Koma ka ga abin da ke ciki

Koma ga abubuwan da ke ciki

 BABI NA SHA TARA

Ka Kasance Kusa da Jehobah

Ka Kasance Kusa da Jehobah

1, 2. A ina za mu sami wurin ɓuya ko mafaka?

A CE kana tafiya wani wuri sai hadari ya ɗauro kuma aka soma iska mai ƙarfi. Gari ya yi duhu kuma aka soma walƙiya da tsawa. Jim kaɗan bayan haka, sai aka soma ruwa kuma ka fara neman wurin ɓoyewa. Kana kan nema sai ka ga wani wuri mai kyau da za ka ɓuya. Babu shakka, hankalinka zai kwanta, ko ba haka ba?

2 Haka yanayinmu yake a yau. Abubuwa suna daɗa lalacewa a duniya yanzu. Za ka iya yin tunani, ‘A ina zan sami wurin ɓuya ko mafaka?’ Wani marubucin Zabura ya ce: “Zan ce da Ubangiji, shi ne mafakata da marayata kuma; Allahna, a gareshi nake dogara.” (Zabura 91:2) Hakika, Jehobah zai iya sauƙaƙa matsalolin da muke fuskanta yanzu kuma zai yi mana abubuwa masu kyau sosai a nan gaba.

3. Yaya za mu iya sa Jehobah ya zama mafakarmu?

3 Ta yaya Jehobah yake kāre mu? Yana yin hakan ta wajen taimaka mana mu magance duk wata matsalar da muke fuskanta kuma ya fi ƙarfin kowane mutum da zai so ya yi mana lahani. Ko da wani mummunan abu ya same mu a yau, muna da tabbaci cewa Jehobah zai kawar da shi a nan gaba. Littafi Mai Tsarki ya ce: “Ku tsare kanku cikin ƙaunar Allah.” (Yahuda 21) Ya kamata mu kasance kusa da Jehobah don ya taimake mu a lokuta masu wuya. Amma yaya za mu yi hakan?

 KA NUNA GODIYA DON ƘAUNAR DA ALLAH YAKE MANA

4, 5. Ta yaya Jehobah ya nuna cewa yana ƙaunarmu?

4 Idan muna son mu kasance kusa da Jehobah, muna bukatar mu san cewa yana ƙaunarmu sosai. Ka yi tunani a kan dukan abubuwa masu kyau da Jehobah ya yi mana. Ya halicci wannan duniya mai kyau da dukan itatuwa da kuma dabbobi da ke cikinta dominmu. Ya kuma ba mu abinci masu ɗanɗano da kuma ruwa mai tsabta. Jehobah ya koya mana sunansa da kuma halayensa masu kyau a cikin Littafi Mai Tsarki. Mafi muhimmanci ma, ya aiko da Ɗansa da yake ƙauna, wato Yesu Kristi zuwa duniya ya mutu dominmu. (Yohanna 3:16) Kuma wannan fansar da Ɗansa ya yi ta sa mun sami begen yin rayuwa har abada a nan gaba.

5 Jehobah ya kafa Mulkinsa kuma wannan Mulkin zai cire dukan matsalolinmu nan ba da daɗewa ba. Mulkin zai mayar da duniya aljanna, yadda kowa zai kasance da kwanciyar hankali da kuma farin cikin har abada. (Zabura 37:29) Wata hanya kuma da Jehobah yake nuna cewa yana ƙaunarmu ita ce ta wajen koya mana yadda za mu bi da rayuwarmu yanzu. Ƙari ga hakan, ya ce mu yi addu’a kuma yana shirye ya amsa addu’o’inmu. Jehobah ya nuna sarai cewa yana ƙaunar kowannenmu.

6. Me ya kamata ka yi don yadda Jehobah yake ƙaunarka?

6 Me ya kamata ka yi don yadda Jehobah yake ƙaunarka? Ka nuna masa cewa kana godiya don dukan tanadin da ya yi maka. Abin baƙin ciki ne cewa mutane da yawa a yau ba sa nuna godiya. Haka ya taɓa faruwa sa’ad da Yesu yake duniya. Akwai wani lokacin da Yesu ya warkar da kutare goma, amma ɗaya ne tak ya ce ya gode. (Luka 17:12-17) Muna so mu zama kamar wannan mutumin da ya  gode wa Yesu. Muna bukatar mu riƙa gode wa Jehobah a kowane lokaci.

7. Yaya ya kamata mu ƙaunaci Jehobah?

7 Muna kuma bukatar mu nuna cewa muna ƙaunar Jehobah. Yesu ya gaya wa almajiransa cewa wajibi ne su ƙaunaci Jehobah da dukan zuciyarsu da dukan ransu da kuma dukan hankalinsu. (Karanta Matta 22:37.) Me hakan yake nufi?

8, 9. Yaya za mu nuna cewa muna ƙaunar Jehobah?

8 Shin furta cewa muna ƙaunar Jehobah yana nufin cewa muna yin hakan da gaske? A’a. Idan muna ƙaunar Jehobah da dukan zuciyarmu da dukan ranmu da kuma dukan hankalinmu, to, ayyukanmu za su nuna hakan. (Matta 7:16-20) Littafi Mai Tsarki ya ce za mu bi dokokin Allah idan muna ƙaunar sa. Shin yin hakan yana da wuya ne? A’a, domin dokokin Jehobah “ba su da ban ciwo.”—Karanta 1 Yohanna 5:3.

9 Za mu yi farin ciki da kuma rayuwa mai ma’ana idan muka bi dokokin Jehobah. (Ishaya 48:17, 18) Amma mene ne zai taimaka mana mu kasance kusa da Jehobah? Bari mu ga amsar.

KA CI GABA DA KUSANTAR JEHOBAH

10. Me ya sa ya kamata ka ci gaba da koyo game da Jehobah?

10 Ta yaya ka zama aminin Jehobah? Nazarin Littafi Mai Tsarki da kake yi ya taimaka maka ka san Jehobah da kuma ƙulla dangantaka da shi. Wannan dangantakar tana kamar wutar da kake so ta ci gaba da ci. Kamar yadda wuta take bukatar itace don ta ci gaba da ci, haka ma kake bukatar ka ci gaba da koyo game da Jehobah don dangantakarku ta yi ƙarfi.—Misalai 2:1-5.

Ƙaunarmu ga Jehobah tana kamar wutar da ke bukatar itace don ta ci gaba da ci

11. Ta yaya koyarwar Littafi Mai Tsarki za ta shafe ka?

11 Yayin da kake ci gaba da yin nazarin Littafi Mai Tsarki,  za ka koya abubuwan da za su ratsa zuciyarka. Ka lura yadda almajiran Yesu biyu suka ji sa’ad da Yesu yake bayyana musu annabcin Littafi Mai Tsarki. Sun ce: ‘Zuciyarmu ba ta yi ƙuna daga cikinmu ba, sa’anda yake yi mana zance a kan hanya, yana bayyana mana littattafai?’—Luka 24:32.

12, 13. (a) Mene ne zai iya faruwa da ƙaunarmu ga Allah? (b) Me za mu iya yi don kada dangantakarmu da Jehobah ta yi tsami?

12 Kamar yadda zukatan almajiran Yesu suka yi ƙuna sa’ad da suka fahimci Nassosi, wataƙila kai ma ka ji hakan sa’ad da ka soma fahimtar Littafi Mai Tsarki. Hakan ya taimaka maka ka san Jehobah kuma ka ƙaunace shi. Babu shakka, ba ka son wannan ƙaunar ta yi sanyi.—Matta 24:12.

13 Da zarar ka zama aminin Allah, kana bukatar ka yi ƙoƙari don kada dangantakarka da Shi ta yi tsami. Wajibi ne ka ci gaba da koyo game da Jehobah da Yesu, kuma ka yi tunani a kan abin da kake koya da kuma yadda za ka yi  amfani da shi. (Yohanna 17:3) A duk lokacin da ka karanta ko kuma ka yi nazarin Littafi Mai Tsarki, zai dace ka tambayi kanka: ‘Mene ne hakan yake koya mini game da Jehobah? Me ya sa nake bukatar in ƙaunace shi da dukan zuciyata da kuma dukan raina?’—1 Timotawus 4:15.

14. Ta yaya addu’a take sa ƙaunarmu ga Jehobah ta yi ƙarfi?

14 Tattaunawa da amininka a kai a kai yana sa dangantakarku ta yi ƙarfi. Hakazalika, yin addu’a ga Jehobah a kai a kai yana sa mu ƙaunace shi sosai. (Karanta 1 Tasalonikawa 5:17.) Addu’a babbar gata ce daga Ubanmu na sama. Ya kamata mu riƙa gaya masa abin da ke zuciyarmu. (Zabura 62:8) Bai kamata mu haddace addu’armu ba, amma mu tabbatar da abin da muke faɗa. Hakika, idan mun ci gaba da yin nazarin Littafi Mai Tsarki kuma muka yi addu’a daga zuciyarmu, ƙaunarmu ga Jehobah za ta yi ƙarfi.

KOYA WA MUTANE GAME DA JEHOBAH

15, 16. Yaya kake ɗaukan yin wa’azi?

15 Idan muna so mu kasance kusa da Jehobah, muna bukatar mu gaya ma wasu abin da muka yi imani da shi. Gaya wa mutane game da Jehobah babban gata ne. (Luka 1:74) Aiki ne da Yesu ya ba dukan Kiristoci na gaskiya. Kowannenmu yana bukatar ya yi wa’azi game da Mulkin Allah. Shin ka riga ka soma yin hakan?—Matta 24:14; 28:19, 20.

16 Manzo Bulus ya san cewa yin wa’azi yana da muhimmanci sosai, shi ya sa ya kira shi aiki “mai-daraja.” (2 Korintiyawa 4:7) Gaya wa mutane game da Jehobah da kuma nufinsa ne aiki mafi muhimmanci. Idan muka yi wa’azi, muna wa Jehobah hidima ne kuma yana daraja abin da muke yi. (Ibraniyawa 6:10) Yin wa’azi kuma zai iya amfanar ka da kuma mutanen da suka saurare ka. Me ya sa? Domin kana taimaka ma wasu da kuma kanka ku  kusaci Jehobah kuma ku sami rai na har abada. (Karanta 1 Korintiyawa 15:58.) Babu wani aikin da zai sa ka farin ciki kamar wannan.

17. Me ya sa yin wa’azi yake da gaggawa?

17 Muna bukatar yin wa’azi da gaggawa sosai. Nassi ya ƙarfafa mu mu “yi wa’azin kalma” kuma mu “yi naciya” a kai. (2 Timotawus 4:2) Mutane suna bukatar su ji bishara game da Mulkin Allah. Littafi Mai Tsarki ya ce: “Babbar ranar Ubangiji ta gabato, tana gabatowa da sauri.” Ƙarshen wannan zamanin “ba zai makara ba.” (Zafaniya 1:14; Habakkuk 2:3; Littafi Mai Tsarki) Hakika, Jehobah zai halaka wannan duniyar Shaiɗan nan ba da daɗewa ba. Amma kafin ya yi hakan, muna bukatar mu gargaɗi mutane domin su yanke shawarar bauta wa Jehobah.

18. Me ya sa muke bukatar mu bauta wa Jehobah tare da sauran Kiristoci na gaskiya?

18 Jehobah yana so mu bauta masa tare da sauran Kiristoci na gaskiya. Littafi Mai Tsarki ya ce: ‘Bari kuma mu lura da juna domin mu tsokani [wato ƙarfafa] juna zuwa ga ƙauna da nagargarun ayyuka; kada mu fasa tattaruwanmu, kamar yadda waɗansu sun saba yi, amma mu gargaɗar da juna; balle fa yanzu, da kuna ganin ranan nan tana gusowa.’ (Ibraniyawa 10:24, 25) Ya kamata mu yi iya ƙoƙarinmu don mu kasance a dukan taronmu. Waɗannan taron suna ba mu damar ƙarfafa juna.

19. Mene ne zai taimaka mana mu ƙaunaci ’yan’uwanmu Kiristoci?

19 Idan kana halartar taronmu, za ka haɗu da abokan kirki da za su taimaka maka ka bauta wa Jehobah. Za ka haɗu da ’yan’uwa maza da mata kamar kai da suke iya ƙoƙarinsu su bauta masa. Suna kamar kai domin a wasu lokuta suna iya yin kuskure. Idan suka yi abin da ba daidai ba, sai ka yafe musu. (Karanta Kolosiyawa 3:13.) Ka riƙa mai da hankali ga halaye masu kyau na ’yan’uwanka  maza da mata, domin yin hakan zai taimaka maka ka ƙaunace su kuma ka kusaci Jehobah.

RAI NA HAKIKA

20, 21. Mene ne “rai wanda yake na hakika”?

20 Jehobah yana son dukan aminansa su ji daɗin rayuwa. Littafi Mai Tsarki ya koya mana cewa rayuwar da za mu yi a nan gaba za ta yi dabam da wadda muke yi yanzu.

Jehobah yana so ka ji daɗin ‘rai na hakika.’ Shin za ka sami wannan rai kuwa?

21 A nan gaba, ba za mu rayu shekara 70 ko 80 ba, amma har abada. Za mu ji daɗin “rai na har abada” cikin ƙoshin lafiya da salama da kuma farin ciki a aljanna mai kyan gaske. Abin da Littafi Mai Tsarki ya kira “rai wanda yake na hakika” ke nan. Jehobah ya yi alkawarin ba mu wannan rai na hakika. Muna bukatar mu yi iya ƙoƙarinmu yanzu don mu sami wannan rai.—1 Timotawus 6:12, 19, LMT.

22. (a) Ta yaya za mu iya ‘riƙe rai wanda yake na hakika’? (b) Me ya sa samun rai na har abada ba hakkinmu ba ne?

22 Ta yaya za mu iya ‘riƙe rai wanda yake na hakika’? Wajibi ne mu “yi alheri” kuma mu zama “mawadata cikin kyawawan ayyuka.” (1 Timotawus 6:18) Hakan yana nufin cewa muna bukatar mu yi abin da muke koya a Littafi Mai Tsarki. Amma, ba ƙoƙarin da muke yi ba ne zai sa mu sami wannan rai ba. Samun rai na har abada ba hakkinmu ba ne. Me ya sa? Domin kyauta ce da Jehobah yake ba dukan amintattun bayinsa saboda ‘alherinsa.’ (Romawa 5:15) Ubanmu na sama yana so ya ba bayinsa masu aminci wannan kyautar.

23. Me ya sa muke bukatar yanke shawara mai kyau yanzu?

23 Ka tambayi kanka, ‘Shin ina bauta wa Allah a hanyar da yake so kuwa?’ Idan ka lura cewa kana bukatar yin wasu canje-canje, zai dace ka yi hakan ba tare da ɓata lokaci ba. Idan muka dogara ga Jehobah kuma muka yi iya ƙoƙarinmu don mu yi masa biyayya, zai zama  mafakarmu. Zai kāre bayinsa masu aminci a wannan ƙarshen mugun zamanin Shaiɗan. Bayan haka, Jehobah zai tabbatar cewa mun kasance cikin Aljanna har abada, kamar yadda ya yi alkawari. Babu shakka, za ka iya samun rai na hakika, idan ka yanke shawara mai kyau yanzu!