Koma ka ga abin da ke ciki

Koma ga abubuwan da ke ciki

 BABI NA SHA UKU

Mu Daraja Rai da Allah Ya Ba Mu Kyauta

Mu Daraja Rai da Allah Ya Ba Mu Kyauta

1. Waye ne ya ba mu rai?

JEHOBAH “Allah mai-rai ne.” (Irmiya 10:10) Shi ne Mahaliccinmu kuma shi ya ba mu rai. Littafi Mai Tsarki ya ce: “Kai ka halicci dukan abu, saboda nufinka kuma suka kasance, saboda nufinka aka halicce su.” (Ru’ya ta Yohanna 4:11) Hakika, Jehobah yana son mu rayu. Rai kyauta ce daga wurinsa.—Karanta Zabura 36:9.

2. Me ya kamata mu yi idan muna so mu yi nasara a rayuwa?

2 Jehobah ya ba mu abubuwan da muke bukata, kamar abinci da kuma ruwa. (Ayyukan Manzanni 17:28) Ƙari ga haka, yana son mu ji daɗin rayuwa. (Ayyukan Manzanni 14:15-17) Idan muna so mu yi nasara a rayuwa, ya kamata mu bi dokokin Allah.—Ishaya 48:17, 18.

RA’AYIN ALLAH GAME DA RAI

3. Mene ne Jehobah ya yi sa’ad da Kayinu ya kashe Habila?

3 Littafi Mai Tsarki ya ce rai da muke da shi yana da daraja a gaban Jehobah. Alal misali, a lokacin da Kayinu ɗan Adamu da Hawwa’u ya yi fushi sosai da ɗan’uwansa Habila, Jehobah ya gargaɗe shi. Maimakon Kayinu ya yi biyayya da abin da Allah ya gaya masa, sai ya yi fushi sosai har “ya tasar wa Habila ƙanensa, ya kashe shi.” (Farawa 4:3-8) Allah ya yi wa Kayinu horo don ya kashe Habila. (Farawa 4:9-11) Yin fushi da ƙiyayya suna da hatsari don za su iya sa mu yi faɗa ko kuma mugunta. Duk  mutumin da yake irin wannan halin ba zai sami rai na har abada ba. (Karanta 1 Yohanna 3:15.) Idan muna son mu faranta wa Jehobah rai, dole ne mu ƙaunaci dukan mutane.—1 Yohanna 3:11, 12.

4. Mene ne ɗaya cikin dokokin da Allah ya ba Isra’ilawa ya koya mana game da kyautar rai da Allah ya ba mu?

4 Dubban shekaru bayan haka, Dokoki goma da Jehobah ya ba Musa sun nuna cewa yana ɗaukan rai da daraja. Ɗaya daga cikin dokokin ya ce: “Ba za ka yi kisankai ba.” (Kubawar Shari’a 5:17) Idan mutum ya kashe wani da gangan, shi ma za a kashe shi.

5. Yaya Allah yake ɗaukan zub da ciki?

5 Yaya Allah yake ɗaukan zub da ciki? Har ran yaro da ke cikin mamarsa ma yana da daraja a gaban Jehobah. A Dokar da Jehobah ya ba Isra’ilawa, ya ce idan wani ya ji ma mace mai juna biyu rauni kuma jaririn da ke cikinta ya mutu, za a kashe mutumin. (Karanta Fitowa 21:22, 23; Zabura 127:3.) Wannan ya koya mana cewa zub da ciki laifi ne.—Ka duba Ƙarin bayani na 28.

6, 7. Ta yaya muke nuna wa Jehobah cewa muna ɗaukan rai da daraja?

6 Ta yaya za mu nuna wa Jehobah cewa muna daraja ranmu da kuma na wasu? Ta wurin ƙin yin wasu abubuwan da za su sa rayukanmu da na wasu cikin haɗari. Don haka, bai kamata mu sha tabar sigari ko wi-wi ko kuma miyagun ƙwayoyi ba. Me ya sa? Don za su iya yi mana lahani har ma su kashe mu.

7 Da yake Allah ne ya ba mu rai da kuma jiki, ya kamata mu yi amfani da su a hanyar da yake so. Don haka, ya kamata mu kula da jikinmu sosai. Idan ba mu yi hakan ba, ba za mu kasance da tsabta a gaban Allah ba. (Romawa 6:19; 12:1; 2 Korintiyawa 7:1) Idan ba ma  daraja rai, ba zai yiwu mu bauta wa Jehobah ba domin shi ne ya ba mu rai. Ko da yake yana da wuya mu daina wasu munanan halayen da muke da su, Jehobah zai taimaka mana idan muna ƙoƙari mu nuna cewa muna daraja rai.

8. Mene ne za mu yi don mu tabbata cewa ranmu da na wasu ba sa cikin haɗari?

8 Mun koya cewa rai kyauta ce daga wurin Allah. Jehobah ya tabbata cewa za mu yi iya ƙoƙarinmu don kada mu sa ranmu da na wasu cikin haɗari. Muna yin haka ta yadda muke tuƙa motocinmu da kekunanmu da kuma babur. Ƙari ga haka, muna guje wa wasu irin wasannin da za su saka rayukanmu cikin haɗari. (Zabura 11:5) Kuma zai dace mu sa gidajenmu su kasance marar haɗari. Jehobah ya dokaci Isra’ilawa cewa: “Sa’anda ka gina sabon gida, sai ka ja rawani bisa bene, domin kada ka ja wa gidanka alhakin jini, idan wani ya faɗo daga can.”—Kubawar Shari’a 22:8.

9. Yaya ya kamata mu bi da dabbobi?

9 Yadda muke bi da dabbobi ma yana da muhimmanci a gaban Jehobah. Allah ya yarda mu riƙa yanka dabbobi don abinci da kuma kayan sakawa. Ƙari ga haka, ya amince mu kashe dabbobi idan suna so su yi mana lahani. (Farawa 3:21; 9:3; Fitowa 21:28) Amma bai kamata mu kashe dabbobi ba gaira ba dalili ba ko kuma mu kashe su don wasa.—Misalai 12:10.

KA DARAJA RAI

10. Ta yaya muka sani cewa jini yana wakiltar rai?

10 Jini yana da tsarki a gaban Jehobah don jini yana wakiltar rai. Bayan da Kayinu ya kashe Habila, Jehobah ya ce masa: “Muryar jinin ƙaninka ta yi ƙara a wurina  daga ƙasa.” (Farawa 4:10) Jinin Habila yana wakiltar ransa kuma Jehobah ya yi wa Kayinu horo don ya kashe ɗan’uwansa Habila. Bayan ambaliyar ruwan da aka yi a zamanin Nuhu, Jehobah ya sake nuna cewa jini yana wakiltar rai. Jehobah ya amince Nuhu da iyalinsa su ci naman dabbobi. Ya ce: “Kowane abu mai-motsi wanda yake da rai za ya zama abincinku; kamar ganye duk na ba ku su.” Amma akwai abu ɗaya da Jehobah ya dokace su kada su ci: “Sai dai nama tare da ransa, watau jininsa ke nan, wannan ba za ku ci ba.”—Farawa 1:29; 9:3, 4.

11. Wace doka game da jini ce Allah ya ba al’ummar Isra’ila?

11 Bayan wajen shekara ɗari takwas da Allah ya dokaci Nuhu kada ya ci jini, ya sake ba mutanensa wannan umurnin: “Kuma kowane mutum wanda ke na ’ya’yan Isra’ila, ko kuwa na baƙin da ke sauke daga cikinsu wanda yana farauta ya kama kowane nama, ko tsuntsu, halal ga ci; sai shi zubar da jininsa, ya rufe da ƙura.” Sai ya ƙara da cewa: “Ba za ku ci jini” ba. (Levitikus 17:13, 14) Har ila, Jehobah ya so mutanensa su ɗauki jini da tsarki. Ya ce su ci nama amma ban da jini. Kuma ya gaya musu cewa idan suka yanka dabba, su zubar da jininsa a ƙasa.

12. Ta yaya Kiristoci suke ɗaukan jini?

12 Wasu shekaru bayan mutuwar Yesu, manzanni da kuma dattawa da ke ikilisiyar Kirista a Urushalima sun yi taro don su san wasu fannonin Dokar da Allah ya ba Isra’ilawa da ya shafi Kiristoci. (Karanta Ayyukan Manzanni 15:28, 29; 21:25.) Jehobah ya taimaka musu su fahimci cewa har ila jini yana da tsarki a gareshi kuma ya kamata su ma su ɗauke shi da tsarki. Bai kamata Kiristoci na farko su ci ko sha jini ko kuma su ci mushe ba.  Za a iya kwatanta yin hakan da bautar gumaka ko kuma yin lalata. Daga wannan lokacin, Kiristoci na gaskiya sun daina ci ko kuma shan jini. A yau kuma fa? Jehobah yana so mu ɗauki jini da tsarki.

13. Me ya sa bai dace Kiristoci su amince da ƙarin jini ba?

13 Shin hakan yana nufin cewa bai kamata a yi wa Kiristoci ƙarin jini ba? Ƙwarai kuwa. Jehobah ya dokace mu kada mu ci ko kuma mu sha jini. Idan likita ya ce kada ka sha giya, za ka so a yi maka allurar giyar ne? Ko kaɗan! Haka ma, dokar nan na cewa kada mu ci ko sha jini yana nufin ƙin amincewa da ƙarin jini.—Ka duba Ƙarin bayani na 29.

14, 15. Me ya sa yake da muhimmanci Kiristoci su daraja rai kuma su yi biyayya ga Jehobah?

14 Mene ne za mu yi idan likita ya gaya mana cewa za mu mutu idan ba mu karɓi ƙarin jini ba? Kowanenmu ya kamata ya tsai da shawara a kan wannan Dokar Allah da kansa. Kiristoci suna ɗaukaka wannan kyautar rai da Allah ya ba mu, duk da haka, ba sa amincewa da ƙarin jini. Suna neman wasu hanyoyin jinya da ba su shafi jini ba.

15 Muna iya ƙoƙarinmu don mu kula da lafiyar jikinmu, amma da yake rai yana da daraja a wurin Allah, ba za mu karɓi ƙarin jini ba. Gwamma mu yi biyayya ga Jehobah, maimakon mu yi rashin biyayya don ba ma son mu mutu. Yesu ya ce: “Dukan wanda yake nufi shi ceci ransa, ɓad da ransa shi yake yi: kuma dukan wanda yake ɓad da ransa sabili da ni, samunsa yake yi.” (Matta 16:25) Muna so mu yi biyayya ga Jehobah don muna ƙaunar sa. Ya san abin da ya fi dacewa da mu kuma muna ɗaukan rai da daraja da kuma tsarki yadda shi ma yake yi.—Ibraniyawa 11:6.

16. Me ya sa bayin Allah suke masa biyayya?

 16 Bayin Allah masu aminci sun ƙuduri aniya su yi biyayya ga dokarsa game da jini. Ba za su ci ko sha jini ba kuma bai dace su karɓi ƙarin jini don jinya ba. * Amma za su iya amincewa da wasu jinya don su kāre ransu. Sun tabbata cewa Mahaliccin rai da jini ya san abin da ya dace da su. Shin ka gaskata cewa Allah ya san abin da ya fi dacewa da kai?

HANYA ƊAYA TAK TA YIN AMFANI DA JINI DA JEHOBAH YA AMINCE DA ITA

17. Wace hanya ɗaya ce kaɗai Jehobah ya amince a yi amfani da jini?

17 Jehobah ya gaya wa Isra’ilawa a Dokar da ya bayar ta hannun Musa cewa: ‘Gama ran nama yana cikin jini: na kuwa ba ku shi bisa bagadi domin a yi kafarar [wato, don neman gafarar] rayukanku: gama jini ne ke yin kafara saboda rai.’ (Levitikus 17:11) Idan Isra’ilawa suka yi zunubi, za su iya neman gafara ta wurin yin hadaya da dabba kuma firist ne zai zuba jinin a kan bagadi a haikalin. A wannan hanya ce kaɗai Jehobah ya amince a yi amfani da jini.

18. Ta yaya muke amfana daga hadayar Yesu?

18 A lokacin da Yesu ya zo duniya, ya ba da ransa ko kuma jininsa don mu sami gafarar zunubai kuma hakan ya sa an daina yin hadayu da dabbobi. (Matta 20:28; Ibraniyawa 10:1) Ran Yesu yana da daraja sosai shi ya sa bayan da Jehobah ya tashe shi zuwa sama, Jehobah ya ba dukan mutane gatan yin rayuwa a duniya har abada.—Yohanna 3:16; Ibraniyawa 9:11, 12; 1 Bitrus 1:18, 19.

Ta yaya za ka nuna cewa kana daraja rai da kuma jini?

19. Me ya wajaba mu yi don mu kuɓuta “daga jinin dukan mutane”?

 19 Muna godiya ga Jehobah don wannan kyauta mai tamani da ya ba mu, wato rai! Kuma muna so mu gaya wa mutane cewa idan sun ba da gaskiya ga Yesu, za su yi rayuwa har abada. Muna ƙaunar mutane kuma muna iya ƙoƙarinmu don mu koya musu abin da za su yi don su sami rai. (Ezekiyel 3:17-21) Kamar manzo Bulus, za mu iya cewa: “Ni kuɓutace ne daga jinin dukan mutane. Gama ban ji nauyin bayana maku dukan shawarar Allah” ba. (Ayyukan Manzanni 20:26, 27) Hakika, muna nuna cewa muna daraja rai da jini sa’ad da muka gaya wa mutane game da Jehobah da kuma yadda rai yake da daraja a gareshi.

^ sakin layi na 16 Don ƙarin bayani game da ƙarin jini, ka duba littafin nan “Ku Tsare Kanku Cikin Ƙaunar Allah,” shafuffuka na 77-79 wanda Shaidun Jehobah suka wallafa.