Koma ka ga abin da ke ciki

Koma ga abubuwan da ke ciki

 BABI NA GOMA

Gaskiya Game da Mala’iku da Kuma Aljanu

Gaskiya Game da Mala’iku da Kuma Aljanu

1. Me ya sa zai dace mu koya game da mala’iku?

JEHOBAH yana so mu san iyalinsa. Mala’iku suna cikin iyalin Allah. Littafi Mai Tsarki ya kira su “’ya’yan Allah.” (Ayuba 38:7) Mene ne mala’iku suke yi? Ta yaya suka taimaki mutane a dā? Kuma ta yaya za su iya taimaka mana a yau?—Ka duba Ƙarin bayani na 8.

2. Yaya mala’iku suka soma wanzuwa? Mala’iku nawa ne aka halitta?

2 Ya kamata mu san yadda mala’iku suka soma wanzuwa. Littafin Kolosiyawa 1:16 ya ce Jehobah ya halicci Yesu, bayan haka, sai aka “halicci dukan abu, cikin sammai da bisa duniya” har da mala’iku. Mala’iku nawa ne ya halitta? Littafi Mai Tsarki ya ce akwai miliyoyin mala’iku.—Zabura 103:20; Ru’ya ta Yohanna 5:11.

3. Mene ne Ayuba 38:4-7 suka ce game da mala’iku?

3 Littafi Mai Tsarki ya kuma ce Jehobah ya halicci mala’iku kafin ya yi duniya. Yaya suka ji sa’ad da suka ga duniya? Littafin Ayuba ya nuna cewa sun yi matuƙar farin ciki. A lokacin, dukan mala’iku suna bauta wa Allah tare.—Ayuba 38:4-7.

MALA’IKU SUN TAIMAKI BAYIN ALLAH

4. Ta yaya muka san cewa mala’iku suna son mutane?

4 Mala’iku sun daɗe suna son mutane kuma suna son su ga cewa nufin Allah ga duniya da kuma mutane ya cika. (Misalai 8:30, 31; 1 Bitrus 1:11, 12) Babu shakka, sun yi baƙin ciki sosai sa’ad da Adamu da Hawwa’u suka yi  tawaye ga Allah. Sun ma fi baƙin ciki yanzu da yawancin mutane suke tawaye ga Jehobah. Amma sa’ad da wani ya tuba kuma ya komo ga Allah, mala’iku suna farin ciki. (Luka 15:10) Mala’iku suna ƙaunar mutanen da suke bauta wa Allah. Jehobah yana amfani da mala’iku wajen taimaka wa bayinsa a duniya da kuma kāre su. (Ibraniyawa 1:7, 14) Bari mu tattauna wasu misalai.

“Allahna ya aiko mala’ikansa, ya rufe bakin zakuna.”—Daniyel 6:22

5. Ta yaya mala’iku suka taimaka wa bayin Allah a zamanin dā?

 5 Jehobah ya tura mala’iku biyu su taimaki Lutu da iyalinsa don kada su halaka a cikin birnin Saduma da Gwamarata. (Farawa 19:15, 16) Ɗarurruwan shekaru bayan haka, an jefa annabi Daniyel cikin ramin zakuna, amma ba su yi masa kome ba domin ‘Allah ya aiko mala’ikansa, ya rufe bakin zakunan.’ (Daniyel 6:22) Daga baya, Jehobah ya aiko da mala’ikansa ya ciro manzo Bitrus daga gidan yari. (Ayyukan Manzanni 12:6-11) Mala’iku sun kuma taimaka wa Yesu sa’ad da yake duniya. Alal misali, bayan da Yesu ya yi baftisma, ‘mala’iku sun yi masa hidima.’ (Markus 1:13, Littafi Mai Tsarki) Wani mala’ika ya “ƙarfafa” Yesu jim kaɗan kafin a kashe shi.—Luka 22:43.

6. (a) Ta yaya muka san cewa mala’iku suna taimaka wa bayin Allah a yau? (b) Waɗanne tambayoyi ne za mu amsa yanzu?

6 Mala’iku sun daina bayyana ga mutane a yau. Amma har ila, Allah yana amfani da mala’iku don ya taimaka wa bayinsa. Littafi Mai Tsarki ya ce: “Mala’ikansa yana tsaron waɗanda ke tsoron Ubangiji, ya cece su daga hatsari.” (Zabura 34:7, LMT) Me ya sa muke bukatar kāriya? Domin muna da maƙiya da yawa da suke so su yi mana lahani. Su waye ne waɗannan maƙiyan? Daga ina suke? Ta yaya suke ƙoƙarin yi mana lahani? Don sanin amsoshin waɗannan tambayoyin, zai dace mu tattauna abin da ya faru jim kaɗan bayan da Allah ya halicci Adamu da Hawwa’u.

MAƘIYAN DA BA A GANI DA IDO

7. Shin Shaiɗan ya yi nasara wajen yaudarar mutane kuwa? Ka bayyana.

7 Mun koya a Babi na 3 cewa wani mala’ika ya yi tawaye ga Allah kuma yana son sarauta. Littafi Mai Tsarki ya  kira shi Shaiɗan da Iblis. (Ru’ya ta Yohanna 12:9) Shaiɗan ya kuma so wasu su yi tawaye ga Allah. Ya yaudari Hawwa’u, kuma tun daga lokacin, ya yaudari yawancin mutane. Amma wasu mutane kamar su Habila da Anuhu da Nuhu sun kasance da aminci ga Jehobah.—Ibraniyawa 11:4, 5, 7.

8. (a) Ta yaya wasu mala’iku suka zama aljanu? (b) Mene ne aljanun suka yi don kada ambaliyar ruwa ta halaka su?

8 A zamanin Nuhu, wasu mala’iku sun yi tawaye kuma sun sauko duniya. Me ya sa? Littafi Mai Tsarki ya ce sun so su auri mata. (Karanta Farawa 6:2.) Amma hakan bai dace da mala’iku ba. (Yahuda 6) Yawancin mutane a lokacin suna yin munanan abubuwa kamar waɗannan miyagun mala’ikun. Sai Jehobah ya yanke shawara cewa zai halaka miyagun mutane da ambaliyar ruwa mai ƙarfi sosai. Amma ya ceci bayinsa masu aminci. (Farawa 7:17, 23) Miyagun mala’ikun sun koma sama don kada ambaliyar ruwan ta halaka su. Littafi Mai Tsarki ya kira su aljanu. Sun goyi bayan Shaiɗan kuma ya zama shugabansu.—Matta 9:34.

9. (a) Me ya faru da aljanu sa’ad da suka koma sama? (b) Me za mu tattauna yanzu?

9 Jehobah bai yarda aljanun su sake kasance cikin iyalinsa ba domin sun yi tawaye. (2 Bitrus 2:4) Aljanu ba su da iko su canja siffarsu kamar dā, amma har ila, suna “ruɗin dukan duniya.” (Ru’ya ta Yohanna 12:9; 1 Yohanna 5:19) Bari mu tattauna yadda suke yin nasara wajen yaudarar mutane da yawa.—Karanta 2 Korintiyawa 2:11.

YADDA ALJANU SUKE YAUDARAR MUTANE

10. Ta yaya aljanu suke rinjayar mutane?

10 Aljanu suna yaudarar mutane a hanyoyi da yawa. Idan mutane suna sha’ani da aljanu, suna yin hakan kai  tsaye ko kuma da taimakon boka ko masu tsafi. Ana kiran yin sha’ani da aljanu sihiri. Amma Littafi Mai Tsarki ya ja mana kunne cewa mu nisanta kanmu daga aljanu da kuma ayyukansu. (Galatiyawa 5:19-21) Me ya sa? Domin aljanu suna yin amfani da dabaru dabam-dabam don su rinjayi mutane kamar yadda mafarauci yake yin amfani da tarko don ya kama dabba.—Ka duba Ƙarin bayani na 26.

11. Mene ne dūba, kuma me ya sa ya kamata mu guje shi?

11 Ɗaya cikin dabarunsu shi ne dūba. Dūba shi ne yin amfani da ikon aljanu wajen neman sanin abin da zai faru a nan gaba ko sanin wani sirri. Wani yana iya yin hakan ta wajen kallon taurari da ishara da katin sihiri da yin amfani da wani irin kwallo ko kuma duba tafin hannun mutum. Wasu sun ɗauka cewa waɗannan abubuwan ba za su kawo mummunar sakamako ba. Amma hakan ba gaskiya ba ne. Alal misali, Littafi Mai Tsarki ya nuna cewa aljanu da masu dūba suna aiki tare. Littafin Ayyukan Manzanni 16:16-18 ya ce “ruhu na dūba” ya taimaka wa wata yarinya wajen yin ‘dūba.’ Bayan da manzo Bulus ya fitar da aljanin, sai ikon yin dūba ya bar yarinyar.

12. (a) Me ya sa yin sha’ani da aljanu yake da haɗari? (b) Me ya sa bayin Allah ba sa sha’ani da aljanu?

12 Aljanu suna kuma yin amfani da wata dabara wajen rinjayar mutane. Suna neman su sa mu gaskata cewa za mu iya tattaunawa da matattu kuma mutane ba sa mutuwa da gaske. Sun ce suna rayuwa a wani wuri, za su iya yi mana magana da kuma lahani. Alal misali, wani da aka yi masa rasuwa zai iya zuwa wajen boka domin ya taimaka masa ya yi magana da mataccen. Bokan zai iya gaya wa mutumin wani labari mai daɗi game da mataccen ko  kuma ya kwaikwayi muryar mataccen. (1 Sama’ila 28:3-19) A yau, mutane suna yin abubuwa iri-iri a lokacin jana’iza domin suna ganin cewa matattu suna rayuwa a wani wuri. Hakan ya haɗa da yin biki a lokacin jana’iza da bikin cika shekara da mutuwa da yin hadayu don matattu da zaman takaba da farkawa da kuma wasu bukukuwa da ake yi don a tuna da matattu. Idan Kiristoci suka ƙi saka hannu a waɗannan al’adun, danginsu ko kuma mutanen ƙauyensu za su iya zaginsu ko kuma su ƙi yin cuɗanya da su. Amma Kiristoci sun san cewa matattu ba sa rayuwa a wani wuri. Ba zai yiwu a tattauna da matattu ba kuma ba za su iya yi mana lahani ba. (Zabura 115:17) Ka yi hattara. Kada ka kuskura ka yi sha’ani da matattu ko aljanu kuma kada ka saka hannu a al’adunsu.—Karanta Kubawar Shari’a 18:10, 11; Ishaya 8:19.

13. Mene ne mutane da yawa da suke tsoron aljanu a dā suka yi?

13 Aljanu suna yaudarar mutane da kuma tsoratar da su. A yau, Shaiɗan da aljanunsa sun san cewa ‘lokacinsu ya ƙure.’ Nan ba da daɗewa ba, Allah zai cire su daga duniya, saboda haka, suna cike da fushi. (Ru’ya ta Yohanna 12:12, 17, LMT) Amma, dubban mutane da suke tsoron aljanu a dā sun daina tsoronsu. Me ya taimaka musu su daina tsoron aljanu?

YADDA ZA KA SAMU ’YANCI DAGA ALJANU KUMA KA YI TSAYAYYA DA SU

14. Ta yaya za mu iya ’yantar da kanmu daga aljanu, kamar yadda Kiristoci suka yi a zamanin dā?

14 Littafi Mai Tsarki ya gaya mana yadda za mu samu ’yanci daga aljanu kuma mu yi tsayayya da su. Alal misali, wasu mutane a birnin Afisa suna sha’ani da aljanu kafin su koyi gaskiya. Me suka yi don su sami ’yanci?  Littafi Mai Tsarki ya ce: “Waɗansu kuwa ba kaɗan ba daga masu-yin sihiri suka tattara littattafansu, suka ƙone su a gaban dukan mutane.” (Ayyukan Manzanni 19:19) Sun ƙona littattafansu na sihiri domin suna so su zama Kiristoci. Matakin da ya kamata a ɗauka ke nan a yau. Mutanen da suke so su bauta wa Jehobah suna bukatar su nisanta kansu daga kayayyakin aljanu. Wannan ya haɗa da littattafai da mujallu da fina-finai da waƙoƙi da wasanni da kuma hotuna da ke sa a ga kamar sihiri abu ne mai kyau. Ya kuma haɗa da abubuwan da mutane suke sakawa don su kāre kansu daga miyagun abubuwa.—1 Korintiyawa 10:21.

15. Me kuma muke bukata mu yi don mu yi tsayayya da Shaiɗan da kuma aljanunsa?

15 Bayan wasu shekaru da mutanen Afisa suka ƙona littattafansu na sihiri, manzo Bulus ya aika musu wasiƙa cewa har ila, suna bukatar su yi ‘fama’ da kuma kokuwa da “mugayen ruhohi.” (Afisawa 6:12, LMT) Ko da yake sun riga sun ƙona littattafansu, amma aljanu sun ci gaba da neman zarafin yi musu lahani. Saboda haka, wane mataki kuma suke bukatar su ɗauka? Bulus ya gaya musu: “Ku ɗauki garkuwa ta bangaskiya, da shi za ku iya ɓice [ko kāre] dukan jefe-jefe masu-wuta na Mugun.” (Afisawa 6:16) Kamar yadda garkuwa take kāre soja a lokacin yaƙi, hakan ma bangaskiyarmu za ta iya kāre mu. Idan muna da tabbaci sosai cewa Jehobah zai iya kāre mu, za mu iya yin tsayayya da Shaiɗan da kuma aljanunsa.—Matta 17:20.

16. Ta yaya za mu iya ƙarfafa bangaskiyarmu ga Jehobah?

16 Ta yaya za mu ƙarfafa bangaskiyarmu ga Jehobah? Muna bukatar karanta Littafi Mai Tsarki kullum da kuma dogara ga Jehobah don ya kāre mu. Idan mun dogara sosai  ga Jehobah, Shaiɗan da aljanunsa ba za su iya yi mana lahani ba.—1 Yohanna 5:5.

17. Wane abu ne kuma zai iya kāre mu daga aljanu?

17 Waɗanne matakai ne kuma Kiristocin da ke Afisa suke bukatar ɗaukawa? Suna zama ne a birnin da ke cike da ayyukan aljanu. Saboda haka, Bulus ya ce musu: “Kuna addu’a kowane” lokaci. (Afisawa 6:18) Suna bukatar su roƙi Jehobah ya kāre su a kowane lokaci. Shin hakan ya shafe mu ma a yau? Ƙwarai kuwa. Muna rayuwa a duniyar da ke cike da ayyukan aljanu. Saboda haka, muna bukatar mu roƙi Jehobah ya kāre mu kuma mu yi amfani da sunansa sa’ad da muke addu’a. (Karanta Misalai 18:10.) Idan mun ci gaba da roƙon Jehobah ya ’yantar da mu daga hannun Shaiɗan, Jehobah zai amsa addu’o’inmu.—Zabura 145:19; Matta 6:13.

18, 19. (a) Me zai taimaka mana mu yi nasara wajen yin tsayayya da Shaiɗan da kuma aljanunsa? (b) Wace tambaya ce za mu amsa a babi na gaba?

18 Idan mun kawar da dukan kayayyakin aljanu kuma muka dogara ga Jehobah don ya kāre mu, za mu iya yin tsayyaya da Shaiɗan da kuma aljanunsa. Ba ma bukatar mu ji tsoronsu. (Karanta Yaƙub 4:7, 8.) Jehobah ya fi aljanu ƙarfi sosai. Ya hukunta su a zamanin Nuhu kuma a nan gaba, zai halaka su. (Yahuda 6) Ka tuna cewa ba mu kaɗai ba ne muke wannan famar ba. Jehobah yana yin amfani da mala’ikunsa wajen kāre mu. (2 Sarakuna 6:15-17) Za mu iya kasancewa da tabbaci cewa da taimakon Jehobah, za mu yi nasara wajen yin tsayayya da Shaiɗan.—1 Bitrus 5:6, 7; 2 Bitrus 2:9.

19 Amma me ya sa har ila, Allah bai halaka Shaiɗan da kuma aljanunsa da yake suna jawo matsaloli da yawa a duniya ba? Za mu amsa wannan tambayar a babi na gaba.