Me Za Mu Koya Daga Littafi Mai Tsarki?

An shirya wannan littafin domin ya taimaka maka ka sami amsoshin Littafi Mai Tsarki a kan tambayoyi kamar su, dalilin da ya sa muke shan wahala da me ke faruwa sa’ad da mutum ya mutu da yadda iyalinmu za ta zauna lafiya da dai sauransu.

Me Ya Sa Allah Ya Halicce Mu?

Za ka iya tunanin abin da ya sa muke shan wahala a yau. Littafi Mai Tsarki ya ce nan ba da dadewa ba, Allah zai kawo karshen shan wahala da ciwo da kuma mutuwa.

BABI NA 1

Wane ne Allah?

Kana ganin Allah ya damu da kai kuwa? Ka koya game da halayen Allah da kuma yadda za ka iya zama amininsa.

BABI NA 2

Littafi Mai Tsarki Maganar Allah Ne

Ta yaya Littafi Mai Tsarki zai taimaka maka ka bi da matsalolinka na yau da kullum? Me ya sa za ka iya tabbatar da annabcin da ke cikinsa?

BABI NA 3

Me Ya Sa Allah Ya Halicci Mutane?

Yaya rayuwa za ta kasance a nan gaba sa’ad da duniya ta zama aljanna?

BABI NA 4

Wane ne Yesu Kristi?

Ka koya dalilin da ya sa Yesu ne almasihu da aka yi alkawarinsa, da kuma inda ya fito da kuma dalilin da ya sa shi ne makadaicin dan Allah.

BABI NA 5

Fansa, Kyauta ce Mafi Girma Daga Allah

Mece ce fansar? Ta yaya za ta amfane ka?

BABI NA 6

Me Ke Faruwa da Mutum Sa’ad da Ya Mutu?

Ka koya abin da Littafi Mai Tsarki ya ce game da wurin da matattu suke da kuma dalilin da ya sa mutane suke mutuwa.

BABI NA 7

Za a Ta da Matattu!

Dan’uwanka ya taba rasuwa kuwa? Zai yiwu ka sake ganinsa kuwa? Ka koya abin da Littafi Mai Tsarki ya ce game da tashin matattu.

BABI NA 8

Mene ne Mulkin Allah?

Mutane da yawa sun san addu’ar ubangijinmu. Mene ne ma’anar furucin nan: “Mulkinka shi zo”?

BABI NA 9

Shin Karshen Duniya Ya Kusa?

Ka bincika yadda abubuwan da ke faruwa da kuma halayen mutane suka nuna cewa muna rayuwa gab da karshen wannan zamanin, kamar yadda Littafi Mai Tsarki ya annabta.

BABI NA 10

Gaskiya Game da Mala’iku da Kuma Aljanu

Littafi Mai Tsarki ya yi magana game da mala’iku da aljanu. Shin wadannan halittun ruhu sun wanzu da gaske? Za su iya taimaka maka ko kuma yi mana lahani?

BABI NA 11

Me Ya Sa Muke Shan Wahala Sosai?

Mutane da yawa suna ganin Allah da laifi don wahalar da ke duniya. Mene ne ra’ayinka? Ka koya abin da Littafi Mai Tsarki ya ce ya sa muke shan wahala.

BABI NA 12

Ta Yaya Za Ka Iya Zama Aminin Allah?

Zai yiwu mu faranta wa Jehobah rai. Babu shakka, za ka iya zama amininsa.

BABI NA 13

Mu Daraja Rai da Allah Ya Ba Mu Kyauta

Mene ne ra’ayin Allah game da zub da ciki da karban karin jini da kuma ran dabba?

BABI NA 14

Yadda Iyalinka Za Ta Zauna Lafiya

Kaunar da Yesu ya nuna misali ne mai kyau ga mazaje da mata da iyaye da kuma yara. Me za mu iya koya daga wurinsa?

BABI NA 15

Yadda Ya Dace a Bauta wa Allah

Ka bincika abubuwa shida da ke nuna mutanen da ke bin addini na gaskiya.

BABI NA 16

Ka Yanke Shawarar Bauta wa Allah

Wadanne kalubale za ka fuskanta sa’ad da kake gaya wa wasu abubuwan da ka koya? Ta yaya za ka yi hakan ba tare da bata musu rai ba?

BABI NA 17

Gatan da Muke da Shi na Yin Addu’a

Shin Allah yana jin addu’o’inmu kuwa? Sanin abin da Littafi Mai Tsarki ya ce game da addu’a zai taimaka maka ka san amsar.

BABI NA 18

Alkawarin Yin Nufin Allah da Kuma Baftisma

Wadanne matakai muke bukata mu dauka kafin mu cancanci yin baftisma? Ka bincika abin da baftisma take nufi da kuma yadda ya kamata a yi.

BABI NA 19

Ka Kasance Kusa da Jehobah

Ta yaya za mu nuna kauna da godiya ga dukan abubuwan da Allah yake yi mana?

Karin bayanai

Ma’anar kalmomi da furucin da aka yi amfani da su a littafin nan Me Za Mu Koya Daga Littafi Mai Tsarki?