Koma ka ga abin da ke ciki

Koma ga abubuwan da ke ciki

DARASI NA 10

Mece Ce Bauta ta Iyali?

Mece Ce Bauta ta Iyali?

Koriya ta Kudu

Brazil

Ostareliya

Gini

Tun a zamanin dā, Jehobah ya bukaci kowace iyali ta keɓe lokaci domin ta ƙarfafa dangantakarta da Shi kuma iyalin ta ƙarfafa ƙaunar da suke yi wa juna. (Kubawar Shari’a 6:6, 7) Shi ya sa Shaidun Jehobah suke keɓe lokaci a kowane mako don kowace iyali ta yi nazarin Littafi Mai Tsarki, kuma ta tattauna batutuwan da suka shafi dangantakarta da Allah, hankali kwance. Ko da kana zaune ne kai kaɗai, kana iya yin amfani da wannan damar don ka ƙarfafa dangantakarka da Allah ta wajen yin nazarin batutuwan da kake so daga Littafi Mai Tsarki.

Lokaci ne na ƙara kusantar Jehobah. “Ku kusato ga Allah, shi kuwa za ya kusato gare ku.” (Yaƙub 4:8) Muna ƙara sanin Jehobah sa’ad da muka koyi halinsa da kuma ayyukansa daga Kalmarsa, Littafi Mai Tsarki. Hanya mai sauƙi ta fara bauta ta iyali a lokacin da kuka keɓe a kowane mako ita ce, ku yi amfani da wasu daga cikin wannan lokacin ku karanta Littafi Mai Tsarki tare, kuna iya bin tsarin taron Rayuwa ta Kirista da Hidimarmu na kowane mako. Kuna iya sa kowa a iyalinku ya karanta wani sashen Littafi Mai Tsarki da za a karanta a makon, bayan haka, sai ku tattauna abubuwan da kuka koya daga Nassin a matsayin iyali.

Lokaci ne da ke sa iyali su ƙara kusantar juna. Mazaje da matansu, da kuma iyaye da ’ya’yansu suna ƙarfafa dangantakar da ke tsakanin su sa’ad da suka yi nazarin Littafi Mai Tsarki tare. Ya kamata hakan ya zama abin da kowa a cikin iyalin zai riƙa sa rai a kowane mako. Iyaye za su iya zaɓan batutuwa masu amfani da za su tattauna daga wasu talifofin Hasumiyar Tsaro da sauran littattafai ko kuma daga dandalin jw.org daidai da shekarun yaransu. Kuna iya tattauna matsalar da yaranku suke fuskanta a makaranta da kuma yadda za su warware su. Ban da haka ma, zai yi kyau ku riƙa duba tashan da muke yaɗa shirye-shiryenmu a JW (tv.jw.org) kuma ku tattauna wasu darussa tare. Kuna iya yin waƙoƙin da za a rera a taro a makon kuma kuna iya jin daɗin ci-da-sha bayan bauta ta iyali.

Wannan lokaci na musamman da kuka keɓe a kowane mako don ku bauta wa Jehobah tare zai taimaka wa kowa a iyalin ya riƙa jin daɗin karanta Kalmar Allah, kuma Jehobah zai albarkaci ƙoƙarin da kuke yi.—Zabura 1:1-3.

  • Me ya sa muke keɓe lokaci don bauta ta iyali?

  • Ta yaya iyaye za su sa kowa a cikin iyali ya ji daɗin bauta ta iyali?