Koma ka ga abin da ke ciki

Koma ga abubuwan da ke ciki

 BABI NA 14

Sun Goyi Bayan Mulkin Allah Ne Kaɗai

Sun Goyi Bayan Mulkin Allah Ne Kaɗai

MANUFAR WANNAN BABIN

Bayin Allah ba na duniya ba ne domin suna so su kasance da amince ga Mulkin

1, 2. (a) Wace ƙa’ida ce mabiyan Yesu suke bi har wa yau? (b) Ta yaya abokan gāba suka yi yunƙurin yin nasara a kanmu, amma mene ne sakamakon?

YESU ya tsaya a gaban Bilatus, alƙali mafi iko na Yahudawa, kuma Yesu ya ba da wata ƙa’ida da mabiyansa suke bi har wa yau. Ya ce: “Mulkina ba na wannan duniya ba ne: da mulkina na wannan duniya ne, da ma’aikatana su a yi yaƙi, domin kada a bashe ni cikin hannun Yahudawa, amma yanzu mulkina ba daga nan yake ba.” (Yoh. 18:36) Bilatus ya sa an kashe Yesu, amma nasarar da ya yi ba ta wayi gari ba, domin an ta da Yesu. Sarakunan Daular Roma sun yi ƙoƙari su halaka mabiyan Kristi, amma muradinsu ya bi ruwa. Kiristoci na dā sun yaɗa bisharar Mulkin a duk faɗin duniya.—Kol. 1:23.

2 Bayan aka kafa Mulkin a shekara ta 1914, wasu gwamnatoci masu iko sun yi yunƙurin halaka bayin Allah gaba ɗaya. Amma, babu wanda ya yi nasara a cikin su. Gwamnatoci da kuma ƙungiyoyin siyasa da yawa sun yi ƙoƙarin tilasta mana mu goyi bayansu. Amma ba su iya raba kanmu ba. A yau ma, akwai magoya bayan Mulkin a kusan ko’ina a duniya. Duk da haka, muna da haɗin kai kuma babu ruwanmu da harkar siyasa. Irin haɗin kai da muke da shi tabbaci ne cewa Mulkin Allah yana sarauta kuma Sarki Yesu Kristi yana yi mana ja-gora, yana gyara mu kuma yana kāre mu. Ka yi la’akari da yadda ya yi hakan, kuma ka lura da yadda ya taimaka mana mu yi nasara a shari’a sau da sau yayin da muke ci gaba da kasancewa “ba na duniya ba.”—Yoh. 17:14.

Wani Batu Mai Muhimmanci

3, 4. (a) Waɗanne abubuwa ne suka faru a lokacin da Mulkin ya soma sarauta? (b) Shin bayin Allah sun fahimci batun kasancewa da halin ba-ruwanmu da farko kuwa? Ka bayyana.

3 Bayan da Mulkin ya soma sarauta, yaƙi ya ɓarke a sama kuma aka jefo Shaiɗan duniya. (Karanta Ru’ya ta Yohanna 12:7-10, 12.) A sakamakon hakan, yaƙi ya ɓarke a nan duniya, wanda ya gwada imanin bayin Allah. Sun ƙudura su bi misalin Yesu ta wajen kasancewa ba na duniya ba. Amma da farko, ba su gama fahimtar abin da kasancewa da halin-ba-ruwanmu da siyasa ya ƙunsa ba.

 4 Alal misali, a cikin kundi na shida na littafin nan Millennial Dawn, * wanda aka wallafa a shekara ta 1904, an ƙarfafa Kiristoci kada su goyi bayan yaƙi. Amma an kuma ce idan aka tilasta wa Kirista ya shiga soja, ya yi ƙoƙari ya yi aikin da bai shafi faɗa ba, idan kuma hakan bai yiwu ba kuma ya je yaƙi, to ya tabbata cewa bai yi kisa ba. Da yake furta albarkacin bakinsa game da wannan batun, ɗan’uwa Herbert Senior da ke da zama a ƙasar Biritaniya, wanda ya yi baftisma a shekara ta 1905, ya ce: “’Yan’uwa sun ɗan rikice game da batun nan cewa ba laifi ba ne a shiga soja idan za a yi ayyukan da ba su ƙunshi yin kisa kai tsaye ba.”

5. Ta yaya Hasumiyar Tsaro ta 1 ga Satumba, 1915, ta soma ba mu ƙarin haske?

5 Amma Hasumiyar Tsaro ta 1 ga Satumba, 1915, ta soma ba da ƙarin haske a kan wannan batun. Ta yi kalami a kan shawarar da aka bayar a cikin littafin nan Studies in the Scriptures, cewa: “Ba za mu iya cewa idan mutum ya shiga soja don yin wasu ayyukan da ba su ƙunshi faɗa kai tsaye ba ya saba wa imanin Kirista ba.” Amma idan aka ce za a kashe Kirista don ya ƙi shiga da kuma saka kakin soja fa? Talifin ya ci gaba da cewa: “Da a harɓi mutum saboda ya kasance da aminci ga Sarkin Salama kuma ya bi umurninsa, ko kuma a harɓe shi don yana goyon bayan sarakunan wannan duniyar ta wajen taka dokokin Sarkinmu na Sama, wanne ya fi? Ai gwamma mutum ya mutu saboda ya kasance da aminci ga Sarkinmu na Sama.” Duk da wannan gargaɗin, talifin ya ce: “Ba umurni muke bayarwa ba. Shawara ce kawai.”

6 Mene ne ka koya daga misalin Ɗan’uwa Herbert Senior?

6 Wasu ’yan’uwa sun fahimci wannan batun, kuma sun kasance a shirye su fuskanci duk abin da zai faru da su a sakamakon ƙin shiga soja. Herbert Senior da aka ambata a baya ya ce: “A ra’ayina, da mutum ya riƙa sauke harsashi daga jirgi [aikin da ba yaƙi kai tsaye ba] da kuma mutum ya riƙa saka waɗannan harsashin a cikin bindiga don harɓi, duk kanwar ja ce.” (Luk 16:10) An kai Ɗan’uwa Senior kurkuku don ya ƙi shiga soja saboda imaninsa. Da shi da wasu ’yan’uwa 4 suna cikin rukunin mutane 16 da suka ƙi shiga soja saboda imaninsu. Wasu daga cikinsu mabiyan wasu ɗariku ne da aka kai su gidan yari da ke garin Richmond a Biritaniya, kuma daga baya aka san su da sunan nan Richmond 16. Akwai lokacin da aka kai Herbert da kuma wasu bakin dāga a Faransa a ɓoye, kuma aka yanke musu hukuncin kisa. Sai aka jera su a gaban sojoji don a harɓe su, amma ba a yi hakan ba. A maimakon haka, an sauƙaƙa hukuncin zuwa ɗaurin shekaru goma a fursuna.

“Na fahimci cewa an bukaci mutanen Allah su zauna lafiya da kowa har ma a lokacin yaƙi.”—Simon Kraker (Ka duba sakin layi na 7)

7. Mene ne mutanen Allah suka fahimta kafin a soma Yaƙin Duniya na Biyu?

7 Kafin a soma Yaƙin Duniya na Biyu, bayin Jehobah sun fahimci abin da kasancewa da halin-ba-ruwanmu da yaƙi ya ƙunsa da kuma abin da suke bukata su yi idan suna so su  yi koyi da Yesu. (Mat. 26:51-53; Yoh. 17:14-16; 1 Bit. 2:21) Alal misali, an wallafa wani talifi mai jigo “Neutrality” (Halin-ba-ruwanmu) a Hasumiyar Tsaro ta 1 ga Nuwamba, 1939, wanda ya ce: “Daga yanzu, ƙa’idar da bayin Jehobah za su riƙa bi ita ce wadda ta bukace su su guji goyon bayan ƙasashe a yin yaƙi.” Ga abin da Simon Kraker, wanda ya yi hidima a hedkwatar da ke Brooklyn a ƙasar Amirka ya faɗa game da wannan talifin: “Na fahimci cewa an bukaci mutanen Allah su zauna lafiya da kowa har ma a lokacin yaƙi.” Wannan koyarwar da mutanen Allah suka samu a kan kari ta shirya su don su fuskanci farmakin da za a kawo musu domin suna goyon bayan Mulkin.

Sun Fuskanci Hamayya Mai Kama da “Kogi”

8, 9. Ta yaya annabcin manzo Yohanna ya cika?

8 Manzo Yohanna ya annabta cewa bayan an kafa Mulkin a shekara ta 1914, babban macijin, wato Shaiɗan Iblis zai yi ƙoƙarin halaka magoya bayan Mulkin Allah ta yin aman kogi a alamance. * (Karanta Ru’ya ta Yohanna 12:9, 15.) Ta yaya wannan annabcin ya cika? Tun daga shekara ta 1920, an tsananta wa bayin Allah sosai. An tsare Ɗan’uwa Kraker a kurkuku kamar yadda aka yi wa ’yan’uwa da  yawa a Arewacin Amirka a lokacin yaƙin duniya na biyu, don ya goyi bayan Mulkin Allah. A lokacin wannan yaƙin, Shaidun Jehobah ne suka fi yawa a cikin waɗanda aka saka a manyan gidajen yari a ƙasar Amirka don sun ƙi zuwa yaƙi saboda imaninsu.

9 Iblis da ma’aikatansa sun dāge su ga cewa talakawan Mulkin Allah a ko’ina sun musanta imaninsu. A ƙasashen Afirka da Turai da kuma Amirka, an kai su gaban kotuna da kuma waɗanda suke tsai da shawara ko za a saki fursuna tun lokacinsa bai yi ba. Da yake sun yi tsayin daka cewa ba za su yi yaƙi ba, an kai su kurkuku, an yi musu dukan tsiya da kuma lahani. A ƙasar Jamus, bayin Allah sun sha wuya don sun ƙi ɗaukaka Hitler ko kuma shiga soja. An riƙe aƙalla ’yan’uwa 6,000 a sansani a lokacin mulkin Nazi kuma ’yan’uwa sama da 1,600 ’yan ƙasan Jamus da kuma wasu ƙasashe sun rasa rayukansu saboda wulaƙancin da suka sha. Duk da haka, Iblis ya kasa yi wa mutanen Allah lahani na dindindin.—Mar. 8:34, 35.

““Ƙasa” Ta Shanye “Kogin”

10. Mene ne “ƙasa” take wakilta, kuma ta yaya ta taimaka wa bayin Allah?

10 Annabcin da manzo Yohanna ya rubuta ya nuna cewa “ƙasa” za ta shanye “kogin,” wato wasu mutanen kirki a wannan zamanin za su sauƙaƙa tsanantawa da ake yi wa mutanen Allah. A wace hanya ce sashen wannan annabcin ya cika? Shekaru da yawa bayan Yaƙin Duniya na Biyu, ‘ƙasar’ ta taimaka ma waɗanda suka goyi bayan Mulkin Almasihu da aminci. (Karanta Ru’ya ta Yohanna 12:16.) Alal misali, manyan kotuna da yawa sun kāre ’yancin Shaidun Jehobah na ƙin shiga soja da kuma saka hannu a duk wata harkar da ta shafi ɗaukaka ƙasa. Bari mu tattauna yadda Jehobah ya taimaka wa mutanensa su yi nasara sa’ad da aka kai su kotu sau da sau don su ƙi shiga soja.—Zab. 68:20.

11, 12. Waɗanne matsaloli ne ’yan’uwa Sicurella da Thlimmenos suka fuskanta, amma wane sakamako aka samu?

11 Amirka. Anthony Sicurella wanda iyayensa Shaidun Jehobah ne, ya yi baftisma a lokacin da ya kai shekara 15. Sa’ad da ya kai shekara 21, ya yi rajista da hukumar da ke shigar da mutane soja ƙarfi da yaji a matsayin mai bishara. Bayan shekara biyu, wato a shekara ta 1950, ya sake rubuta wasiƙa don a saka sunansa a cikin waɗanda ba za su shiga soja ba saboda imaninsu. Hukumar Bincike ta Amirka ta amince da roƙonsa, amma Ma’aikatar Shari’a ta ƙi. Bayan shari’a sau da sau a kotun, sai Ɗan’uwa Sicurella ya ɗaukaka ƙara zuwa Kotun Ƙoli na ƙasar Amirka kuma kotun ya yarda ya saurari ƙarar. Daga baya, Kotun Ƙolin ya yanke hukunci cewa ɗan’uwanmu bai yi wani laifi ba. Sauran mazauna ƙasar Amirka da suka ƙi shiga soja saboda imaninsu ma sun amfana daga wannan hukuncin da aka yanke.

 12 Girka. A shekara ta 1983, an ɗora wa Iakovos Thlimmenos laifin yin tawaye, don kawai ya ƙi ya saka kakin soja, kuma aka tura shi kurkuku. Bayan da aka sake shi, sai ya nemi aikin akanta amma aka ƙi ba shi aikin don sunansa yana cikin masu aikata laifi. Sai ya kai ƙara kotu, amma da ya ga cewa bai yi nasara a kotunan da ke Girka ba, sai ya ɗaukaka ƙara zuwa Kotun Turai na ’Yancin ’Yan Adam [ECHR]. A shekara ta 2000, Hukuma Mafi Iko a Kotun Turai na ’Yancin ’Yan Adam, wato Grand Chamber, wadda ta ƙunshi alkalai 17 ta goyi bayansa. Hukuncin da wannan hukumar ta yanke ta zama gurbi ga sauran shari’u da suka shafi wariya. Kafin a yanke wannan hukuncin, sunayen ’yan’uwanmu sama da 3,500 a Girka sun shiga takardar sunayen masu aikata laifi domin an kai su kurkuku saboda sun ƙi shiga soja. Amma bayan hukuncin, ƙasar Girka ta kafa wata doka da ta sa aka cire sunayen waɗannan ’yan’uwan daga cikin takardar sunayen masu aikata laifi. Ƙari ga haka, an aiwatar da wata doka da aka kafa sa’ad da aka yi juyin Kundin Tsarin Dokar ƙasar ’yan shekaru kafin wannan lokacin. Wannan dokar ta ba dukan ’yan ƙasar Girka ’yancin yin aikin farar hula idan ba sa so su yi aikin soja.

“Kafin in shiga kotun, na yi addu’a ga Jehobah, sai ya sa zuciyata ta kwanta.”—Ivailo Stefanov (Ka duba sakin layi na 13)

13, 14. Waɗanne darussa ne kake ganin za mu iya koya daga abin da ya faru da Ɗan’uwa Stefanov da kuma Bayatyan?

13 Bulgaria. A shekara ta 1994, an saka sunan Ivailo Stefanov mai shekaru 19 a cikin sunayen masu shiga soja. Ɗan’uwanmu ya ƙi shiga soja kuma ya ƙi yin ayyukan da ba su ƙunshi yin faɗa kai tsaye ba da sojoji ne suke ja-gora. Saboda haka, aka yanke masa hukuncin ɗauri na watanni 18, amma ya kai ƙara don yana da ’yancin ƙin yin aikin soja saboda imaninsa. Sai aka ɗaukaka ƙararsa zuwa Kotun Turai na ’Yancin ’Yan Adam. A shekara ta 2001, an sasanta da Ɗan’uwa Stefanov kafin ma a saurari ƙararsa. Gwamnatin Bulgaria ta yi wa Ɗan’uwa Stefanov da kuma sauran ’yan ƙasar da suka ƙi aikin soja kuma suka zaɓi su yi aikin farar hula ahuwa. *

14 Armeniya. A shekara ta 2001, an tilasta wa Vahan Bayatyan ya shiga soja. * Ya yi ƙoƙari ya kāre kansa a kotunan ƙasar, amma bai yi nasara ba. An yanke masa hukuncin ɗaurin shekaru biyu da rabi a fursuna a watan Satumba 2002. Amma bayan ya yi wata goma da rabi, sai aka sake shi. A lokacin da yake fursuna, ya ɗaukaka ƙara zuwa Kotun Turai na ’Yancin ’Yan Adam kuma suka saurare shi. Amma a ranar 27 ga Oktoba, 2009, Kotun ya yanke hukunci kuma bai yi nasara ba. Hakan ya zama kamar an ci nasara a kan sauran ’yan’uwanmu a Armeniya da suke fuskantar irin wannan matsalar. Amma Hukuma Mafi Iko a Kotun Turai na  ’Yancin ’Yan Adam ta sake bincika hukuncin da aka yanke wa Ɗan’uwa Bayatyan. A sakamakon haka, Hukumar ta yanke hukunci a ranar 7 ga Oktoba, 2011, kuma Ɗan’uwa Bayatyan ya yi nasara. Wannan ne karo na farko da Kotun Turai na ’Yancin ’Yan Adam ya yanke hukunci cewa bisa ga ’yancin ra’ayi da na lamiri da kuma na addini, mutum yana da ’yanci ya ƙi shiga soja saboda imaninsa. Wannan hukuncin ya kāre ’yancin Shaidun Jehobah da kuma na miliyoyin mutane a dukan ƙasashen da ke Ƙungiyar Ƙasashen Turai. *

Shaidun Jehobah a Armeniya sun ji dadin hukuncin da Kotun ECHR ya yanke cewa mutum zai iya kin shiga soja saboda imaninsa

Batun Ɗaukaka Ƙasa

15. Me ya sa mutanen Jehobah ba sa yin abubuwan da ake yi don a ɗaukaka ƙasa?

15 Ban da ƙin shiga soja, mutanen Jehobah suna nuna cewa su magoya bayan Mulkin Almasihu ne ta wajen ƙin yin abubuwan da ake yi don a ɗaukaka ƙasa. Ƙishin ƙasa ta zama gama gari, musamman ma bayan Yaƙin Duniya na Biyu. A ƙasashe da yawa, an bukaci ’yan ƙasa su yi rantsuwa cewa za su kasance da aminci ga ƙasarsu ta wajen raira taken ƙasa ko  kuma sāra wa tutar ƙasarsu. Amma, Jehobah ne kaɗai muke bauta wa. (Fit. 20:4, 5) Hakan ya sa aka tsananta mana sosai. Duk da haka, Jehobah ya sake sa “ƙasa” ko kuma wasu mutanen kirki su sauƙaƙa tsanantawar da aka yi mana. Bari mu tattauna wasu daga cikin nasarorin da Jehobah ya ba mu ta hannun Kristi a wannan batun.—Zab. 3:8.

16, 17. Mene ne Lillian da William, ’ya’yan Gobitas suka fuskanta, kuma me ka koya daga labarinsu?

16 Amirka. A shekara ta 1940, Kotun Ƙoli na Amirka ya goyi bayan Shaidun Jehobah a hukuncin da ya yanke a shari’ar Minersville School District da Gobitis. Wata yarinya Mashaidiya ’yar shekara 12 mai suna Lillian Gobitas * da ɗan’uwanta ɗan shekara 10 mai suna William sun ƙi su sāra wa tuta ko kuma raira taken ƙasa don suna so su yi biyayya ga Jehobah. Saboda haka, aka kore su daga makaranta. Sai aka kai ƙara Kotun Ƙoli, wanda ya yanke hukunci cewa matakin da makarantar ta ɗauka yana bisa doka don hakan yana ƙarfafa haɗin kan ƙasa. Wannan hukuncin ya rura wutar tsanantawa. An kori yara Shaidu da yawa daga makaranta, an kori Shaidu da yawa daga aiki kuma ’yan zanga-zanga sun gwada wa Shaidu da yawa azaba. Littafin nan The Lustre of Our Country ya bayyana cewa “tsanantawa da Shaidun Jehobah suka fuskanta daga 1941 zuwa 1943 tauye ’yancin addini ne da ba a taɓa ganin irinsa ba a ƙarni na ashirin a ƙasar Amirka.”

17 Nasarar magabtan Allah ba ta wayi gari ba. A shekara ta 1943, Kotun Ƙoli ya gudanar da wata shari’a makamancin na iyalin Gobitis. Shari’ar tsakanin West Virginia State Board of Education da Barnette ne. A wannan karon, Shaidun Jehobah ne suka yi nasara. Wannan ne karo na farko a tarihin ƙasar Amirka da Kotun Ƙoli ya sake yanke hukunci da ya bambanta da wanda ya yanke da farko a cikin gajeren lokaci. Bayan wannan hukuncin, tsanantawa da ake yi wa Shaidun Jehobah a Amirka ta ragu sosai. Wannan hukuncin ya kuma kyautata ’yancin dukan mazauna ƙasar Amirka.

18, 19. Mene ne Pablo Barros ya ce ya taimaka masa ya kasance da aminci, kuma ta yaya bayin Jehobah za su iya bin misalinsa a yau?

18 Ajantina. A shekara ta 1976, an kori yaran Ɗan’uwa Barros, wato Pablo mai shekara takwas da kuma Hugo mai shekara bakwai daga makaranta don sun ƙi sāra wa tuta. Wata rana, shugabar makarantar su Pablo ta ture shi kuma ta ƙwale shi. Ban da haka ma, ta sa waɗannan yara biyu su dakata har tsawon awa ɗaya bayan an tashi daga makaranta don ta tilasta musu su sāra wa tuta. Pablo ya ce: “Jehobah ne ya taimaka mini in kasance da aminci duk da wannan matsin.”

19 A lokacin da aka kai wannan batun kotu, alƙalin ya goyi bayan matakin da makarantar ta ɗauka na koran Pablo da Hugo daga makaranta. Amma an ɗaukaka ƙarar zuwa  Kotun Ƙoli na ƙasar Ajantina. A shekara ta 1979, wannan Kotun ya yanke hukunci akasin wanda kotun ƙasa ya yanke. Hukuncin yana kamar haka: “Hukuncin da aka yanke [wato koran yaran daga makaranta] ya saɓa wa dokar ƙasa a kan ’yancin koyo (Sashe na 14) da kuma hakkin jiha na tabbatar da cewa yara sun yi makarantar firamare (Sashe na 5).” Yaran Shaidun Jehobah wajen 1,000 sun amfana daga wannan nasarar. Ba a kori waɗanda aka so a kora ba kuma an dawo da waɗanda aka riga aka kora, kamar su Pablo da Hugo.

Yaran Shaidun Jehobah da yawa sun riƙe amincinsu sa’ad da aka jarraba su

20, 21. Ta yaya hukuncin da aka yanke a shari’ar Roel da Emily ya ƙarfafa bangaskiyarka?

20 Filifin. A shekara ta 1990, an kori Roel Embralinag * mai shekara 9, da ’yar’uwarsa Emily mai shekara 10 da kuma wasu ɗalibai Shaidu wajen 66 daga makaranta don sun ƙi su sāra wa tuta. Leonardo, mahaifin su Roel da Emily ya yi ƙoƙarin fahimtar da hukumar makarantar game da matakin yaransa, amma bai yi nasara ba. Sa’ad da yanayin ya yi  tsanani, sai ya kai ƙara Kotun Ƙoli. Leonardo bai da kuɗi da kuma lauya da zai kāre shi. Amma shi da iyalinsa sun roƙi Jehobah ya taimake su. Yaran kuma suna fuskantar hamayya da ba’a a makaranta. Leonardo ya ga kamar ba zai yi nasara ba domin ba shi da ilimin shari’a.

21 Amma da ikon Allah, wani babban lauya mai suna Felino Ganal, wanda ya yi aiki a sanannun ma’aikatun shari’a da yawa a ƙasar ya tsaya a madadin iyalin. Kafin lokacin wannan shari’ar, Ɗan’uwa Ganal ya daina aiki kuma ya zama Mashaidin Jehobah. A lokacin da aka kai shari’a gaban Kotun Ƙoli, sai kotun ya yanke hukunci cewa Shaidun ba su da laifi kuma ya soke matakin da aka ɗauka na koran yaran daga makaranta. Har ila, waɗanda suka yi ƙoƙarin sa bayin Allah su daina kasancewa da aminci ba su yi nasara ba.

Halin Ba-ruwanmu Ya Jawo Haɗin Kai

22, 23. (a) Mene ne ya taimaka mana mu yi nasara a kotu sau da sau? (b) Wane tabbaci ne irin salama da ke tsakaninmu a faɗin duniya ta bayar?

22 Mene ne ya taimaka wa Shaidun Jehobah su yi nasara a kotu sau da sau? Ba mu da masu iko da ke goyon bayanmu. Duk da haka, alƙalai masu gaskiya a kotuna da kuma ƙasashe da yawa sun kāre mu daga ’yan hamayya, kuma shari’un da suka yanke sun zama gurbi. Babu shakka, Kristi ne yake mara mana baya. (Karanta Ru’ya ta Yohanna 6:2.) Me ya sa muke gwagwarmaya haka a kotu? Ba don mu canja tsarin shari’a ba, amma don mu tabbata cewa babu abin da zai hana mu yi wa Sarkinmu Yesu Kristi hidima.—A. M. 4:29.

23 A wannan duniya da siyasa da kuma ƙiyayya ke raba kan mutane, Sarkinmu Yesu Kristi ya albarkaci mabiyansa saboda ƙoƙarin da suke yi don su riƙe matsayinsu na ba-ruwanmu a sha’anin siyasa da kuma yaƙi. Shaiɗan ya kasa raba kanmu. Mulkin ya tattara miliyoyin mutane da suka ƙi “koyon yaƙi.” Irin salama da ke tsakaninmu a faɗin duniya abin mamaki ne, kuma tabbaci ne cewa Mulkin Allah ya soma sarauta!—Isha. 2:4.

^ sakin layi na 4 An kuma san wannan kundin da sunan nan The New Creation. Daga baya, an canja sunan kundin nan Millennial Dawn zuwa Studies in the Scriptures.

^ sakin layi na 8 Don ƙarin bayani a kan wannan annabcin, ka duba littafin nan Revelation—Its Grand Climax At Hand!, babi na 27, shafuffuka na 184-186.

^ sakin layi na 13 Sasantawar ta bukaci gwamnatin Bulgaria su yarda ma duk waɗanda suka ƙi shiga soja saboda imaninsu su yi aikin farar hula a ƙarƙashin ja-gorancin farar hula.

^ sakin layi na 14 Don ka sami cikakken labari, ka karanta Hasumiyar Tsaro ta 1 ga Nuwamba, 2012, shafuffuka na 29-31, a Turanci.

^ sakin layi na 14 A cikin shekaru 20, gwamnatin Armeniya ta ɗaure Shaidun Jehobah matasa fiye da 450. An saki waɗanda suka rage a cikin kurkuku a watan Nuwamba, 2013.

^ sakin layi na 16 An yi kuskure a rubutun sunan iyalin a cikin takardun kotu.

^ sakin layi na 20 An yi kuskure a rubutun sunan nan Ebralinag a cikin takardun kotu.