Koma ka ga abin da ke ciki

Koma ga abubuwan da ke ciki

 BABI NA SHA SHIDA

Ka Yanke Shawarar Bauta wa Allah

Ka Yanke Shawarar Bauta wa Allah

1, 2. Wace tambaya ce ta wajaba mu yi wa kanmu, kuma me ya sa yin hakan yake da muhimmanci?

BABU SHAKKA, yayin da kake nazarin Littafi Mai Tsarki, ka koya cewa mutane da yawa da suke ce suna bauta wa Allah suna koyar ko kuma yin abubuwan da Allah ba ya so. (2 Korintiyawa 6:17) Shi ya sa Jehobah ya ce mu fita daga addinin ƙarya, wato “Babila Babba.” (Ru’ya ta Yohanna 18:2, 4) Kai kuma fa, wane zaɓi ne za ka yi? Kowannenmu yana da ’yancin yin zaɓi kuma wajibi ne mu yi wa kanmu wannan tambayar, ‘Shin ina so in bauta wa Allah a hanyar da yake so ko kuwa ina so in bauta masa a hanyar da na saba?’

2 Idan ka riga ka daina tarayya da addinin ƙarya, to, muna taya ka murna. Amma wataƙila har ila, kana yin wasu bukukuwa ko al’adun addinan ƙarya. Bari mu tattauna wasu cikin waɗannan bukukuwa da al’adu kuma mu ga dalilan da suka sa ya kamata mu kasance da ra’ayin Jehobah game da waɗannan abubuwan.

BAUTAR GUMAKA DA KAKANNI

3. (a) Me ya sa yake ma wasu wuya su daina yin amfani da gumaka a bauta? (b) Mene ne Littafi Mai Tsarki ya ce game da yin amfani da gumaka a bauta?

3 Wasu mutane sun yi shekaru da yawa suna yin amfani da gumaka ko bagaden tsafi don bauta wa Allah. Idan kai ma kana yin hakan, wataƙila za ka ji cewa bai dace a bauta wa Allah ba tare da yin amfani da waɗannan abubuwan  ba. Amma ka tuna cewa Jehobah ne yake koya mana yadda za mu bauta masa. Kuma Littafi Mai Tsarki ya gaya mana dalla-dalla cewa Jehobah ba ya so mu yi amfani da gumaka don bauta masa.—Karanta Fitowa 20:4, 5; Zabura 115:4-8; Ishaya 42:8; 1 Yohanna 5:21.

4. (a) Me ya sa bai dace mu bauta wa kakanninmu ba? (b) Me ya sa Jehobah ya ce kada mu tattauna da matattu?

4 Wasu mutane suna ɓata lokacinsu garin neman su faranta ran kakaninsu da suka mutu. Suna ma iya bauta musu. Amma mun koya cewa mutanen da suka mutu ba za su iya taimaka mana ko kuma yi mana lahani ba. Ba sa rayuwa a wani wuri. Son yin magana da matattu bai dace ba domin aljanu ne ainihi suke yin maganar ba matattun ba. Shi ya sa Jehobah ya umurci Isra’ilawa cewa kada su tattauna da matattu ko kuma su yi sha’ani da aljanu.—Kubawar Shari’a 18:10-12; ka duba Ƙarin bayani na 26 da 31.

5. Mene ne zai taimaka maka ka daina bauta wa kakanninka da kuma daina yin amfani da gumaka don bauta wa Allah?

5 Mene ne zai iya taimaka maka ka daina yin amfani da gumaka don bautar Allah ko kuma ka daina bauta wa kakanninka? Kana bukatar ka karanta Littafi Mai Tsarki, kuma ka yi tunani sosai a kan yadda Jehobah yake ɗaukan waɗannan abubuwan. Yin amfani da gumaka don bauta wa Allah da kuma bauta wa kakanninmu “abin ƙyama” ne a gare shi. (Kubawar Shari’a 27:15) Ka riƙa yin addu’a ga Jehobah kullum don ya taimaka maka ka kasance da ra’ayinsa kuma ka bauta masa a hanyar da yake so. (Ishaya 55:9) Idan ka yi hakan, Jehobah zai taimaka maka ka daina yin tarayya da addinin ƙarya da kuma al’adunsa.

YA DACE MU YI BIKIN KIRSIMATI KUWA?

6. Me ya sa ake bikin haihuwar Yesu a ranar 25 ga Disamba?

6 Kirsimati sanannen biki ne a ko’ina kuma mutane  da yawa suna tsammani cewa bikin tuna da haihuwar Yesu ne. Amma Kirsimati yana da alaƙa da addinin ƙarya. Wani littafin tarihi ya ce Romawa masu bautar gumaka ne suke bikin haihuwar rana a ranar 25 ga Disamba. Limaman Coci sun so masu bautar gumaka su zama Kiristoci. Saboda haka, ko da yake ba a haifi Yesu a ranar 25 ga Disamba ba, sun yanke shawarar yin bikin haihuwar Yesu a wannan kwanan watan. (Luka 2:8-12) Almajiran Yesu ba su yi bikin Kirsimati ba. Wani littafi ya ce har shekara 200 bayan haihuwar Yesu, “babu wanda ya san ainihin lokacin da aka haife shi, mutane ƙalilan ne suka damu da ainihin lokacin da aka haife shi.” (Sacred Origins of Profound Things) An soma bikin Kirsimati shekaru da yawa bayan mutuwar Yesu.

7. Me ya sa Kiristoci na gaskiya ba sa Kirsimati?

7 Mutane da yawa sun san cewa arna ne suka soma bikin Kirsimati da al’adunta na yin liyafa da kuma ba da kyauta. Alal misali, akwai lokacin da aka hana yin bikin Kirsimati a Ingila da kuma wasu wurare a Amirka domin an gano cewa bikin arna ne. Ana hukunta kowane mutum da ya yi hakan a lokacin. Amma daga baya, sai mutane suka sake soma bikin Kirsimati. Me ya sa Kiristoci na gaskiya ba sa Kirsimati? Domin suna so su faranta wa Allah rai a dukan fannonin rayuwarsu.

YA DACE MU YI BIKIN HAIHUWA KUWA?

8, 9. Me ya sa Kiristoci a ƙarni na farko ba sa yin bikin ranar haihuwa?

8 Wani sanannen biki kuma shi ne bikin ranar haihuwa. Shin ya kamata Kiristoci su yi bikin ranar haihuwa? Mutane biyu da ba masu bautar Jehobah ba ne suka yi bikin ranar haihuwa da aka ambata a cikin Littafi Mai Tsarki.  (Farawa 40:20; Markus 6:21) A lokacin, ana yin bikin ranar haihuwa don girmama allolin ƙarya. Shi ya sa Kiristoci a ƙarni na farko ba sa yin bikin ranar haihuwa domin “al’adar masu bautar gumaka ne.”—The World Book Encyclopedia.

9 Romawa da Helenawa na zamanin dā sun yi imani cewa ruhu yana zuwa wurin haihuwar kowane mutum kuma ya kāre mutumin a dukan kwanakin ransa. Mutanen da ba Kiristoci ba ne a lokacin suna bikin ranar haihuwa domin suna tsammani cewa hakan zai sa allahnsu ya kāre yaron.

10. Me ya sa bai kamata Kiristoci a yau su yi bikin ranar haihuwa ba?

10 Kana ganin Jehobah zai amince da kowane bikin da yake da alaƙa da addinin ƙarya? (Ishaya 65:11, 12) A’a. Shi ya sa ba ma bikin ranar haihuwa ko kuma bukukuwa da ke da alaƙa da addinin ƙarya.

YA KAMATA MU DAMU DON TUSHEN BUKUKUWAN NE?

11. Me ya sa wasu suke yin Kirsimati da kuma bukukuwan da ba su dace ba? Me ya kamata mu fi ɗaukawa da muhimmanci?

11 Wasu mutane sun san cewa ba masu bautar Allah ba ne suke yin Kirsimati da kuma wasu bukukuwan da ba su dace ba, duk da haka, sun ƙi su daina. Suna tsammanin cewa wannan lokaci ne na kasancewa tare da iyalinsu. Shin ra’ayinka ke nan? Kasancewa da iyalinka ba laifi ba ne. Jehobah ne ya tsara iyali kuma yana so mu ji daɗin iyalinmu. (Afisawa 3:14, 15) Amma, maimakon faranta wa danginmu rai ta wajen yin bukukuwa na addinin ƙarya, ya kamata mu fi ɗaukar ƙulla dangantaka mai kyau da Jehobah da muhimmanci. Shi ya sa manzo Bulus ya ce: Ku riƙa “gwada abin da ke na yarda ga Ubangiji.”—Afisawa 5:10.

12. Me ya sa Jehobah ba ya son wasu bukukuwa?

 12 Wasu suna tsammanin cewa wurin da aka samo bukukuwa ba matsala ba ce, amma ba haka Jehobah yake ji ba. Ba ya amincewa da bukukuwan da aka ɗauko daga addinin ƙarya ko kuma da ke ɗaukaka mutane da ƙasashe. Alal misali, Masarawa suna wa allolinsu bukukuwa da yawa. Bayan Isra’ilawa sun fito daga ƙasar Masar, sai suka soma yin waɗannan bukukuwan kuma suka kira hakan “idi ga Ubangiji.” Amma Jehobah ya hukunta su. (Fitowa 32:2-10) Annabi Ishaya ya ce ‘kada mu taɓa wani abu mai-ƙazamta.’—Karanta Ishaya 52:11.

KA BI DA MUTANE DA KIRKI

13. Waɗanne tambayoyi ne za ka iya yi sa’ad da ka tsai da shawarar daina yin wasu bukukuwa?

13 Za ka iya yi wa kanka tambayoyi da yawa sa’ad da ka tsai da shawarar daina yin bukukuwan da ba su dace ba. Alal misali: Abokan aikina za su iya tambayar dalilin da ya sa ba na bikin Kirsimati? Me ya kamata in yi idan wani ya ba ni kyauta a lokacin Kirsimati? Me zan yi idan mijina ko matata tana so mu yi bukukuwan tare? Ta yaya zan taimaka wa yarana don kada su yi baƙin ciki cewa ba sa yin bikin ranar haihuwarsu da kuma wasu bukukuwan da ba su dace ba?

14, 15. Me za ka iya yi idan wani ya ce maka barka da Kirsimati ko barka da sabuwar shekara ko kuma ya ba ka kyauta?

14 Ya kamata mu yi amfani da basira wajen sanin abin da ya kamata mu faɗa da kuma yi a kowane yanayi. Alal misali, idan wani ya ce maka barka da Kirsimati ko barka da sabuwar shekara, bai kamata ka yi banza da shi ba. Za ka iya ce masa, “Na gode.” Amma idan mutumin yana son ƙarin bayani, za ka iya bayyana masa dalilin da ya sa ba ka irin waɗannan bukukuwan. Ka kasance da fara’a  da kirki da kuma ladabi sa’ad da kake yin hakan. Littafi Mai Tsarki ya ce: “Bari zancenku kullum ya kasance tare da alheri, gyartacce da gishiri, domin ku sani yadda za ku amsa tambayar kowa.” (Kolosiyawa 4:6) Kana iya gaya masa cewa kai ma kana yin tarayya da mutane kuma kana ba da kyauta, amma ba ka so ka yi hakan a wannan lokacin.

15 Me ya kamata ka yi idan wani ya ba ka kyauta? Littafi Mai Tsarki bai ba da jerin dokoki da yawa ba, amma ya dai ce kada mu yi abubuwan da za su sa zuciyarmu ta riƙa damunmu. (1 Timotawus 1:18, 19) Wataƙila mutumin da ya ba ka kyautar bai san cewa ba ka yin irin waɗannan bukukuwan ba. Ko kuma zai iya ce, “Na san cewa ba ka yin waɗannan bukukuwan, duk da haka, ina so in ba ka kyauta.” A irin wannan yanayin, za ka iya yanke shawarar karɓan kyautar ko a’a. Amma ko da wace shawara ce ka yanke, kada ka yi abin da zai sa zuciyarka ta riƙa damunka. Ba zai dace mu yi abin da zai ɓata dangantakarmu da Allah ba.

KAI DA KUMA IYALINKA

Mutanen da suke bauta wa Jehobah suna farin ciki

16. Me ya kamata ka yi idan iyalinka suna so su yi wasu bukukuwa?

16 Me ya kamata ka yi idan iyalinka suna so su yi waɗannan bukukuwan? Bai kamata ka yi jayayya da su ba. Ka tuna cewa suna da ’yancin zaɓan abin da suke so. Ka yi musu fara’a kuma ka girmama su yadda kai ma za ka so a girmama ka. (Karanta Matta 7:12.) Amma, mene ne za ka iya yi idan iyalinka suna so ka kasance tare da su a lokacin da suke yin bukukuwan da ba su dace ba? Ka yi addu’a ga Jehobah don ya taimaka maka ka yanke shawara mai kyau. Ka yi tunani a kan batun kuma ka yi bincike. Ka tuna cewa kana so ka faranta wa Jehobah rai a kowane lokaci.

17. Mene ne za ka iya yi don kada yaranka su yi baƙin ciki idan sun ga wasu yara suna yin bukukuwan da ba su dace ba?

 17 Mene ne za ka iya yi don ka taimaka wa yaranka idan sun ga wasu yara suna yin bukukuwan da ba su dace ba? Za ka iya shirya musu liyafa a kai a kai. Za ka kuma iya ba su kyauta. Kyauta mafi kyau da za ka iya ba yaranka ita ce kasancewa tare da su da kuma nuna musu ƙauna.

KA RIƘA BAUTA TA GASKIYA

18. Me ya sa ya kamata mu riƙa halartan taron Kirista?

18 Idan kana so ka faranta wa Jehobah rai, wajibi ne ka guji bauta ta ƙarya da al’adunta da kuma wasu bukukuwa da suke da alaƙa da bauta ta ƙarya. Muna kuma bukata mu riƙa bauta ta gaskiya. Ta yaya za mu yi hakan? Hanya ɗaya ita ce ta halartan taron Kirista a kai a kai. (Karanta Ibraniyawa 10:24, 25.) Waɗannan taron suna da amfani sosai. (Zabura 22:22; 122:1) Za mu iya ƙarfafa juna sa’ad da muka haɗu a wannan taron.—Romawa 1:12.

19. Me ya sa ya dace ka gaya wa wasu gaskiyar da ka koya a Littafi Mai Tsarki?

19 Wani abu kuma da za ka yi don ka nuna cewa ka zaɓi bauta ta gaskiya ita ce ta wajen gaya wa wasu abubuwan da ka koya a Littafi Mai Tsarki. Mutane da yawa suna baƙin ciki don abubuwan da ke faruwa a duniya. Wataƙila ka san mutanen da suke jin hakan. Zai dace ka gaya musu abubuwan da za su faru a nan gaba. Yayin da kake halartan taron Kirista kuma kake koya wa mutane gaskiyar Littafi Mai Tsarki, za ka soma ƙyamar addinin ƙarya da kuma al’adunsa. Babu shakka, za ka yi farin ciki kuma Jehobah zai saka maka sosai don yadda kake ƙoƙartawa ka bauta masa a hanyar da ta dace.—Malakai 3:10.