Koma ka ga abin da ke ciki

Koma ga abubuwan da ke ciki

 BABI NA ƊAYA

Wane ne Allah?

Wane ne Allah?

1, 2. Waɗanne tambayoyi ne mutane suke yawan yi?

AN SAN yara da yin tambayoyi da yawa. Kana iya yi musu bayani, amma sai su ce maka, ‘Me ya sa?’ Bayan ka ƙara yi musu bayani, za su iya sake ce maka, ‘Amma me ya sa?’

2 Dukanmu muna yin tambayoyi kome girmanmu. Muna iya yin tambayoyi game da abin da za mu ci da kayan da za mu saka da kuma abin da muke so mu saya. Muna kuma iya yin muhimman tambayoyi game da rayuwa da kuma abin da zai faru a nan gaba. Amma idan ba mu gamsu da amsoshin tambayoyin ba, kada mu bar hakan ya sa mu daina neman amsoshin gabaki ɗaya.

3. Me ya sa mutane da yawa suke ji cewa ba za su iya samun amsoshi ga muhimman tambayoyinsu ba?

3 Littafi Mai Tsarki zai iya ba da amsoshi ga muhimman tambayoyin da muke yi kuwa? Wasu suna ganin haka, amma sun ce Littafi Mai Tsarki yana da wuyar fahimta sosai. Suna iya ji cewa malamai da firistoci ko kuma fastoci ne kaɗai za su iya ba da amsoshin. Wasu kuma ba sa so su faɗa cewa ba su san amsoshin ba domin ba sa so su sha kunya. Kai kuma fa?

4, 5. Waɗanne tambayoyi masu muhimmanci ne za ka so ka sami amsoshinsu? Me ya sa ya kamata ka ci gaba da neman amsoshin?

4 Babu shakka, kana so ka sami amsoshi ga tambayoyi kamar su: Me ya sa aka halicce ni? Me zai faru da ni sa’ad da na mutu? Mene ne Littafi Mai Tsarki ya ce game da Allah? Yesu, babban malami ya ce: ‘Ka yi ta roƙo, za a ba ka. Ka yi ta nema, za ka samu. Ka yi ta ƙwanƙwasawa, za a  kuwa buɗe maka.’ (Matta 7:7, Littafi Mai Tsarki) Saboda haka, ka ci gaba da neman amsoshi masu gamsarwa har sai ka samu.

5 Hakika, idan ka ci gaba da ‘neman’ amsoshin, za ka same su a cikin Littafi Mai Tsarki. (Misalai 2:1-5) Amsoshin ba su da wuyar fahimta. Abin da ka koya zai sa ka yi farin ciki a rayuwa yanzu kuma ka kasance da begen yin rayuwa a nan gaba. Bari mu tattauna wata tambaya da mutane da yawa ba su fahimta ba.

ALLAH YA DAMU DA MU KUWA KO SHI MARAR TAUSAYI NE?

6. Me ya sa wasu suke tunani cewa Allah bai damu da wahalar da suke sha ba?

6 Mutane da yawa suna tunani cewa Allah bai damu da mu ba. Suna ganin cewa idan Allah ya damu da su da gaske, duniya ba za ta kasance haka ba. Duniya tana cike da yaƙe-yaƙe da ƙiyayya da kuma wahala. Mutane suna ciwo da wahala da kuma mutuwa. Wasu suna iya ce, ‘Idan Allah ya damu da mu, to, me ya sa bai kawo ƙarshen wahala ba?’

7. (a) Mene ne malaman addinai suke faɗa da ke sa mutane tunani cewa Allah marar tausayi ne? (b) Me ya sa muka tabbata cewa ba Allah ne ke jawo munanan abubuwan da ke faruwa ba?

7 A wasu lokuta, malaman addinai suna sa mutane su ɗauka cewa Allah marar tausayi ne. Idan wani bala’i ya faru, suna ce hakan nufin Allah ne ko kuma haka Allah ya ƙaddara. Sa’ad da suka ce haka, suna ɗora wa Allah laifi. Amma Littafi Mai Tsarki ya ce ba Allah ne ke jawo munanan abubuwan da ke faruwa ba. Littafin Yaƙub 1:13 ya ce Allah ba ya jarraba kowannenmu da munanan abubuwa ba. Ayar ta ce: “Kada kowa sa’ad da ya jarabtu ya ce, daga wurin Allah ne na jarabtu: gama Allah ba ya  jarabtuwa da mugunta, shi kuwa da kansa ba ya jarabtan kowa.” Hakan yana nufin cewa ko da yake Allah bai kawar da munanan abubuwa ba tukun, ba shi yake sa su faru ba. (Karanta Ayuba 34:10-12.) Ga wani misali.

8, 9. Me ya sa bai dace mu ɗora wa Allah laifi don matsalolin da muke fuskanta ba? Ka ba da misali.

8 A ce wani saurayi yana zama tare da iyayensa. Mahaifinsa yana ƙaunarsa sosai kuma ya yi masa tarbiyya mai kyau. Sai wata rana ya yi tawaye da mahaifinsa kuma ya bar gida. A can, ya soma yin abubuwa marar kyau kuma ya faɗa cikin matsala. Shin za ka ga mahaifinsa da laifi ne domin bai hana yaron barin gida ba? A’a! (Luka 15:11-13) Kamar yadda wannan mahaifin bai hana ɗansa barin gida ba, Allah ma bai hana mutane yanke shawarar da suke so ba ko da suna so su yi tawaye ne. Saboda haka, idan wani mugun abu ya faru, bai kamata mu ɗauka cewa Allah ne ya sa ya faru ba. Ba zai dace mu ga Allah da laifi ba.

9 Akwai dalilin da ya sa Allah bai cire munanan abubuwa ba tukun. Za ka koyi abin da Littafi Mai Tsarki ya ce game da wannan batun a Babi na 11. Amma ya kamata ka kasance da tabbaci cewa Allah yana ƙaunarmu kuma ba shi yake jawo matsalolin da muke fuskanta ba. Hakika, Shi kaɗai ne zai iya cire matsalolin.—Ishaya 33:2.

10. Me ya tabbatar mana cewa Allah zai gyara dukan abubuwan da miyagu suka ɓata?

10 Allah mai tsarki ne. (Ishaya 6:3) Dukan ayyukansa suna da tsarki da kuma kyau. Saboda haka, za mu iya dogara da shi. Ba haka ’yan Adam suke ba. A wasu lokuta, suna yin abubuwan da ba su dace ba. Har shugaba mafi kirki bai da iko ya gyara dukan abubuwan da miyagu suka ɓata. Allah ya fi kowa iko. Yana da iko ya gyara dukan abubuwan da miyagu suka ɓata kuma babu shakka, zai yi hakan.  Zai cire dukan munanan abubuwa kuma ba za su sake kasancewa ba.—Karanta Zabura 37:9-11.

YAYA ALLAH YAKE JI IDAN YA GA MUTANE SUNA SHAN WAHALA?

11. Yaya Allah yake ji game da wahalar da kake sha?

11 Yaya Allah yake ji sa’ad da ya ga abubuwan da ke faruwa a duniya da kuma waɗanda kake fuskanta? Littafi Mai Tsarki ya ce Allah yana son “adalci.” (Zabura 33:5) Saboda haka, yana son abubuwa masu kyau kuma yana ƙin abubuwa marasa kyau. Ba ya farin ciki sa’ad da mutane suke shan wahala. Littafi Mai Tsarki ya ce ran Allah ya ‘ɓace’ sosai sa’ad da ya ga duniya ta cika da mugunta a zamanin dā. (Farawa 6:5, 6) Allah bai canja ba. (Malakai 3:6) Littafi Mai Tsarki ya ce Allah ya damu da kai ƙwarai.—Karanta 1 Bitrus 5:7.

Littafi Mai Tsarki ya ce Jehobah Allah mai ƙauna ne, kuma shi ya halicci sama da ƙasa

12, 13. (a) Me ya sa muke ƙauna da kuma kula da wasu, kuma yaya muke ji game da wahalar da mutane suke sha a duniya? (b) Me ya tabbatar mana cewa Allah zai cire dukan wahala da rashin adalcin da ke faruwa?

12 Littafi Mai Tsarki kuma ya ce Allah ya halicce mu a cikin siffarsa. (Farawa 1:26) Hakan yana nufin cewa Allah ya halicce mu da halaye masu kyau irin nasa. Saboda haka, idan ranka yana ɓacewa sa’ad da ka ga wani marar laifi yana shan wahala, to, ka san cewa hakan ya ma fi damun Allah! Me ya sa muka tabbata da hakan?

13 Littafi Mai Tsarki ya koya mana cewa “Allah ƙauna ne.” (1 Yohanna 4:8) Ƙauna ce ke sa Allah ya yi dukan abubuwan da yake yi. Muna ƙauna domin Allah ma yana ƙauna. Ka yi la’akari da wannan: Shin za ka cire wahala da rashin adalci a duniya idan kana da ikon yin hakan? Babu shakka, za ka yi hakan, domin kana ƙaunar mutane. Allah kuma fa? Yana da iko, kuma zai cire dukan wahala da  rashin adalci a duniya domin yana ƙaunarmu. Ka kasance da tabbaci cewa Allah zai cika dukan alkawuran da ya yi da muka ambata a farkon wannan littafin! Amma kana bukatar ka san Allah sosai domin ka amince da waɗannan alkawuran.

ALLAH YANA SO KA SAN SHI

Idan kana so ka zama abokin wani, za ka gaya masa sunanka. Allah ya gaya mana sunansa a cikin Littafi Mai Tsarki

14. Mene ne sunan Allah, kuma me ya tabbatar mana cewa ya kamata mu yi amfani da shi?

14 Idan kana so ka zama abokin wani, mene ne kake fara gaya masa game da kanka? Sunanka, ko ba haka ba? Shin Allah yana da suna ne? Addinai da yawa sun ce sunansa Allah ne ko Ubangiji, amma waɗannan laƙabi ne ba sunaye ba. Laƙabi ne kamar “sarki” ko “shugaban ƙasa.” Allah ya gaya mana cewa sunansa Jehobah ne. Zabura 83:18 ta ce: ‘Domin su sani kai, wanda sunanka Jehobah ne, kai kaɗai ne Maɗaukaki bisa dukan duniya.’ Marubutan Littafi Mai Tsarki sun rubuta sunan Allah fiye da sau dubu bakwai a cikin Littafi Mai Tsarki. Jehobah yana so ka san sunansa kuma ka yi amfani da shi. Shi ya sa ya ba ka damar sanin sunansa domin ka zama amininsa.

15. Mene ne ma’anar sunan nan Jehobah?

15 Sunan nan Jehobah,  yana da ma’ana sosai. Yana nufin cewa Allah zai iya cika dukan alkawuransa kuma ya cim ma nufinsa. Babu abin da zai iya hana shi yin hakan. Jehobah ne kaɗai ya cancanci a kira shi da wannan sunan. *

16, 17. Mene ne ma’anar (a) “Mai-iko duka”? (b) “Sarkin zamanai”? (c) “Mahalicci”?

16 Kamar yadda muka karanta ɗazun, Zabura 83:18 ta  ce game da Jehobah: ‘Kai kaɗai ne Maɗaukaki.’ Ru’ya ta Yohanna 15:3 kuma ta ce: ‘Ayyukanka masu-girma ne, masu-ban al’ajabi, ya Ubangiji Allah, Mai-iko duka; halayenka kuma masu-adalci ne, masu-gaskiya kuma, ya Sarkin zamanai.’ Mene ne ma’anar laƙabin nan “Mai-iko duka”? Yana nufin cewa Jehobah ya fi kowa a sama da duniya iko. Kuma laƙabin nan “Sarkin zamanai” yana nufin cewa ba shi da mafari da kuma ƙarshe. Zabura 90:2 ta bayyana cewa Jehobah yana wanzuwa koyaushe. Hakan abin mamaki ne, ko ba haka ba?

17 Jehobah kaɗai ne Mahalicci. Ru’ya ta Yohanna 4:11 ta ce: “Kai ne mai-isa ka karɓi ɗaukaka da daraja da iko, ya Ubangijinmu da Allahnmu: gama kai ka halicci dukan abu, saboda nufinka kuma suka kasance, saboda nufinka aka halicce su.” Hakika, Jehobah ne ya halicci mala’iku da taurari da ’ya’yan itatuwa da kifaye da kuma dukan abubuwa!

 ZAI YIWU KA ZAMA AMININ JEHOBAH?

18. Me ya sa wasu suke gani ba zai yiwu su zama aminan Allah ba? Mene ne Littafi Mai Tsarki ya ce game da hakan?

18 Sa’ad da wasu suka karanta game da halayen Jehobah, hakan na sa su yi mamaki kuma su ce, ‘Tun da Allah yana da iko da girma kuma yana can cikin sama, to yaya zai yiwu ya damu da ni?’ Shin, hakan Allah yake so mu ji game da shi? A’a. Jehobah yana son ya kusace mu. Littafi Mai Tsarki ya ce Allah bai “da nisa da kowane ɗayanmu.” (Ayyukan Manzanni 17:27) Allah yana son ka kusace shi kuma ya yi alkawari cewa ‘zai kusace ka.’—Yaƙub 4:8, LMT.

19. (a) Me zai taimaka maka ka zama aminin Allah? (b) Wane halin Jehobah ne ka fi so?

19 Me zai taimaka maka ka zama aminin Allah? Yesu ya ce: “Rai na har abada ke nan, su san ka, Allah makaɗaici mai-gaskiya, da shi kuma wanda ka aiko, Yesu Kristi.” (Yohanna 17:3) Ka ci gaba da yin nazari game da Jehobah da kuma Yesu kuma za ka san su sosai. Sa’an nan, za ka iya samun rai na har abada. Alal misali, mun riga mun koya cewa “Allah ƙauna ne.” (1 Yohanna 4:16) Ban da haka, yana da wasu halaye masu kyau. Littafi Mai Tsarki ya ce Jehobah yana “cike da juyayi, mai-alheri kuma, mai-jinkirin fushi, mai-yalwar jinƙai da gaskiya.” (Fitowa 34:6) Jehobah “nagari ne” kuma yana “hanzarin gafartawa.” (Zabura 86:5) Allah yana da haƙuri da kuma aminci. (2 Bitrus 3:9; Ibraniyawa 10:23) Za ka koyi abubuwa da yawa game da halayensa masu kyau yayin da kana ci gaba da karanta Littafi Mai Tsarki.

20-22. (a) Me zai taimaka maka ka kusaci Allah ko da yake ba ka ganin sa? (b) Me ya kamata ka yi idan wasu suna so su hana ka yin nazarin Littafi Mai Tsarki?

20 Me zai taimaka maka ka kusaci Allah da yake ba ka  ganin sa? (Yohanna 1:18; 4:24; 1 Timotawus 1:17) Idan ka karanta game da Jehobah a cikin Littafi Mai Tsarki, za ka san cewa yana wanzuwa da gaske. (Zabura 27:4; Romawa 1:20) Yayin da kake ci gaba da koyo game da Jehobah, za ka ƙaunace shi sosai kuma hakan zai sa ka kusace shi.

Uba yana ƙaunar yaransa, amma Ubanmu na sama ya fi ƙaunarmu

21 Za ka fahimci cewa Jehobah Ubanmu ne. (Matta 6:9) Shi ne ya halicce mu kuma yana so mu ji daɗin rayuwa. Abin da uba mai ƙauna zai so ya yi wa yaransa ke nan. (Zabura 36:9) Hakika, Littafi Mai Tsarki ya ce za ka iya zama aminin Jehobah. (Yaƙub 2:23) Babu shakka, wannan babban gata ne. Jehobah, wanda shi ne Mahaliccin sama da ƙasa yana so ka zama amininsa!

22 Wasu mutane suna son ka daina yin nazarin Littafi Mai Tsarki. Wataƙila suna tsoro don kada ka canja addininka. Amma kada ka ƙyale kowa ya hana ka zama aminin Jehobah. Babu wani amini da za ka samu da ya kai shi.

23, 24. (a) Me ya sa ya kamata ka ci gaba da yin tambayoyi? (b) Me za mu tattauna a babi na gaba?

23 Yayin da kake yin nazarin Littafi Mai Tsarki, za ka ga wasu abubuwa masu wuyan fahimta. Kada ka bar kunya ta hana ka yin tambayoyi. Yesu ya ce mu zama masu sauƙin kai kamar ƙananan yara. (Matta 18:2-4) Yara suna yin tambayoyi da yawa. Allah yana son ka sami amsoshin tambayoyin da kake yi. Saboda haka, ka yi nazarin Littafi Mai Tsarki da kyau domin ka tabbata cewa abin da ka koya gaskiya ne.—Karanta Ayyukan Manzanni 17:11.

24 Hanya mafi kyau na koya game da Jehobah ita ce ta yin nazarin Littafi Mai Tsarki. A babi na gaba, za mu tattauna abin da ya sa Littafi Mai Tsarki ya yi dabam da wasu littattafai.

^ sakin layi na 15 Idan babu sunan Jehobah a cikin naka Littafi Mai Tsarki ko kuma kana son ƙarin bayani game da ma’anar sunan da kuma yadda ake furta shi, ka duba Ƙarin bayani na 1.