Koma ka ga abin da ke ciki

Koma ga abubuwan da ke ciki

Wasiƙa Daga Hukumar da Ke Kula da Ayyukan Shaidun Jehobah

Wasiƙa Daga Hukumar da Ke Kula da Ayyukan Shaidun Jehobah

’Yan’uwa Masu Shela:

A CE kana hidima a Bethel da ke Brooklyn kuma da safiyar ranar Jumma’a, 2 ga Oktoba, 1914, kana zaune a wurin zamanka a cikin ɗakin cin abinci kana jiran Ɗan’uwa C. T. Russell ya shigo. Sai farat ɗaya ƙofar ta buɗe kuma Ɗan’uwa Russell ya shigo. Ya ɗan dakata, sai ya gai da iyalin Bethel da fara’a kamar yadda ya saba yi, ya ce: “Ina kwananku.” Bayan haka, maimakon ya je wurin zamansa, sai ya tafa hannu ya ce: “Lokacin Al’ummai ya ƙare; kuma zamanin sarakuna ya wuce!” Ka yi farin ciki matuƙa domin ka daɗe kana jiran wannan lokacin! Sai kai da sauran ’yan’uwa a Bethel kuka tafa sosai.

Yanzu, shekaru da yawa sun wuce tun lokacin da Ɗan’uwa Russell ya yi wannan furucin. Mene ne Mulkin ya cim ma tun lokacin?  Hakika, Mulkin ya cim ma abubuwa da yawa. Jehobah yana amfani da Mulkin don ya koyar da mutanensa da kuma yi musu gyara. Ya soma yin hakan daga shekara ta 1914, a lokacin da mutanensa ’yan dubbai ne kawai zuwa yau da mutanensa sun fi miliyan bakwai da dubu ɗari biyar. A waɗanne hanyoyi ne ka amfana daga irin wannan koyarwar?

A yau, muna yawan jin ’yan’uwa suna cewa, “Ƙungiyar Jehobah tana samun ci gaba!” kuma hakan gaskiya ce. Amma dai, tun shekara ta 1914, karusar da ke wakiltar sashen ƙungiyar Jehobah da ke sama tana ci gaba kullum, kamar yadda za mu gani ta wurin nazarin wannan littafin. Masu shelar bisharar Mulkin Allah sun yi amfani da hanyoyi dabam-dabam don yaɗa bishara a faɗin duniya. Alal misali, sun yi yawo da fosta kuma sun yi amfani da jaridu da hotuna da katuna da rediyo da garmaho da kuma Intane.

Da taimakon Jehobah, yanzu muna wallafa littattafai da ke bayyana Littafi Mai Tsarki a harsuna sama da 670, kuma muna rarraba wa mutane ba a kan wani farashi ba. Wasu sun ba da kai wajen gina Majami’un Mulki da Majami’un Taro da ofisoshin reshe, duk a ƙasashe masu arziki da kuma ƙasashen da ake ƙarancin arziki. Sa’ad da bala’i ya auku ma, ’yan’uwa maza da mata sukan ba da agaji nan da nan. Wannan tabbaci ne cewa su masu taimako ne a “kwanakin shan wuya.”—Mis. 17:17.

A wasu lokatai, limaman addini da kuma sauran magabtanmu suna sa a yi mana ‘hukunci na zalunci.’ Amma, yayin da muka yi la’akari da yadda ƙoƙarinsu yakan ci tura sau da sau har ma ya kai ga “yaɗuwar bishara,” hakan yana ƙarfafa mu sosai.—Isha. 10:1; Filib. 1:12.

Yin tarayya da ku ’yan’uwa gata ne babba, domin dukanmu ’yan ‘gidan’ Sarki Yesu Kristi ne. Ku san cewa muna ƙaunar ku sosai kuma muna fata cewa bayanin da ke cikin littafin nan zai taimaka muku ku ɗauki gādonku da muhimmanci sosai.—Mat. 24:45.

Da fatan alheri, mu

’Yan’uwanku,

Hukumar da Ke Kula da Ayyukan Shaidun Jehobah