Koma ka ga abin da ke ciki

Koma ga abubuwan da ke ciki

 BABI NA SHA ƊAYA

Me Ya Sa Muke Shan Wahala Sosai?

Me Ya Sa Muke Shan Wahala Sosai?

1, 2. Waɗanne irin tambayoyi ne mutane da yawa suke yi?

A KOWACE rana, muna jin labaran munanan abubuwan da suke faruwa a duniya. Alal misali, muna jin yadda guguwar tsunami ta halaka ƙauye gabaki ɗaya. Da yadda wani ɗan bindiga ya buɗe wuta a coci, a sakamakon hakan, mutane da yawa sun mutu, wasu kuma sun ji rauni. Ƙari ga haka, wata mata ta rasu ta bar yara biyar sanadiyyar ciwon kansa.

2 Sa’ad da irin waɗannan matsalolin suka faru, mutane da dama suna cewa, “Me ya sa hakan yake faruwa”? Wasu kuma sai su riƙa neman dalilin da ya sa mutane suke ƙiyayya da kuma shan wahala sosai. Kai kuma fa, ka taɓa yin irin wannan tambayar kuwa?

3, 4. (a) Waɗanne tambayoyi ne Habakkuk ya yi? (b) Yaya Jehobah ya amsa masa?

3 Akwai mutane da dama masu bangaskiya a cikin Littafi Mai Tsarki da suka taɓa yi wa Allah irin waɗannan tambayoyin. Alal misali, annabi Habakkuk ya tambayi Jehobah: “Don me kake nuna mini saɓo, ka sa ni in duba shiririta kuma? gama ɓarna da mugunta suna gabana; akwai husuma, jayayya kuma ta taso.”—Habakkuk 1:3.

4 Littafin Habakkuk 2:2, 3, yana ɗauke da amsar da Allah ya ba Habakkuk da kuma alkawarin da ya yi masa cewa zai magance matsalolin. Jehobah yana ƙaunar mutane sosai. Littafi Mai Tsarki ya ce: ‘Yana kula da kai.’ (1 Bitrus 5:7) Babu shakka, Allah ya tsani mugunta da  kuma wahala fiye da duk wani mutum. (Ishaya 55:8, 9) Saboda haka, bari mu tattauna tambayar nan, Me ya sa muke shan wahala sosai?

ME YA SA WAHALA TAKE KO’INA?

5. Mene ne malaman addinai da yawa suke cewa game da wahalar da muke sha? Mene ne Littafi Mai Tsarki ya ce?

5 Malaman addinai suna yawan cewa shan wahala nufin Allah ne. Wasu suna cewa duk wani abu da ya faru daga Allah ne ko da mummuna ne domin Allah ya riga ya ƙaddara su, kuma ba za mu iya fahimtar dalilinsa na yin hakan ba. Wasu kuma suna cewa yara da manya suna mutuwa domin su kasance tare da Allah a sama. Amma hakan ba gaskiya ba ne. Jehobah ba ya sa munanan abubuwa su faru. Littafi Mai Tsarki ya ce: “Sam, Allah ba mai aikata mugunta ba ne, a wurin Mai Iko Duka ba kuskure.”—Ayuba 34:10, Littafi Mai Tsarki.

6. Me ya sa mutane da yawa suke ɗora wa Allah laifin matsalolin da ke duniya?

6 Mutane da yawa suna ɗora wa Allah laifin matsalolin da muke fama da su. Me ya sa? Domin sun ɗauka cewa Allah ne yake mulkin wannan duniyar. Amma, mun koya a Babi na 3 cewa Shaiɗan ne yake mulkin duniya.

7, 8. Me ya sa wahala ta cika duniya?

7 Littafi Mai Tsarki ya ce “duniya duka kuwa tana hannun Mugun.” (1 Yohanna 5:19, LMT) Shaiɗan ne yake mulkin wannan duniyar kuma shi mugu ne da kuma marar tausayi. Yana “ruɗin dukan duniya.” (Ru’ya ta Yohanna 12:9) Mutane da yawa suna yin koyi da shi. Kuma shi ya sa duniya take cike da ƙaryace-ƙaryace da ƙiyayya da kuma zalunci.

8 Akwai wasu dalilai kuma da suka sa ake shan wahala sosai a duniya. Mun gāji zunubi daga Adamu da Hawwa’u  bayan sun yi tawaye da Allah. Kuma wannan zunubin yana sa ’yan Adam su sa wasu su sha wahala. Suna yawan so su kasance a gaba a kome. Suna yin faɗa da yaƙi da kuma cin zali. (Mai-Wa’azi 4:1; 8:9) A wasu lokuta kuma, mutane suna shan wahala saboda ‘sa’a da tsautsayi.’ (Mai-Wa’azi 9:11, LMT) Hatsari da kuma wasu munanan abubuwa suna faruwa sa’ad da muke wani wurin a lokacin da bai dace ba.

9. Me ya sa muka tabbata cewa Jehobah yana da dalili mai kyau na ƙyale wahala ta ci gaba har yanzu?

9 Jehobah ba ya jawo wa mutane wahala. Bai kamata mu ɗora masa laifi don yaƙi da mugunta da kuma zalunci da ake yi a duniya ba. Allah ba ya jawo bala’i da girgizar ƙasa da guguwa da kuma ambaliyar ruwa. Amma za mu iya cewa, ‘Idan Jehobah Mai iko duka ne, me ya sa bai cire waɗannan matsalolin ba?’ Mun san cewa Allah yana kula da mu sosai, saboda haka, yana da dalili mai kyau na ƙyale wahala ta ci gaba har yanzu.—1 Yohanna 4:8.

DALILIN DA YA SA ALLAH YA ƘYALE SHAN WAHALA

10. Mene ne Shaiɗan ya ce game da Allah?

10 Shaiɗan ya rinjayi Adamu da Hawwa’u a lambun Adnin. Shaiɗan ya ce Allah bai iya sarauta ba. Ya ce Allah ya hana Adamu da Hawwa’u moran abubuwa masu kyau. Ya so su yarda cewa ya fi Jehobah iya sarauta kuma ba lallai sai sun yi biyayya ga Allah ba.—Farawa 3:2-5; ka duba Ƙarin bayani na 27.

11. Wace tambaya ce za mu amsa?

11 Adamu da Hawwa’u sun yi wa Jehobah rashin biyayya kuma sun yi tawaye. Sun ɗauka cewa suna da ’yancin zaɓan nagarta da mugunta. Mene ne Jehobah zai yi don ya nuna cewa ’yan tawayen ba su da gaskiya kuma shi ne ya san abin da ya fi dacewa da mu?

12, 13. (a) Me ya sa Jehobah bai halaka ’yan tawayen nan da nan ba? (b) Me ya sa Jehobah ya ƙyale Shaiɗan ya zama mai mulkin wannan duniyar kuma ’yan Adam su mallaki kansu?

 12 Jehobah bai halaka Adamu da Hawwa’u nan da nan ba. Maimakon haka, ya bar su su haifi yara. Bayan haka, Jehobah ya sa ya yiwu ’ya’yan Adamu da Hawwa’u su zaɓi wanda suke so ya yi sarauta a kansu. Nufin Jehobah shi ne ya cika duniyar nan da mutanen da ba sa zunubi. Hakan zai faru kome ƙoƙarin Shaiɗan.—Farawa 1:28; Ishaya 55:10, 11.

13 Shaiɗan ya ƙalubalanci Jehobah a gaban miliyoyin mala’iku. (Ayuba 38:7; Daniyel 7:10) Saboda haka, Jehobah ya ba shi lokaci ya nuna ko zarginsa gaskiya ne. Ya kuma ba mutane lokaci su kafa nasu mulki da ikon Shaiɗan don su ga ko za su yi nasara ba tare da taimakon Allah ba.

14. Mene ne damar da Jehobah ya ba Shaiɗan da kuma ’yan Adam ya nuna?

14 Mutane sun yi shekaru da yawa suna sarautar kansu, amma ba su yi nasara ba. An riga an ƙaryata Shaiɗan. Mutane suna bukatar ja-gorar Allah. Annabi Irmiya ya faɗi gaskiya sa’ad da ya ce: “Ya Ubangiji, na tabbata hanyar mutum ba cikin nasa hannu take ba; mutum kuwa ba shi da iko shi shirya tafiyarsa.”—Irmiya 10:23.

ME YA SA JEHOBAH BAI ƊAUKI MATAKI BA HAR YANZU?

15, 16. (a) Me ya sa Jehobah ya ƙyale wahala ta ci gaba har yanzu? (b) Me ya sa Jehobah bai magance matsalolin da Shaiɗan ya jawo ba?

15 Me ya sa Jehobah bai ɗauki mataki a kan Shaiɗan ba har yanzu? Me ya sa bai hana munanan abubuwa faruwa ba? Ana bukatar lokaci don a tabbatar  cewa sarautar Shaiɗan ta kāsa. ’Yan Adam sun gwada sarauta iri-iri amma ba su yi nasara ba. Ko da yake sun sami ci gaba sosai a fannonin kimiyya da fasaha, rashin adalci da talauci da kuma yaƙe-yaƙe sun zama ruwan dare gama gari. ’Yan Adam ba za su iya yin sarauta ba sai da taimakon Allah.

16 Amma, Jehobah bai magance matsalolin da Shaiɗan ya jawo ba. Idan ya yi hakan, zai nuna cewa yana goyon bayan sarautar Shaiɗan, kuma wannan abu ne da ba zai taɓa yi ba. Ƙari ga haka, idan ya magance matsalolin, ’yan Adam za su ɗauka cewa suna da ikon yin sarauta ba tare da taimakon Allah ba. Amma hakan ƙarya ne, kuma Jehobah ba zai yi hakan ba. Ba ya yin ƙarya.—Ibraniyawa 6:18.

17, 18. Wane mataki ne Jehobah zai ɗauka don ya kawar da dukan matsalolin da Shaiɗan ya jawo?

17 Shin Jehobah zai iya magance dukan matsalolin da Shaiɗan da kuma mutane suka jawo sanadiyyar tawayensu? Ƙwarai kuwa. Allah yana da ikon yin duk abin da yake so. Jehobah ya san lokacin da zai ɗauki mataki a kan Shaiɗan. A lokacin, zai mayar da duniya ta zama aljanna kamar yadda ya so tun asali. Dukan mutanen da ke cikin “kabarbaru” za su tashi. (Yohanna 5:28, 29) Mutane ba za su sake yin ciwo ko mutuwa ba. Yesu zai cire dukan matsalolin da Shaiɗan ya jawo. Jehobah zai yi amfani da Yesu wajen “halaka ayyukan Shaiɗan.” (1 Yohanna 3:8) Muna matuƙar farin ciki domin a yanzu, Jehobah yana haƙuri da mu. Yana so mu san shi kuma mu yanke shawarar bauta masa. (Karanta 2 Bitrus 3:9, 10.) Sa’ad da muke shan wahala, yana taimaka mana mu jimre.—Yohanna 4:23; karanta 1 Korintiyawa 10:13.

 18 Jehobah ba ya tilasta mana mu bauta masa. Ya ba mutane ’yancin yin zaɓi. Bari mu tattauna yadda wannan kyautar take amfanarmu.

YAYA ZA KA YI AMFANI DA ’YANCINKA NA YIN ZAƁI?

19. Wace kyauta ce Jehobah ya ba mu? Me ya sa ya dace mu daraja wannan kyautar?

19 Wannan kyautar da Jehobah ya ba mu, wato ’yancin yin zaɓi ya bambanta mu da dabbobi. Dabbobi ba su da ’yancin zaɓan abu mai kyau da marar kyau, amma mu za mu iya sarrafa rayuwarmu yadda muke so. Za mu kuma iya yanke shawarar bauta wa Jehobah ko a’a. (Misalai 30:24) Bugu da ƙari, ba ma kamar inji da ke yin abubuwan da aka tsara shi ya yi kawai. Muna da ’yancin zaɓan abokanmu da yadda muke so rayuwarmu ta kasance da kuma abubuwan da muke so mu yi. Jehobah yana so mu ji daɗin rayuwa.

20, 21. Wane zaɓi ne ya kamata ka yi yanzu?

20 Jehobah yana so mu ƙaunace shi. (Matta 22:37, 38) Yana kamar uba da ke farin ciki sa’ad da ɗansa ya ce masa “Baba, ina ƙaunarka sosai.” Yaron ne ya so faɗin hakan, ba don an tilasta masa ba. Jehobah ya ba mu ’yancin zaɓan wanda muke so mu bauta wa. Shaiɗan da Adamu da kuma Hawwa’u sun zaɓi su yi tawaye da Jehobah. Ta yaya za ka yi amfani da ’yancinka na yin zaɓi?

21 Ka yi amfani da ’yancinka wajen bauta wa Jehobah. Akwai miliyoyin mutane da suka yanke shawarar faranta wa Allah rai kuma sun ƙi bin Shaiɗan. (Misalai 27:11) Me ya kamata ka yi yanzu don ka kasance cikin sabuwar duniya sa’ad da Allah ya cire wahala gabaki ɗaya? Za mu amsa wannan tambayar a babi na gaba.