Koma ka ga abin da ke ciki

Koma ga abubuwan da ke ciki

 BABI NA 17

Koyar da Masu Hidimar Mulkin

Koyar da Masu Hidimar Mulkin

MANUFAR WANNAN BABIN

Yadda makarantu na ƙungiyar Jehobah suke shirya masu hidimar Mulkin su yi hidimarsu da kyau

1-3. Ta yaya Yesu ya yaɗa bishara, kuma waɗanne tambayoyi za mu yi?

YESU ya yi wa’azi a Galili har tsawon shekaru biyu. (Karanta Matta 9:35-38.) Ya je birane da ƙauyuka da dama, yana koyarwa a cikin majami’u kuma yana wa’azin bishara game da Mulkin Allah. A duk inda Yesu ya yi wa’azi, jama’a sun bi shi. Yesu ya lura cewa “girbi hakika yana da yawa,” amma ana bukatar ƙarin ma’aikata.

2 Yesu ya yi shiri don a yi wannan wa’azin sosai. Ta yaya ya yi hakan? Ta wajen aika manzanni 12 “su yi wa’azin mulkin Allah.” (Luk 9:1, 2) Wataƙila manzannin sun yi tunani a kan yadda za su iya cika aikin. Amma kafin Yesu ya ce su soma aikin, ya koyar da su kamar yadda Ubansa na sama ya koyar da shi.

3 Hakan zai sa mu yi wasu tambayoyi kamar: Mene ne Uban ya koya wa Yesu? Mene ne Yesu ya koya wa manzanninsa? Kuma ta yaya Yesu, Sarkin Mulkin Allah yake koyar da mabiyansa a yau don su cika hidimarsu?

“Ina Faɗin Waɗannan Magana Yadda Uba Ya Koya Mani”

4. A yaushe ne Jehobah ya koyar da Yesu, kuma a ina ya yi masa koyarwar?

4 Yesu ya bayyana sarai cewa Ubansa ne ya koyar da shi. A lokacin da Yesu yake hidima a duniya, ya ce: “Ina faɗin waɗannan magana yadda Uba ya koya mani.” (Yoh. 8:28) A yaushe ne aka koyar da Yesu, kuma a ina? Babu shakka, an soma koyar da Ɗan fari na Allah nan da nan bayan an halicce shi. (Kol. 1:15) Ɗan ya yi shekaru da yawa a sama yana saurara da kuma lura da abin da Mai Koyarwa Mai Girma yake yi. (Isha. 30:20) A sakamakon haka, Ɗan ya koyi halaye da ayyuka da kuma nufin Ubansa sosai.

5. Wane umurni ne Uban ya ba Ɗansa game da hidimar da zai yi a duniya?

5 Da sannu-sannu, Jehobah ya koya wa Ɗansa yadda zai yi hidima a duniya. Ka yi la’akari da wani annabci da ya bayyana dangantakar da ke tsakanin Mai Koyarwa Mafi Girma da kuma Ɗansa na fari. (Karanta Ishaya 50:4, 5.) Annabcin ya ce Jehobah yakan tayar da Ɗansa “safiya kan safiya.” Wannan annabcin ya misalta Jehobah da malamin da ke tayar da  ɗalibinsa daga barci kowace safiya don ya koyar da shi. Wani littafin bincike na Littafi Mai Tsarki ya ce: “Kamar dai Jehobah . . . ya sa shi a makaranta, ya koya masa yadda zai yi wa’azi da kuma abin da zai yi wa’azi a kai.” A wannan “makarantar” da ke sama, Jehobah ya koya wa Ɗansa ‘abin da zai faɗa da maganar da zai yi.’ (Yoh. 12:49) Uban ya kuma ba Ɗansa umurni a kan yadda zai koyar da mutane. * Sa’ad da Yesu yake duniya, ya bi umurnin da Ubansa ya ba shi ta wajen cika hidimarsa kuma ya koyar da mabiyansa su cika hidimarsu.

6, 7. (a) Mene ne Yesu ya koya wa manzanninsa, kuma mene ne hakan ya shirya su su yi? (b) Wace koyarwa ce Yesu ya tabbata cewa mabiyansa suna mora a yau?

6 Mene ne Yesu ya koya wa manzanninsa kamar yadda aka ambata ɗazu? Littafin Matta sura 10 ta ce Yesu ya ba su takamaiman umurni game da yadda za su yi wa’azi kuma hakan ya haɗa da umurni game da: inda za su yi wa’azi (ayoyi na 5 da 6), abin da za su yi wa’azi a kai (aya ta 7), muhimmancin dogara ga Jehobah (ayoyi na 9 da 10), yadda za su gabatar da wa’azinsu (ayoyi na 11-13), yadda za su bi da mutanen da ba su saurare su ba (ayoyi na 14 da 15), da kuma abin da za su yi sa’ad da aka tsananta musu (ayoyi na 16-23). * Wannan koyarwar da Yesu ya yi wa manzanninsa kai tsaye ta taimaka musu su yi ja-gora a yin wa’azi a ƙarni na farko.

7 A yau kuma fa? Yesu Kristi wanda shi ne Sarkin Mulkin Allah, ya ba mabiyansa aiki mafi girma, wato yin bishara “ta mulki . . . ga dukan al’ummai.” (Mat. 24:14) Shin Sarkin ya koya mana yadda za mu yi wannan aikin? Ƙwarai kuwa! Sarkin ya tabbata cewa an koya wa mabiyansa yadda za su yi wa’azi ga mutane da kuma yadda za su gudanar da ayyuka na musamman a cikin ikilisiya. Ya cim ma dukan waɗannan abubuwan daga sama.

Yadda Ake Koyar da ’Yan’uwa Su Zama Masu Bishara

8, 9. (a) Mene ne ainihin manufar Makarantar Hidima ta Allah? (b) Ta yaya Makarantar Hidima ta Allah ta taimaka maka ka ƙware a hidima sosai?

8 Ƙungiyar Jehobah ta daɗe tana yin amfani da manyan taro da kuma taron ikilisiya, kamar Taron Hidima don koya wa bayin Allah yadda za su yi wa’azi. Amma daga shekara ta 1940 zuwa 1949, ’yan’uwa masu ja-gora a hedkwata sun soma yin amfani da makarantu dabam-dabam don a koyar masu wa’azi.

9 Makarantar Hidima ta Allah. Kamar yadda muka tattauna a babin da ya gabata, an soma makarantar nan ne a shekara ta 1943. Shin an kafa wannan makarantar ne don kawai a koya wa ’yan’uwa yin jawabai masu ƙayatarwa a taron ikilisiya? A’a. Ainihin manufar makarantar a dā da kuma yanzu ita ce koyar da bayin Allah su yi amfani da furucinsu wajen yabon Jehobah sa’ad da suke yin wa’azi. (Zab. 150:6) Makarantar tana koyar da dukan ’yan’uwa maza da mata don su kyautata yadda suke yin wa’azin Mulkin.

10, 11. Su waye ne za su iya zuwa Makarantar Gilead yanzu, kuma mene ne manufar makarantar?

 10 Makarantar Littafi Mai Tsarki ta Gilead. An soma makarantar a ranar 1 ga Fabrairu, 1943. An kafa makarantar ne asali don a koyar da majagaba da kuma wasu masu hidima ta cikakken lokaci don su yi wa’azi a ƙasashen waje. Amma daga watan Oktoba na 2011, waɗanda ake gayyata zuwa makarantar su ne: ’Yan’uwan da ke hidimar majagaba ta musamman da masu kula masu ziyara da matansu da masu hidima a Bethel da kuma masu wa’azi a ƙasashen waje da ba su halarci makarantar ba tukun.

11 Mene ne manufar Makarantar Littafi Mai Tsarki ta Gilead? Wani ɗan’uwa da ya daɗe yana koyarwa a makarantar ya ce: “Ana so ne a ƙarfafa bangaskiyar ɗaliban ta wajen nazarin Kalmar Allah sosai kuma a taimaka musu su kasance da halayen da za su taimaka musu su shawo kan ƙalubalen da za su fuskanta a hidimarsu. Wani dalili na musamman kuma da ya sa aka kafa makarantar shi ne don a taimaka wa ɗaliban su yi marmarin yin wa’azi.”—Afis. 4:11.

12, 13. Ta yaya makarantar Gilead ta taimaka a yin wa’azi a faɗin duniya? Ka ba da misali.

12 Ta yaya Makarantar Gilead ta taimaka wajen yin wa’azi a faɗin duniya? Tun shekara ta 1943, ɗalibai sama da 8,500 sun sauke karatu daga makarantar, * kuma sun yi wa’azi a sama da ƙasashe 170 a faɗin duniya. Masu wa’azi a ƙasashen waje sun yi amfani da koyarwar da aka yi musu ta wajen yin hidima da ƙwazo kuma sun koya wa wasu su yi hakan. A yawancin lokatai, ’yan’uwan ne suke ja-gora a yin wa’azi a yankunan da babu isashen masu shela ko kuma babu gaba ɗaya.

13 Ka yi la’akari da abin da ya faru a ƙasar Japan, inda aka daina yin wa’azi a lokacin Yaƙin Duniya na Biyu. Kafin watan Satumba na shekara ta 1949, masu shela da ke ƙasar baki ɗaya ba su kai goma ba. Amma a ƙarshen wannan shekarar, sai aka tura ’yan’uwa guda 13 da suka sauke karatu a Makarantar Gilead don su yi wa’azi a ƙasar Japan. Daga baya, aka daɗa tura wasu. Da farko, ’yan’uwan sun mai da hankali ga manyan birane, amma daga baya, sai suka koma wasu ƙananan birane. ’Yan’uwan sun ƙarfafa ɗalibansu da kuma wasu ’yan’uwa su soma hidimar majagaba. Shin sun sami sakamako mai kyau ne? Hakika! A yau, akwai masu shelar Mulki fiye da 216,000 a ƙasar Japan, kuma kusan kashi 40 cikin ɗari na masu shela majagaba ne! *

14. Wane tabbaci ne makarantun ƙungiyar Jehobah suke ba da? (Ka kuma duba akwatin nan “ Makarantun Koyar da Masu Hidimar Mulki,” a shafi na 188.)

14 Wasu makarantu na ƙungiyar Jehobah. Makarantar Hidima ta Majagaba da Makarantar Littafi Mai Tsarki don Kiristoci Ma’aurata da kuma Makarantar Littafi Mai Tsarki don ’Yan’uwa Maza Marasa Aure sun taimaka wa waɗanda suka halarta su kyautata dangantakarsu da Jehobah kuma su yi ja-gora a wa’azi. * Dukan waɗannan makarantun sun  ba da tabbaci cewa Sarkinmu ya koyar da mabiyansa sosai domin su cika hidimarsu.—2 Tim. 4:5.

Yadda Ake Koyar da ’Yan’uwa Maza Su Yi Ayyuka na Musamman

15. A waɗanne hanyoyi ne ya kamata maza masu hakki a ƙungiyar Jehobah su yi koyi da Yesu?

15 Annabcin Ishaya da muka ambata ɗazu ya ce Allah ya koyar da Yesu. A wannan “makarantar” da ke sama, Ɗan ya koyi ‘abin da zai faɗa, domin ya iya ƙarfafa marar ƙarfi.’ (Isha. 50:4, Littafi Mai Tsarki) Yesu ya yi amfani da wannan koyarwar sa’ad da yake duniya ta wajen taimaka wa dukan waɗanda suke ‘wahala da masu-nauyin kaya’ su sami kwanciyar rai. (Mat. 11:28-30) Ya kamata maza masu hakki a ƙungiyar Jehobah ma su yi koyi da Yesu ta wajen taimaka wa ’yan’uwansu maza da mata su sami kwanciyar rai. Domin a cim ma wannan burin, an kafa makarantu don a taimaka wa ’yan’uwa maza su ƙware sosai wajen yi wa ’yan’uwansu hidima.

16, 17. Mene ne manufar Makarantar Hidima ta Mulki? (Ka kuma duba ƙarin bayani.)

16 Makarantar Hidima ta Mulki. An soma aji na farko na wannan makarantar a ranar 9 ga Maris, 1959, a birnin  South Lansing, a jihar New York. An gayyaci masu kula masu ziyara da kuma bayin ikilisiya (an kira su shugabannin ikilisiya daga baya) su halarci makarantar na tsawon wata ɗaya. Daga baya, an fassara abin da ake tattaunawa a ajin daga Turanci zuwa wasu harsuna, kuma an soma koyar da ’yan’uwa maza daga dukan faɗin duniya. *

Ɗan’uwa Lloyd Barry yana koyarwa a Makarantar Hidima ta Mulki a shekara ta 1970 a ƙasar Japan

17 Littafin nan 1962 Yearbook of Jehovah’s Witnesses ya yi wannan furucin game da manufar Makarantar Hidima ta Mulki: “A wannan duniyar da mutane suke a taƙure, ya wajaba masu kula a cikin ikilisiyar Shaidun Jehobah su zama mazajen da suka tsara salon rayuwarsu daidai wa daida domin su kula da kowa a cikin ikilisiya sosai. Bai kamata kuma su yi watsi da iyalansu domin suna so su kula da ikilisiya ba, amma ya kamata su kasance da sanin yakamata. Babban gata ne bayin ikilisiya a dukan duniya su halarci wannan Makarantar Hidima ta Mulki domin su koyi abubuwan da za su taimake su su cika hakkinsu bisa ga umurnin Littafi Mai Tsarki.”—1 Tim. 3:1-7; Tit. 1:5-9.

18. Ta yaya dukan bayin Allah suke amfana daga Makarantar Hidima ta Mulki?

 18 Dukan bayin Jehobah sun amfana daga Makarantar Hidima ta Mulki. Ta yaya? Domin sa’ad da dattawa da bayi masu hidima suka yi amfani da abin da suka koya a makarantar, suna yin koyi da Yesu ta wajen sa ’yan’uwa su sami kwanciyar rai. Babu shakka, kana godiya sa’ad da dattijo ko bawa mai hidima ya ziyarce ka domin ya ƙarfafa ka ko ya yaba maka ko kuma ya saurare ka sosai, ko ba haka ba? (1 Tas. 5:11) Irin waɗannan mazan da suka ƙware albarka ne sosai ga ikilisiyarsu!

19. Waɗanne makarantu ne Kwamitin Koyarwa yake lura da su, kuma mene ne manufar makarantun?

19 Wasu makarantu na ƙungiyar Jehobah. Kwamitin Koyarwa na Hukumar da Ke Kula da Ayyukan Shaidun Jehobah ne yake lura da makarantun nan da ke koyar da ’yan’uwa maza masu hakki a ƙungiyar Jehobah. An shirya waɗannan makarantun don su taimaki dattawan ikilisiya da masu kula masu ziyara da kuma mambobin Kwamitin da Ke Kula da Ofishin Reshe su cim ma ayyukansu da kyau. Koyarwa ta Littafi Mai Tsarki da ake tanadarwa a makarantun tana ƙarfafa waɗannan ’yan’uwa su ci gaba da kyautata dangantakarsu da Jehobah da kuma yin amfani da ƙa’idodin Littafi Mai Tsarki a yadda suke bi da tumakin da Jehobah ya ba su riƙo.—1 Bit. 5:1-3.

Aji na farko na Makarantar Koyar da Masu Hidima da aka yi a shekara ta 2007 a ƙasar Malawi

20. Me ya sa Yesu ya ce Jehobah ne yake ‘koyar’ da dukanmu, kuma mene ne ka ƙudura niyyar yi?

20 Hakika, Sarkin Mulkin Allah ya tabbata cewa an koyar da mabiyansa da kyau. Jehobah ne ya fara koyar da Ɗansa, kuma Ɗan ya koyar da mabiyansa. Shi ya sa Yesu ya ce Jehobah ne yake ‘koyar’ da dukanmu. (Yoh. 6:45; Isha. 54:13) Bari mu yi iya ƙoƙarinmu don mu amfana daga koyarwar da Sarkinmu yake tanadar mana, ko da ta hanyar Makarantar Hidima ta Allah ne ko wasu taron ikilisiya ko kuma sauran makarantun da aka tattauna a wannan babin. Kada mu manta cewa ainihin manufar waɗannan makarantun ita ce mu ci gaba da kyautata dangantakarmu da Jehobah domin mu yi hidimarmu da kyau.

^ sakin layi na 5 Ta yaya muka san cewa Uban ya koya wa Ɗansa yadda zai koyar da mutane? Ka yi la’akari da wannan: Yadda Yesu yake yawan yin amfani da kwatanci sa’ad da yake koyarwa ya cika wani annabci da aka yi shekaru da yawa kafin a haife shi. (Zab. 78:2; Mat. 13:34, 35) Babu shakka, Jehobah, Wanda ya sa aka yi annabcin, ya koya wa Ɗansa tun da wuri yadda zai yi amfani da kwatanci ko almara sa’ad da yake koyarwa.—2 Tim. 3:16, 17.

^ sakin layi na 6 ’Yan watanni bayan haka, Yesu ya tura wasu almajirai “saba’in, ya aike su biyu biyu” don su yi wa’azi. Kafin ya aike su, ya koyar da su.—Luk 10:1-16.

^ sakin layi na 12 Wasu sun halarci Makarantar Gilead fiye da sau ɗaya.

^ sakin layi na 13 Don ƙarin bayani a kan yadda ’yan’uwan da suka sauke karatu a Makarantar Gilead suka taimaka a yin wa’azi a faɗin duniya, ka duba littafin nan Jehovah’s Witnesses—Proclaimers of God’s Kingdom, babi na 23.

^ sakin layi na 14 An mai da Makarantar Littafi Mai Tsarki don Kiristoci Ma’aurata da kuma Makarantar Littafi Mai Tsarki don ’Yan’uwa Maza Marasa Aure zuwa Makarantar Masu Yaɗa Bisharar Mulki.

^ sakin layi na 16 A yau, dukan dattawa suna amfana daga Makarantar Hidima ta Mulki. Ana gudanar da wannan makarantar bayan ’yan shekaru kuma tsawon ajin yakan bambanta. Tun daga shekara ta 1984, bayi masu hidima ma sun amfana daga wannan makarantar.