Koma ka ga abin da ke ciki

Koma ga abubuwan da ke ciki

Hagu: Taron da aka yi a fili a Landan, Ingila, a 1945; dama: Ranar taro na musamman a Malawi, Afirka a 2012

SASHE NA 5

Ilimantarwa Game da Mulkin​—⁠Yadda Ake Koyar da Bayin Sarkin

Ilimantarwa Game da Mulkin​—⁠Yadda Ake Koyar da Bayin Sarkin

A CE ka halarci wani babban taro, kuma wani ɗan’uwa matashi daga ikilisiyarku yana ba da jawabinsa na farko a babban taron. Yayin da kake jin daɗin jawabin da yake yi, zuciyarka ta cika da mamakin yadda Allah yake koyar da mutanensa. Ka tuna da jawabinsa na farko a Majami’ar Mulkinku, kuma ga shi yanzu ya zama ƙwararre! Ya samu wannan koyarwar ce a Makarantar Hidima ta Allah da Makarantar Hidima ta Majagaba, kuma shi da matarsa ba su daɗe da halartar Makarantar Masu Yaɗa Bisharar Mulki ba. Yayin da kake tafawa bayan ɗan’uwan ya kammala jawabinsa mai daɗi, sai ka soma tunanin irin koyarwar da bayin Allah da suka halarci taron suka samu.

Littafi Mai Tsarki ya yi annabci game da lokacin da Jehobah zai koyar da mutanensa. (Isha. 54:13) Muna raye ne a wannan lokacin. Muna samun koyarwa ta hanyar littattafanmu da taron ikilisiya da manyan taro da kuma makarantu dabam-dabam da aka tsara don su taimaka mana mu ƙware wajen gudanar da ayyuka a ƙungiyar Jehobah. A wannan sashen, za mu tattauna yadda waɗannan koyarwar suke ba da tabbaci cewa Mulkin Allah yana sarauta a yau.

A WANNAN SASHEN

BABI NA 16

Yin Taro don Ibada

Ta yaya za mu amfana sosai sa’ad da muka halarci taro don mu bauta wa Jehobah?

BABI NA 17

Koyar da Masu Hidimar Mulkin

Ta yaya makarantu na ƙungiyar Jehobah ta shirya masu hidimar Mulkin Allah su cika aikinsu?