ta ci gaba da yaɗuwa da sauri’ a faɗin duniya, kuma ɗaukaka ta kasance ga Allah.—2 Tasalunikawa 3:1.

  • Ta yaya jw.org yake taimaka wa mutane da yawa su koyi gaskiyar da ke cikin Littafi Mai Tsarki?

  • Mene ne za ka so ka bincika a Yanar gizonmu?