Koma ka ga abin da ke ciki

Koma ga abubuwan da ke ciki

 BABI NA 7

Hanyoyin Yin Wa’azi—Yin Amfani da Hanyoyi Dabam-dabam don Yin Wa’azi

Hanyoyin Yin Wa’azi—Yin Amfani da Hanyoyi Dabam-dabam don Yin Wa’azi

MANUFAR WANNAN BABIN

Bayin Allah sun yi amfani da hanyoyi dabam-dabam wajen yi wa jama’a wa’azi

1, 2. (a) Wace dabara ce Yesu ya yi amfani da ita don ya yi wa jama’a wa’azi? (b) Ta yaya amintattun almajiran Yesu suke bin misalinsa, kuma me ya sa?

JAMA’A sun kewaye Yesu a gaɓar teku, sai ya tashi ya shiga cikin kwalekwale kuma aka ɗan ja kwalekwalen zuwa cikin tekun. Me ya sa? Ya san cewa ruwan zai daɗa ƙarfin muryarsa kuma hakan zai sa jama’ar su ji abin da yake faɗa da kyau.—Karanta Markus 4:1, 2.

2 Hakazalika, ba da daɗewa ba kafin a kafa Mulkin a sama har zuwa ’yan shekaru bayan hakan, almajiran Yesu masu aminci sun bi misalinsa ta wajen yin amfani da sababbin hanyoyi don yaɗa bisharar Mulkin ga jama’a. A ƙarƙashin ja-gorancin Sarkin, mutanen Allah sun ci gaba da ƙirƙiro da kuma inganta hanyoyin wa’azi ta wajen yin amfani da sababbin fasaha. Muna so mu yi wa’azi iyakacin ƙoƙarinmu kafin ƙarshen ya zo. (Mat. 24:14) Ka yi la’akari da wasu hanyoyi da muka yi amfani da su don yi wa mutane wa’azi a ko’ina. Ka kuma yi tunani a kan hanyoyin da za ka iya yin koyi da bangaskiyar mutanen da suka yi wa’azi a zamanin Ɗaliban Littafi Mai Tsarki.

Yin Wa’azi ga Jama’a

3. Me ya sa maƙiyan gaskiya suka yi fushi domin muna amfani da jaridu?

3 Jaridu. Ɗan’uwa Russell da abokan aikinsa sun soma wallafa Hasumiyar Tsaro tun shekara ta 1879 kuma ta hakan, sun kai wa mutane da yawa saƙon Mulkin. Amma kafin shekara ta 1914, Kristi ya canja abubuwa don a yaɗa bisharar ga mutane a wurare da yawa. Wannan canjin ya soma ne a shekara ta 1903. A shekarar, Dr. E. L. Eaton, wanda yake wakiltar limaman ɗarikokin Protestant a Pennsylvania ya ƙalubalanci Ɗan’uwa Charles Taze Russell su yi mahawara a kan koyarwar Littafi Mai Tsarki. Eaton ya aika wa Ɗan’uwa Russell wasiƙa kuma a ciki ya ce: “Ina ganin zai dace mu yi mahawara a kan batun wasu koyarwar da ni da kai muke samun saɓani, . . . da mutane za su yi sha’awar ji.” Ɗan’uwa Russell da abokan aikinsa ma sun ga cewa jama’a za su so su ji wannan mahawarar, saboda haka, suka shirya a buga mahawarar a cikin wata jarida mai tashe mai suna The Pittsburgh Gazette. Domin mutane da yawa sun ji daɗin karanta waɗannan talifofin kuma Ɗan’uwa Russell ya bayyana  gaskiyar Littafi Mai Tsarki dalla-dalla, kamfanin da ke wallafa jaridar ya amince ya riƙa wallafa jawaban Russell kowane mako. Babu shakka, hakan ya sa maƙiyan gaskiya fushi sosai!

A shekara ta 1914, fiye da jaridu 2,000 ne suke wallafa jawaban Ɗan’uwa Russell

4, 5. Wane hali ne Russell ya kasance da shi, kuma yaya ’yan’uwan da ke ja-gora a yau za su iya bin misalinsa?

4 Ba da daɗewa ba, kamfanoni masu buga jaridu da yawa sun so su riƙa wallafa jawaban Ɗan’uwa Russell. Kafin shekara ta 1908, Hasumiyar Tsaro ta ce ana wallafa waɗannan jawaban a cikin “jaridu guda goma sha ɗaya a kai a kai.” Amma, ’yan’uwa da suka san sana’ar jaridu suka shawarci Ɗan’uwa Russell cewa idan ya ƙaura da ofisoshin ƙungiyar daga birnin Pittsburgh zuwa wani sanannen birni, ƙarin kamfanonin jaridu za su yarda su wallafa waɗannan jawaban. Bayan Ɗan’uwa Russell ya yi tunani sosai a kan wannan shawarar, sai ya ƙaurar da ofisoshin zuwa Brooklyn, New York, a shekara ta 1909. Mene ne sakamakon hakan? ’Yan watanni bayan suka ƙaura, jaridu guda 400 suka soma ɗaukan jawaban, kuma an ci gaba da samun ƙarin kamfanonin jaridu da suka yarda su ɗauka jawaban. A lokacin da aka kafa Mulkin a shekara ta 1914, jaridu fiye da dubu biyu ne suke ɗaukan jawaban Ɗan’uwa Russell da wasu talifofinsa a harsuna huɗu.

5 Wane darasi mai muhimmanci ne hakan ya koya mana? Ya kamata ’yan’uwan da suke yin ja-gora a ƙungiyar Jehobah a yau su yi koyi da yadda Ɗan’uwa Russell ya nuna tawali’u. A wace hanya ce za su iya yin hakan? A duk lokacin da suke so su ɗauki muhimman matakai, zai dace su yi la’akari da shawarwarin da wasu suka bayar.—Karanta Misalai 15:22.

6. Ta yaya gaskiyar da aka wallafa a cikin jaridu ta shafi wata mata?

6 Gaskiya game da Mulkin da aka wallafa a cikin waɗannan jaridun sun sa mutane su canja salon rayuwarsu. (Ibran. 4:12) Alal misali, Ora Hetzel, wadda ta yi baftisma a shekara ta 1917, tana ɗaya daga cikin mutanen da suka koyi gaskiya ta waɗannan talifofin. Ora ta ce: “Bayan na yi aure, na je in ziyarci mahaifiyata a birnin Rochester, a jihar Minnesota. Sa’ad da na isa wurin, na gan ta tana ciccire shafofin da ke ɗauke da jawaban Ɗan’uwa Russell daga wata jarida. Sai ta bayyana mini abubuwan da ta koya daga jawaban.” Bayan haka, Ora ta amince da gaskiyar da ta koya kuma ta ci gaba da yaɗa bishara game da Mulkin Allah da aminci har tsawon shekaru sittin.

7. Me ya sa ’yan’uwan da ke ja-gora suka canja ra’ayinsu game da yin amfani da jaridu?

7 A shekara ta 1916, abubuwa biyu sun faru da suka sa ’yan’uwa masu ja-gora a ƙungiyar Jehobah su canja ra’ayinsu game da yaɗa bishara ta hanyar jaridu. Na farko, samun kayayyakin buga littattafai sun zama da wuya sosai domin Yaƙin Duniya na Ɗaya da ake yi a lokacin. A shekara ta 1916, sashen da ke kula da jaridu a ofishinmu na ƙasar Biritaniya ya ce: “Sama da jaridu 30 ne kawai suke wallafa jawabai a yanzu. Ba da daɗewa ba yana yiwuwa wannan adadin ya ragu sosai saboda tsadar takardu.” Abu na biyu da ya faru shi ne mutuwar Ɗan’uwa Russell a ranar 31 ga Oktoba, 1916. Saboda haka, an yi  sanarwa a cikin Hasumiyar Tsaro ta 15 ga Disamba, 1916, cewa: “Yanzu da Ɗan’uwa Russell ya rasu, za a daina wallafa jawabai [a cikin jaridu] gabaki ɗaya.” Ko da yake an daina yin amfani da wannan hanyar don yin wa’azi, an ƙirƙiro wasu hanyoyi kamar su “Photo-Drama of Creation,” kuma an yi nasara sosai.

8. Mene ne shirya fim ɗin “Photo-Drama of Creation” ya ƙunsa?

8 Fina-finai. Ɗan’uwa Russell da abokan aikinsa sun yi shekaru uku suna shirya wani fim mai jigo “Photo-Drama of Creation,” wanda aka fitar a shekara ta 1914. (Mis. 21:5) An yi amfani da hotuna masu motsi da sauti da kuma hotunan da aka zana a gilashi don a shirya fim ɗin. Ɗarurruwan mutane sun yi wasan kwaikwayo a kan wasu labaran Littafi Mai Tsarki har ma da dabbobi kuma aka ɗauki hakan a cikin fim ɗin. Wani rahoto da aka rubuta a shekara ta 1913 ya ce: “An kwaso dabbobi iri-iri masu yawan gaske daga wani babban gidan dabobbi don a shirya su kuma a nuna su a fim ɗin Nuhu da  ke nuna tarihin duniya.” Mutane masu yin zane-zane a Landan da New York da Paris da kuma Philadelphia suka yi wa ɗarurruwan gilashin kala da hannu.

9. Me ya sa aka ɗauki lokaci mai tsawo kuma aka kashe kuɗi sosai a shirya fim ɗin “Photo-Drama of Creation”?

9 Me ya sa aka ɗauki lokaci mai tsawo kuma aka kashe kuɗi mai yawa haka wajen shirya fim ɗin “Photo-Drama of Creation”? Zartarwar da aka yi a jerin manyan taron da aka yi a shekara ta 1913 ta bayyana cewa: “Nasarar da jaridun Amirka suka yi a ilimantar da jama’a ta wajen yin amfani da hotuna da bidiyoyin katun a sashen labarai da kuma jaridunsu, tare da yadda silima suke tashe sun nuna cewa suna da nasu muhimmancin, kuma mun yi imani cewa, a matsayinmu na cikakken masu wa’azi da koyar da Littafi Mai Tsarki, za mu yi amfani da wannan hanyar don yaɗa bishara.”

Sama: Dakin da ake ajiye na’urar nuna fim na “Photo-Drama”; kasa: Wasu hotunan da aka zana a gilashin “Photo-Drama”

10. A garuruwa nawa ne aka nuna fim ɗin “Photo-Drama of Creation”?

10 A shekara ta 1914, an nuna fim ɗin “Photo-Drama of Creation” a birane guda 80 a kowace rana. Mutane kusan miliyan takwas a Amirka da Kanada sun kalli fim ɗin. A wannan shekarar kuma, an nuna fim ɗin a ƙasashen Biritaniya da Denmark da Finland da Jamus da New Zealand da Norway da Ostareliya da Siwizalan da kuma Sweden. An shirya wani nau’in fim ɗin a sauƙaƙen salo, wanda bai haɗa da hotuna masu motsi ba domin ƙananan garuruwa. Shirya wannan nau’in da aka kira “Eureka Drama” ya fi “Photo-Drama of Creation” araha da kuma sauƙin tafiya da shi. Kafin shekara ta 1916, an fassara “Eureka Drama” da kuma “Photo-Drama of Creation” zuwa harsunan Armenian da Faransanci da Jamusanci da Hellenancin da Italiya da Polish da Sifanisanci da Swedish da dai wasu harsuna.

During 1914, the “Photo-Drama” was shown in packed auditoriums

11, 12. Ta yaya fim ɗin “Photo-Drama of Creation” ya shafi wani matashi, kuma wane misali ne ya kafa?

11 Fim ɗin “Photo Drama of Creation” da aka fassara zuwa Faransanci ya ratsa zuciyar wani ɗan shekara 18 mai suna Charles Rohner. Charles ya ce: “An nuna fim ɗin a garinmu, wato, Colmar a birnin Alsace, ƙasar Faransa.” Charles ya ci gaba da cewa: “Tun lokacin da na soma kallon fim ɗin, yadda aka bayyana gaskiyar Littafi Mai Tsarki ya burge ni sosai.”

12 A sakamakon haka, Charles ya yi baftisma kuma ya soma hidima ta cikakken lokaci a shekara ta 1922. Ɗaya daga cikin ayyukan da aka fara danƙa masa shi ne nuna wa mutane fim ɗin a ƙasar Faransa. Sa’ad da Charles yake bayyana yanayin aikin, ya ce: “An ba ni ayyuka da dama. Ina kaɗa garaya, ina kula da kuɗin ikilisiya, kuma ina kula da littattafai. An kuma ce in riƙa sa jama’a su yi shiru kafin a fara nuna fim ɗin. A lokacin shan iska, muna rarraba littattafanmu. Mun sa dukan ’yan’uwa maza da mata su rarraba littattafai a sassa dabam-dabam na majami’ar. Kowannensu zai riƙe littattafai a hannunsa sa’an nan ya rarraba wa dukan mutanen da ke sashensa. Ƙari ga haka, muna ajiye tebura a ƙofar majami’ar kuma mu ajiye littattafai da yawa a kansu.” A shekara ta 1925, an gayyaci Charles ya zo ya yi hidima a Bethel na Brooklyn, Amirka. A wurin, aka sanya shi ya riƙa yi wa mawaƙa ja-gora a wani sabuwar tashar  rediyo da ake kira WBBR. Ya kamata misalin Ɗan’uwa Rohner ya motsa kowannenmu ya yi wa kansa wannan tambayar, ‘A shirye nake in yi duk aikin da aka ba ni don in taimaka wajen yaɗa bishara kuwa?’—Karanta Ishaya 6:8.

13, 14. Ta yaya aka yi amfani da rediyo a yaɗa bishara? (Ka kuma duba akwatunan nan “ Shirye-shiryen Rediyo na WBBR” da “ Wani Babban Taro Mai Muhimmanci.”)

13 Rediyo. An soma rage yin amfani da fim ɗin “Photo-Drama of Creation” daga shekara ta 1920, amma aka soma yin amfani da rediyo don yaɗa bisharar Mulki sosai. Ɗan’uwa Rutherford ya yi amfani da rediyo a lokaci na farko a ranar 16 ga Afrilu, 1922, a wani gidan rediyo mai suna Metropolitan Opera House in Philadelphia, a jihar Pennsylvania. Kimanin mutane 50,000 ne suka saurari jawabin nan “Millions Now Living Will Never Die” (Miliyoyin Mutane da Ke Rayuwa Yanzu Ba Za Su Taɓa Mutuwa Ba). Sa’an nan a shekara ta 1923, aka watsa sassan wani babban taro a rediyo a lokaci na farko. Ƙari ga yin amfani da kafofin watsa labarai da ba namu ba, ’yan’uwan da ke yin ja-gora a lokacin sun yanke shawara cewa zai dace mu gina namu gidan rediyon. An gina gidan rediyon a tsibirin Staten, a birnin New York kuma aka yi masa rajista da suna WBBR. An fara watsa labarai a wannan gidan rediyon a ranar 24 ga Fabrairu, 1924.

 A shekara ta 1922, aƙalla mutane 50,000 ne suka saurari jawabin nan “Miliyoyin Mutane da Ke Raye Yanzu Ba Za Su Taɓa Mutuwa Ba” wanda aka yaɗa a gidan rediyo”

14 Hasumiyar Tsaro ta 1 ga Disamba, 1924, ta bayyana manufar buɗe wannan gidan rediyo na WBBR. Ta ce: “Mun gaskata cewa yin amfani da rediyo ne hanya mafi kyau kuma mafi araha na yaɗa gaskiya game da Allah.” Sai mujallar ta daɗa da cewa: “Idan Ubangiji ya ga cewa ya dace a gina ƙarin gidajen rediyo don yaɗa bishara, zai tanadar da kuɗin a hanyar da ya ga dama.” (Zab. 127:1) Kafin ƙarshen shekara ta 1926, bayin Jehobah sun riga sun gina gidajen rediyo guda shida. An gina biyu a ƙasar Amirka, wato WBBR a birnin New York da kuma WORD a kusa da birnin Chicago. Sauran huɗun kuma an gina su ne a ƙasar Kanada, wato a lardin Alberta da British Columbia da Ontario da kuma Saskatchewan.

15, 16. (a) Wane mataki ne limamai a Kanada suka ɗauka domin muna yin amfani da rediyo a yaɗa bishara? (b) Ta yaya jawabai a rediyo suka taimaka a wa’azi gida-gida?

15 Limaman Kiristendom sun lura da yadda bayin Jehobah suke yaɗa saƙon Littafi Mai Tsarki ga jama’a. Wani mai suna Albert Hoffman, wanda ya san aikin da ake yi a gidan rediyon da ke lardin Saskatchewan a ƙasar Kanada, ya ce: “Mutane da yawa sun soma sanin Ɗaliban Littafi Mai Tsari [sunan da ake kiran Shaidun Jehobah a lokacin]. An yi amfani da wannan gidan rediyon don yaɗa bishara sosai har zuwa shekara ta 1928, lokacin da limaman coci suka zuga hukumomi kuma aka rufe dukan gidajen rediyon Ɗaliban Littafi Mai Tsarki a ƙasar Kanada.”

16 Duk da cewa an rufe gidajen rediyonmu da ke ƙasar Kanada, mun ci gaba da yaɗa jawaban Littafi Mai Tsarki a wasu tashoshin rediyo dabam-dabam a ƙasar. (Mat. 10:23) Don a ƙara inganta wannan shirin na yaɗa bishara, an wallafa jerin sunayen gidajen rediyon da ke watsa jawabai a cikin mujallun Hasumiyar Tsaro da kuma The Golden Age (wanda ake kira Awake!  yanzu). An yi hakan ne don masu shela da ke wa’azi su ƙarfafa mutane su saurari waɗannan jawaban a tashoshin rediyo na yankinsu. Wane sakamako aka samu? Bulletin (wanda ake kira Hidimarmu ta Mulki yanzu) ta watan Janairu 1931 ta ce: “Yaɗa jawabai ta tasoshin rediyo taimako ne sosai ga ’yan’uwan da suke bi gida-gida suna wa’azi. Mun sami rahotanni da yawa cewa mutane da yawa sun saurari ’yan’uwa da suka fita wa’azi domin sun riga sun ji jawaban Ɗan’uwa Rutherford kuma hakan ya motsa su su karɓi littattafan da aka ba su.” Bulletin ɗin ya ce yin amfani da rediyo da kuma yin wa’azi gida-gida su ne “hanyoyi biyu na musamman da ƙungiyar Ubangiji take yaɗa bishara.”

17, 18. Ko da yake yanayi ya canja, ta yaya aka ci gaba da yin amfani da rediyo a yaɗa bishara?

17 Tsakanin shekara ta 1930 zuwa 1939, an soma yin adawa da mu don gidajen rediyo da muke amfani da su. Saboda haka, a ƙarshen shekara ta 1937, bayin Jehobah sun yi wani canji. Sun daina yin amfani da gidajen rediyon, kuma suka mai da hankali sosai ga yin wa’azi gida-gida. * Duk da haka, an ci gaba da yin amfani da gidajen rediyo wajen yaɗa bisharar Mulkin Allah a wurare masu nisa. Alal misali, daga shekara ta 1951 zuwa 1991, an yi amfani da wani gidan rediyo da ke birnin West Berlin a ƙasar Jamus wajen yaɗa jawaban Littafi Mai Tsarki a kai a kai domin mutanen da ke zama a Gabashin Jamus su ji saƙon Mulki. Daga shekara ta 1961 har fiye da shekara talatin, an yi amfani da wani gidan rediyo da ke ƙasar Suriname a Nahiyar Amirka ta Kudu don yaɗa gaskiyar Littafi Mai Tsarki na minti 15 a kowane mako. Daga shekara ta 1969 zuwa 1977, ƙungiyar Jehobah ta buga shirye-shiryen rediyo guda 350 a kaset kuma an kira shi “All Scriptures Is Beneficial” (Dukan Nassosi Suna da Amfani). Gidajen rediyo guda 291, a jihohi 48, a ƙasar Amirka suka watsa waɗannan shirye-shiryen. A shekara ta 1996, wani gidan rediyo a Apia, babban birnin tsibirin Samoa da ke Kudancin Fasifik ya watsa wani shiri na mako-mako mai suna “Answers to Your Bible Questions” (Amsoshin Tambayoyin Littafi Mai Tsarki).

18 A ƙarshen ƙarni na ashirin, an daina yin amfani da gidajen rediyo a matsayin hanya ta musamman na yaɗa bishara. Amma, an ƙirƙiro wata fasaha da ta taimaka wajen yin wa’azi ga mutane masu ɗimbin yawa.

19, 20. Me ya sa bayin Jehobah suka shirya dandalin jw.org, kuma wane sakamako ne aka samu? (Ka kuma duba akwatin nan “ JW.ORG.”)

19 Intane. A shekara ta 2013, mutane sama da biliyan biyu da miliyan ɗari bakwai, wato, wajen kashi arba’in cikin ɗari na mutanen da ke duniya ne suke yin amfani da Intane. Wani ƙirge da aka yi ya nuna cewa wajen mutane biliyan biyu suna shiga Intane ta wayar selula da allon kwamfutar hannu, wato Tablets. Wannan adadin yana ƙaruwa a dukan duniya, amma a Afirka ne adadin mutanen da suke shigan Intane ya fi ƙaruwa sosai, inda akwai rajista fiye da miliyan 90 na shiga Intane ta wajen amfani da wayar selula ko kuma allon kwamfutar  hannu. Hakan ya kawo canji sosai ga hanyar da mutane suke samun bayanai.

20 Daga shekara ta 1997, bayin Jehobah sun soma yin amfani da Intane don yaɗa bishara. A shekara ta 2013, an tsara dandalin jw.org a harsuna wajen 300 kuma an saka bayanai iri-iri game da Littafi Mai Tsarki a harsuna sama da 520 don mutane su iya saukar da su. A kowace rana, mutane sama da 750,000 suna shiga wannan dandalin. A kowane wata, ƙari ga kallon bidiyo a dandalin, mutane suna saukar da littattafai fiye da miliyan 3 da mujallu fiye da miliyan 4 da kuma sauti fiye da miliyan 22.

21. Mene ne ka koya daga labarin Sina?

21 Wannan dandalin ya zama wani gagarumar hanyar yaɗa bishara ta Mulki, har a ƙasashen da ba a iya yin wa’azi a fili. Alal misali, a farkon shekara ta 2013, bayan wani mai suna Sina ya shiga wannan dandalin, sai ya kira hedkwata na Shaidun Jehobah da ke Amirka don ya sami ƙarin bayani game da Littafi Mai Tsarki. Me ya sa wannan kiran take da muhimmanci? Domin Sina Musulmi ne da ke da zama a ƙauye a wata ƙasar da aka hana Shaidun Jehobah gudanar da ayyukansu na ibada. Bayan ya yi wannan kiran, sai aka gaya ma wani Mashaidi a Amirka ya riƙa yin nazarin Littafi Mai Tsarki da shi sau biyu a mako. Sun yi amfani da Intane ta kwamfuta mai kamara don yin wannan nazarin.

Koyar da Mutane

22, 23. (a) Shin hanyoyin da ake amfani da su don yi wa jama’a wa’azi sun canja yin wa’azi gida-gida ne? (b) Ta yaya Sarkin ya albarkaci ƙoƙarinmu?

22 Babu ɗaya daga cikin hanyoyin da muka yi amfani da su a dā wajen yaɗa bishara kamar su jaridu, fim ɗin “Photo-Drama of Creation,” Intane da shirye-shiryen da muka yaɗa a gidajen  rediyo, da zai iya sauya wa’azin da muke yi muna bi gida-gida. Me ya sa? Domin bayin Jehobah suna bin gurbin da Yesu ya kafa ne. Ya yi wa’azi ga jama’a, amma ya fi mai da hankali ne ga yin wa’azi ga mutane ido-da-ido. (Luk 19:1-5) Yesu ya koya wa almajiransa su yi hakan, kuma ya gaya musu saƙon da za su bayar. (Karanta Luka 10:1, 8-11.) Kamar yadda muka tattauna a Babi na 6, ’yan’uwan da ke yin ja-gora a ƙungiyar Jehobah suna ƙarfafa kowanenmu ya yi wa’azi ga mutane ido-da-ido.—A. M. 5:42; 20:20.

23 Yanzu an yi fiye da shekara 100 da kafa Mulkin Allah a sama, kuma mutane miliyan bakwai da dubu ɗari tara ne suke wa’azi suna koya wa mutane nufin Allah. Babu shakka, Sarkin ya albarkaci hanyoyin da muke amfani da su don yaɗa bisharar Mulkin. A babi na gaba, za mu tattauna yadda Sarkin ya yi mana tanadin abubuwan da muke bukata don yin wa’azi ga mutane a kowace al’umma da ƙabila da kuma harshe.—R. Yoh. 14:6.

^ sakin layi na 17 A shekara ta 1957, ’yan’uwan da ke ja-gora sun rufe gidan rediyon WBBR da ke birnin New York, kuma shi ne gidan rediyo na ƙarshe.