Koma ka ga abin da ke ciki

Koma ga abubuwan da ke ciki

 BABI NA SHA HUƊU

Yadda Iyalinka Za Ta Zauna Lafiya

Yadda Iyalinka Za Ta Zauna Lafiya

1, 2. Wace irin rayuwa ce Jehobah yake son iyalai su yi?

JEHOBAH ALLAH ne ya ɗaura aure na farko. Littafi Mai Tsarki ya gaya mana cewa sa’ad da Allah ya halicci mace ta farko, “ya kawo ta wurin mutumin.” Adamu ya yi farin ciki sosai, shi ya sa ya ce: “Wannan yanzu ƙashi ne daga ƙasusuwana, nama ne daga namana.” (Farawa 2:22, 23) Hakan ya nuna cewa Jehobah yana son ma’aurata su yi farin ciki.

2 Abin baƙin ciki shi ne, iyalai da yawa ba su taɓa yin farin ciki ba. Duk da haka, Littafi Mai Tsarki yana ɗauke da ƙa’idodin da za su taimaka wa kowa a cikin iyali su yi nasara kuma su zauna lafiya.—Luka 11:28.

ABIN DA ALLAH YAKE SON MAZAJE SU YI

3, 4. (a) Yaya ya kamata maigida ya bi da matarsa? (b) Me ya sa yake da muhimmanci mata da miji su riƙa gafarta wa juna?

3 Littafi Mai Tsarki ya ce ya kamata mijin kirki ya ƙaunaci matarsa kuma ya daraja ta. Don Allah ka karanta Afisawa 5:25-29. Zai dace miji ya riƙa bi da matarsa cikin ƙauna. Kuma ya kamata ya kāre ta, ya kula da ita kuma kada ya kuskura ya yi wani abin da zai jawo mata lahani.

4 Amma mene ne ya kamata maigida ya yi sa’ad da matarsa ta yi kuskure? Littafi Mai Tsarki ya ce: Ku riƙa “ƙaunar matayenku, kada kuwa ku yi fushi da su.”  (Kolosiyawa 3:19) Ya kamata mazaje su tuna cewa su ma suna yin kuskure. Kuma idan kana son Allah ya gafarce ka, dole ne ka gafarta wa matarka. (Matta 6:12, 14, 15) Idan mata da miji suna gafarta wa juna, hakan zai taimaka musu su zauna lafiya.

5. Me ya sa ya kamata maigida ya daraja matarsa?

5 Jehobah yana son maigida ya daraja matarsa. Ya kamata maigida ya yi tunani sosai game da bukatun matarsa. Wannan ba batun wasa ba ne. Idan maigida ya wulaƙanta matarsa, Jehobah zai iya ƙin jin addu’arsa. (1 Bitrus 3:7) Jehobah yana daraja mutanen da suke ƙaunarsa. Ba ya ɗaukan maza da daraja fiye da mata.

6. Mene ne Littafi Mai Tsarki yake nufi sa’ad da ya ce mata da miji “nama ɗaya” ne?

6 Yesu ya faɗa cewa mata da miji ‘ba biyu ba ne, amma nama ɗaya ne.’ (Matta 19:6) Ya kamata su kasance da aminci ga juna kuma kada su taɓa cin amanar juna. (Misalai 5:15-21; Ibraniyawa 13:4) Ya kamata mata da miji su riƙa mai da hankali ga bukatunsu na jima’i. (1 Korintiyawa 7:3-5) Zai dace maigida ya tuna cewa ‘babu mutum wanda ya taɓa ƙin jiki nasa; amma yakan ciyar da shi ya kuma kiyaye shi.’ Don haka, ya kamata ya ƙaunaci matarsa kuma ya daraja ta. Mace ta fi son maigidanta ya yi mata alheri kuma ya ƙaunace ta sosai.—Afisawa 5:29.

ABIN DA ALLAH YAKE SON MATA SU YI

7. Me ya sa iyali take bukatar shugaba?

7 Kowace iyali tana bukatar shugaban da zai ba da ja-gora don iyalin ta kasance da haɗin kai. Littafin 1 Korintiyawa 11:3 ta ce: “Kan kowane namiji Kristi ne; kan mace kuma namiji ne; kan Kristi kuma Allah ne.”

8. Me zai taimaki mace ta yi wa mijinta ladabi sosai?

 8 Babu maigidan da ba ya kuskure. Idan mace ta goyi bayan shawarar maigidanta da zuciya ɗaya kuma suka kasance da haɗin kai, dukansu za su amfana. (1 Bitrus 3:1-6) Littafi Mai Tsarki ya ce: “Matan kuma ta ga kwarjinin mijinta.” (Afisawa 5:33) Idan addinin matar da na mijin ba ɗaya ba ne fa? Har ila, matar tana bukatar ta yi wa maigidan ladabi sosai. Littafi Mai Tsarki ya ce: ‘Matan aure, ku yi biyayya ga mazanku, don ko waɗansunsu ba su bi maganar Allah ba, halin matansu yā shawo kansu, ba tare da wata magana ba, don ganin tsarkakakken halinku da kuma ladabinku.’ (1 Bitrus 3:1, 2, Littafi Mai Tsarki) Hali mai kyau na matar zai iya sa maigidan ya fahimci kuma ya daraja abin da ta yi imani da shi.

9. (a) Mene ne ya kamata mace ta yi sa’ad da ta sami saɓani da mijinta? (b) Wace shawara ce aka ba mu a littafin Titus 2:4, 5?

9 Mene ne ya kamata mata ta yi sa’ad da ta sami saɓani da mijinta? Ya kamata ta faɗi ra’ayinta cikin ladabi.  Alal misali, akwai lokacin da Saratu ta ba maigidanta Ibrahim wata shawara da bai so ba, amma Jehobah ya gaya masa: “Ka ji maganarta.” (Farawa 21:9-12) Idan maigida da Kirista ne ya tsai da wata shawara da ba ta saɓa wa dokar Allah ba, ya kamata matar ta goyi bayan shawarar. (Ayyukan Manzanni 5:29; Afisawa 5:24) Macen kirki tana kula da iyalinta. (Karanta Titus 2:4, 5.) Sa’ad da maigida da yara suka ga yadda mace take aiki da ƙwazo don su amfana, za su ƙaunace ta sosai.—Misalai 31:10, 28.

Ta yaya Saratu ta kafa misali mai kyau ga matan aure?

10. Mene ne Littafi Mai Tsarki ya faɗa game da rabuwa da kuma kashe aure?

10 A wasu lokuta, ma’aurata suna rabuwa da juna ko kuma suna kashe aurensu ba tare da yin tunani sosai ba. Amma, Littafi Mai Tsarki ya ce: “Kada matan ta rabu da mijinta,” ƙari ga haka, ‘mijin kuma kada ya rabu da matarsa.’ (1 Korintiyawa 7:10, 11) Akwai wasu abubuwan da za su iya sa ma’aurata su rabu da juna, amma wannan shawara ce babba. Kashe aure kuma fa? Dalili ɗaya da Littafi Mai Tsarki ya bayar na kashe aure shi ne idan ɗaya daga cikin ma’auratan ya yi lalata.—Matta 19:9.

ABIN DA ALLAH YAKE SON IYAYE SU YI

Yesu ya kafa misali mai kyau ga kowa a iyali

11. Wane abu mafi muhimmanci ne yara suke bukata?

11 Zai dace iyaye su riƙa ba yaransu lokacinsu sosai. Yaranku suna bukatarku, amma abin da ya fi muhimmanci shi ne ku koya musu game da Jehobah.—Kubawar Shari’a 6:4-9.

12. Mene ne iyaye za su yi don su kāre yaransu?

12 Duniyar nan tana daɗa lalacewa kuma akwai wasu mutanen da suke so su ci zarafin yaranku ta hanyar lalata. Ba abu mai sauƙi ba ne wasu iyaye su tattauna  wannan batun da yaransu. Amma iyaye suna bukatar su ja kunnen ’ya’yansu game da irin waɗannan mutanen kuma su koya musu yadda za su guje su. Wajibi ne iyaye su kāre yaransu. *1 Bitrus 5:8.

13. Ta yaya ya kamata iyaye su koyar da yaransu?

13 Iyaye ne suke da hakkin koyar da yaransu yadda za su kasance da hali mai kyau. Ta yaya za ka yi hakan? Yara suna bukatar horo, amma bai kamata ka yi hakan da rashin tausayi ko ɓacin rai ba. (Irmiya 30:11) Ƙari ga  haka, bai kamata iyaye su yi ma yaransu horo sa’ad da suke fushi ba. Kada furucinku ya zama kamar “sussukan takobi” da zai ɓata wa yaranku rai. (Misalai 12:18) Ku koyar da yaranku su fahimci dalilin da ya sa suke bukatar su riƙa yin biyayya.—Afisawa 6:4; Ibraniyawa 12:9-11; ka duba Ƙarin bayani na 30.

ABIN DA ALLAH YAKE SON YARA SU YI

14, 15. Me ya sa ya kamata yara su yi wa iyayensu biyayya?

14 A koyaushe, Yesu yana yin biyayya ga Ubansa ko da hakan bai da sauƙi. (Luka 22:42; Yohanna 8:28, 29) Jehobah yana son yara su riƙa yin biyayya ga iyayensu.—Afisawa 6:1-3.

15 Yara, ko da kuna ji kamar yana da wuya ku yi wa iyayenku biyayya, ku tuna cewa idan kuka yi biyayya, Jehobah da kuma iyayenku za su yi farin ciki sosai. *Misalai 1:8; 6:20; 23:22-25.

Me zai taimaka wa matasa su kasance da aminci ga Allah sa’ad da aka jarabce su?

16. (a) Ta yaya Shaiɗan yake ƙoƙarin sa matasa su yi abu marar kyau? (b) Me ya sa yake da kyau mu yi abokantaka da mutanen da suke bauta wa Jehobah?

16 Iblis zai iya yin amfani da abokai da kuma wasu matasa don su sa ka yi wani abin da bai dace ba. Ya san cewa irin wannan gwajin zai yi mana wuyan jimrewa. Alal misali, Dinah ’yar Yakubu ta yi abokantaka da mutanen da ba su bauta wa Jehobah ba. Hakan ya jawo mata da iyalinta masifa sosai. (Farawa 34:1, 2) Idan kana da abokai da ba sa bauta wa Jehobah, za su iya matsa maka ka yi wani abin da Jehobah ba ya so, kuma hakan zai iya jawo maka da iyalinka da kuma Allah baƙin ciki sosai. (Misalai 17:21, 25) Shi ya sa yake da kyau ka  yi abokantaka da mutanen da suke bauta wa Jehobah.—1 Korintiyawa 15:33.

YADDA IYALINKA ZA TA ZAUNA LAFIYA

17. Wane hakki ne kowa a cikin iyali yake da shi?

17 Idan kowa a cikin iyali yana bin umurnan Allah, ba za su riƙa faɗa cikin matsaloli ba. Saboda haka, idan kai maigida ne, ka ƙaunaci matarka kuma ka bi da ita cikin ƙauna. Idan ke matar aure ce, ki yi wa mijinki ladabi da biyayya kuma ki bi misalin macen da aka ambata a littafin Misalai 31:10-31. Idan ku iyaye ne, ku koya wa yaranku su ƙaunaci Allah. (Misalai 22:6) Idan kai uba ne, ka ja-goranci iyalinka “da kyau.” (1 Timotawus 3:4, 5; 5:8) Yara kuma su riƙa yin biyayya ga iyayensu. (Kolosiyawa 3:20) Ka tuna cewa kowa a cikin iyali zai iya yin kuskure, saboda haka, ka kasance da sauƙin kai kuma ka riƙa neman gafara. Hakika, Littafi Mai Tsarki yana ɗauke da shawarwarin da za su iya taimaka wa kowa a cikin iyali.

^ sakin layi na 12 Za ka iya samun ƙarin bayani game da yadda za ka kāre yaranka a babi na 32 na littafin nan Ka Koya Daga Wurin Babban Malami, Shaidun Jehobah ne suka wallafa shi.

^ sakin layi na 15 Bai kamata yara su yi biyayya ga iyayensu ba idan suka ce su yi wani abu da ya saɓa wa dokar Allah.—Ayyukan Manzanni 5:29.