Koma ka ga abin da ke ciki

Koma ga abubuwan da ke ciki

 BABI NA 21

Mulkin Allah Ya Halaka Maƙiyansa

Mulkin Allah Ya Halaka Maƙiyansa

MANUFAR WANNAN BABIN

Abubuwan da za su faru kafin yaƙin Armageddon

1, 2. (a) Waɗanne aukuwa ne suka nuna cewa Sarkinmu yana sarauta tun shekara ta 1914? (b) Mene ne za mu tattauna a wannan babin?

HAKIKA, yin la’akari da abubuwan da Mulkin Allah ya cim ma duk da cewa yana sarauta tsakanin maƙiyansa ya ƙarfafa bangaskiyarmu sosai. (Zab. 110:2) Sarkinmu ya shirya masu wa’azi da yardan rai. Ya tsarkake ibadar mabiyansa da kuma ɗabi’arsu. Kuma dukan ƙoƙarin da maƙiyan Mulkin suka yi don su raba kanmu ya ci tura domin muna da haɗin kai a yau. Dukan waɗannan abubuwan da Mulkin ya cim ma da muka tattauna sun tabbatar mana cewa tun shekara ta 1914, Sarkin yana sarauta cikin maƙiyan Mulkin Allah.

2 A nan gaba, Mulkin zai yi abubuwan da suka fi waɗannan. Zai “zo” ya “farfashe dukan waɗannan mulkoki” ya hallaka maƙiyansa. (Mat. 6:10; Dan. 2:44) Amma kafin wannan lokacin, wasu muhimman abubuwa za su faru. Me ke nan? Annabci da yawa na Littafi Mai Tsarki sun amsa wannan tambayar. Bari mu tattauna wasu cikin waɗannan annabcin don mu ga abubuwan da za su faru a nan gaba.

Abin da Zai Faru Kafin “Halaka Farat” Ɗaya

3. Wace aukuwa ta farko ce muke jira?

3 Shelar kwanciyar rai. Sa’ad da manzo Bulus ya rubuta wasiƙa zuwa ga Tasalonikawa, ya ambata aukuwa ta fari da muke jira. (Karanta 1 Tasalonikawa 5:2, 3.) A wannan wasiƙar, Bulus ya ambata “ranar Ubangiji” wadda za ta soma sa’ad da aka kai wa “Babila Babba” hari. (R. Yoh. 17:5) Amma jim kaɗan kafin ranar Jehobah ta soma, al’ummai za su yi shelar “Kwanciyar rai da lafiya”! Wataƙila za a yi wannan shelar sau ɗaya ko kuma sau da yawa. Shin limaman addinai ma za su taya su yin wannan shelar? Tun da su ma na duniya ne, wataƙila za su taya al’ummai yin shela cewa akwai zaman “lafiya.” (Irm. 6:14; 23:16, 17; R. Yoh. 17:1, 2) Wannan shelar kwanciyar  rai da lafiya za ta nuna cewa ranar Jehobah tana gab da aukuwa. Maƙiyan Mulkin Allah ba “za su tsira ba ko kaɗan.”

4. Ta yaya fahimtar annabcin Bulus game da yin shelar kwanciyar rai yake amfanarmu?

4 Ta yaya sanin ma’anar wannan annabcin yake amfanarmu? Bulus ya ce: “Ba cikin duhu ku ke ba, da ranan nan za ta tarshe ku kamar ɓarawo.” (1 Tas. 5:3, 4) Mu ba kamar sauran mutane ba ne domin mun san ma’anar abubuwan da suke faruwa a yau. Ta yaya wannan annabci game da kwanciyar rai da lafiya zai cika? Ba mu sani ba. Amma ya kamata mu sa ido mu ga abin da zai faru. Ƙari ga haka, bari “mu zauna a faɗake, da natsuwa.”—1 Tas. 5:6, Littafi Mai Tsarki; Zaf. 3:8.

Ƙunci Mai Girma Ya Soma

5. Wace aukuwa ce mafarin “matsananciyar wahala”?

5 An kai wa addini hari. Ku tuna cewa Manzo Bulus ya ce: ‘Bayan suna cikin faɗin, kwanciyar rai da lafiya, sai halaka farat ta auko musu.’ Kamar yadda tsawa take biyo bayan walƙiya, hakan ma “halaka farat” ɗaya za ta biyo bayan shelar “Kwanciyar rai da lafiya.” Mene ne za a halaka? Da farko, za a halaka “Babila Babba,” wato daula ta addinin ƙarya da ake kuma kira ‘karuwa.’ (R. Yoh. 17:5, 6, 15) Wannan halakar Kiristendam da dukan addinan ƙarya ce mafarin “matsananciyar wahala” ko kuma ƙunci mai girma. (Mat. 24:21; 2 Tas. 2:8) Wannan aukuwar za ta faru farat ɗaya ga mutane da yawa. Me ya sa? Domin kafin a halaka karuwar, za ta yi zato cewa ita “sarauniya” ce wadda ba za ta taɓa ganin “kewa ba.” Amma za ta ankara cewa ta yi aikin banza. Za a halaka ta kamar a “rana ɗaya.”—R. Yoh. 18:7, 8.

6. Wane ne ko kuma mene ne zai kai wa “Babila Babba” hari?

6 Wane ne ko kuma mene ne zai kai wa “Babila Babba” hari? Wata ‘dabba’ ce mai ‘ƙahoni goma.’ Littafin Ru’ya ta Yohanna ya ce wannan dabbar tana wakiltar Majalisar Ɗinkin Duniya. Ƙahoni goman suna wakiltar dukan ’yan siyasa da suke goyon bayan dabba mai launi “ja wur.” (R. Yoh. 17:3, 5, 11, 12) Shin wannan halakar za ta yi tsanani kuwa? Ƙwarai kuwa! Ƙasashen da ke ƙarƙashin Majalisar Ɗinkin Duniya za su kwashe dukiyar karuwar, su cinye ta kuma su “ƙoƙone ta sarai.”—Karanta Ru’ya ta Yohanna 17:16. *

7. Ta yaya kalmomin Yesu da ke littafin Matta 24:21, 22 suka cika a ƙarni na farko, kuma ta yaya za su cika a nan gaba?

7 Gajartar da kwanakin. Sarkinmu ya bayyana abin da zai faru a wannan lokacin da aka soma ƙunci mai girma. Yesu ya ce: ‘Sabili da zaɓaɓɓu za a gajertar’ da kwanakin. (Karanta Matta 24:21, 22.) Kalmomin Yesu sun ɗan cika a shekara ta 66 a zamaninmu, sa’ad da Jehobah ya  “gajartar” da harin da Romawa suka kai wa Urushalima. (Mar. 13:20) Hakan ya sa Kiristoci da ke Urushalima da kuma Yahudiya su gudu. Mene ne zai faru a dukan duniya a lokacin ƙunci mai girma? Jehobah zai yi amfani da Sarkinmu don ya “gajartar” da harin da Majalisar Ɗinkin Duniya za ta kai wa addinin ƙarya domin kada a halaka shi tare da addini na gaskiya. Addini na gaskiya ɗaya tak zai tsira yayin da aka halaka dukan ƙungiyoyin addinan ƙarya. (Zab. 96:5) Bari mu tattauna abubuwan da za su faru bayan an kammala wannan sashe na ƙunci mai girma.

Abubuwan da Za Su Faru Kafin Yaƙin Armageddon

8, 9. Wace alama ce Yesu ya yi magana a kai, kuma yaya mutane za su aikata don abin da suka gani?

8 Annabcin Yesu game da kwanaki na ƙarshe ya nuna cewa muhimman abubuwa da yawa za su faru kafin a soma yaƙin Armageddon. An ambata abubuwa biyu na farko da za mu tattauna a Linjilar Matta da Markus da kuma Luka.—Karanta Matta 24:29-31; Mar. 13:23-27; Luk 21:25-28.

9 Abubuwan da za su auku a sama. Yesu ya ce: “Rana za ta yi duhu, wata ba za ya ba da haskensa ba, taurari za su yi ta faɗowa daga sama.” Babu shakka, mutane za su daina neman ja-gora daga wurin limamai. Shin Yesu yana yin magana game da abin da zai faru a sama ne? Wataƙila. (Isha. 13:9-11; Joel 2:1, 30, 31) Yaya mutane za su ji sa’ad da suka ga waɗannan abubuwan? Za su yi “ciwon rai” domin sun “ruɗe.” (Luk 21:25; Zaf. 1:17) Hakika, dukan maƙiyan Mulkin Allah, ko su sarakuna ne ko kuma bayi za su ‘sume don tsoro,’ kuma za su gudu su ɓoye. Amma ba za su sami wurin ɓuya daga fushin Sarkinmu ba.—Luk 21:26; 23:30; R. Yoh. 6:15-17.

10. Wane hukunci ne Yesu zai zartar, kuma yaya magoya bayan Mulkin Allah da maƙiyansa za su ji?

10 Zartar da hukunci. Dukan maƙiyan Mulkin Allah za su shaida aukuwar da za ta daɗa ruɗar da su. Yesu ya ce: “Za su ga Ɗan mutum yana zuwa cikin gizagizai tare da iko mai-girma da ɗaukaka.” (Mar. 13:26) Hakan zai nuna cewa Yesu ya zo don ya zartar da hukunci. A wani sashe na wannan annabci game da kwanaki na ƙarshe, Yesu ya ba da ƙarin bayani a kan hukuncin da za a zartar a wannan lokacin. Ya ambata wannan a kwatancin tumaki da awaki. (Karanta Matta 25:31-33, 46.) Za a hukunta amintattun magoya bayan Mulkin a matsayin tumaki kuma za su ‘ta da kansu; gama fansarsu ta kusa.’ (Luk 21:28) Amma, za a hukunta maƙiyan Mulkin a matsayin “awaki” kuma za su “yi baƙin ciki” domin sun  san cewa “za su tafi cikin hukunci na har abada.”—Mat. 24:30; R. Yoh. 1:7.

11. Me ya kamata mu riƙa tunawa da shi yayin da muke jiran abin da zai faru a nan gaba?

11 Bayan Yesu ya zartar da hukunci a kan “dukan al’ummai,” wasu muhimman abubuwa za su auku kafin yaƙin Armageddon. (Mat. 25:32) Bari mu tattauna biyu daga cikin waɗannan aukuwar, wato harin Gog da kuma tattara shafaffu. Yayin da muke tattauna waɗannan aukuwar, ya kamata mu tuna cewa Kalmar Allah ba ta ambata ainihin lokacin da za su auku ba. Wataƙila wasu cikinsu za su faru yayin da wani yake kan aukuwa.

12. Wane hari na ƙarshe ne Shaiɗan zai kai wa Mulkin Allah?

12 Hari na ƙarshe. Gog na ƙasar Magog zai kai wa shafaffun da suka rage a duniya da kuma waɗansu tumaki hari. (Karanta Ezekiyel 38:2, 11.) Wannan harin da Shaiɗan zai kai wa Mulkin Allah da an riga an kafa zai zama na ƙarshe. Shaiɗan ya soma wannan yaƙin da shafaffun da suka rage tun sa’ad da aka koro shi daga sama. (R. Yoh. 12:7-9, 17) Tun da aka soma tattara shafaffu cikin ikilisiyar Kirista ne Shaiɗan ya daɗa ƙwazo wajen neman ya ɓata ci gaban da suke samu a ibadarsu, amma bai yi nasara ba. (Mat. 13:30) A lokacin da za a halaka dukan ƙungiyoyin addinan ƙarya kuma bayin Allah suna zaman lafiya “ba garu, ba kātāko, ba ƙyamare,” Shaiɗan zai sa miyagun bayinsa su kai wa magoya bayan Mulkin hari na ƙarshe.

13. Ta yaya Jehobah zai ɗauki mataki don bayinsa?

13 Ezekiyel ya bayyana abin da zai faru. Sa’ad da yake magana game da Gog, ya ce: “Za ka taso daga wurinka, daga ƙurewar ƙasar arewa, kai, da dangi dayawa tare da kai, dukansu a kan dawakai, jama’a mai-girma, babbar rundunar yaƙi ƙwarai: za ka taso wa mutanena.” (Ezek. 38:15, 16) Wane mataki ne Jehobah zai ɗauka domin wannan harin? Jehobah ya ce: “Hasalata za ta kawo har ƙafar hancina. Zan kira . . . su kawo takobi.” (Ezek. 38:18, 21; karanta Zakariya 2:8.) Jehobah zai ɗauki mataki domin bayinsa da ke duniya. Wannan matakin shi ne yaƙin Armageddon.

14, 15. Wane abu ne kuma zai faru a lokacin da Shaiɗan yake kai wannan harin?

14 Kafin mu tattauna yadda Jehobah zai ɗauki mataki domin bayinsa a lokacin yaƙin Armageddon, bari mu tattauna wata aukuwa ta musamman. Hakan zai auku ne tsakanin lokacin da Shaiɗan zai kai hari da kuma lokacin da Jehobah zai ɗauki mataki a Armagedon. Kamar yadda aka ambata a sakin layi na 11, wannan aukuwa ta biyu ce tattara shafaffun da suka rage.

15 Tattara shafaffu. Matta da Markus sun rubuta cewa furucin da Yesu ya yi game da ‘zaɓaɓɓu,’ wato Kiristoci  shafaffu yana cikin abubuwan da za su faru kafin a soma yaƙin Armageddon. (Ka duba sakin layi na 7.) Sa’ad da Yesu yake magana game da kansa a matsayin Sarki, ya ce: ‘Sa’annan za ya aike mala’iku, za ya tattara zaɓaɓɓunsa daga ƙusurwoyi huɗu, daga iyakar nisan duniya zuwa iyakar nisan sama.’ (Mar. 13:27; Mat. 24:31) Wace tattarawa ce Yesu yake magana a kai? Ba ya magana game da lokaci na ƙarshe da za a tattara shafaffun da suka rage, wanda zai faru jim kaɗan kafin a soma ƙunci mai girma. (R. Yoh. 7:1-3) Maimakon haka, yana magana ne game da wani abu da zai faru a lokacin ƙunci mai girma. Babu shakka, bayan Shaiɗan ya kai hari na ƙarshe ga bayin Allah, za a tattara shafaffun da suka rage a duniya a kai su sama.

16. Wane aiki ne shafaffu za su yi a Armageddon?

16 Ta yaya tattara shafaffun da suka rage yake da alaƙa da yaƙin Armageddon da zai biyo bayan hakan? Lokacin da wannan abin zai faru ya nuna cewa dukan shafaffu za su kasance a sama kafin a soma yaƙin Allah, wato Armageddon. Za a ba abokan sarautar Yesu guda 144,000 iko a sama don su raka Yesu ya halaka maƙiyan Mulkin Allah. (R. Yoh. 2:26, 27) Sa’an nan, mala’iku masu ƙarfi da shafaffun za su raka Kristi, wanda shi ne Jarumin Sarki, yayin da ya kai hari ga “babbar rundunar yaƙi” na maƙiyan da suke so su halaka bayin Jehobah. (Ezek. 38:15) Sa’ad da aka kai musu wannan harin, somawar yaƙin Armagedon ke nan.—R. Yoh. 16:16.

Ƙarshen Ƙunci Mai Girma

An soma yakin Armageddon!

17. Mene ne zai faru da “awakin” a lokacin Armageddon?

17 Zartar da hukunci. Yaƙin Armageddon zai zama ƙarshen ƙunci mai girma. A yanzu, Yesu Alƙalin “dukan al’ummai” ne amma a lokacin, za a ƙara masa matsayi. Zai zama Mai zartar da hukunci, wato zai hukunta dukan mutanen da a dā ya yanke wa hukunci a matsayin “awaki.” (Mat. 25:32, 33) Sarkinmu zai yi amfani da “takobi mai-kaifi” don ya “bubbuga al’ummai.” Hakika, dukan mutane masu kama da awaki, wato daga “sarakuna” zuwa ‘bayi’ za su “shiga madawwamiyar azaba.”—R. Yoh. 19:15, 18; Mat. 25:46.

18. (a) Ta yaya “waɗansu tumaki” za su tsira? (b) Ta yaya Yesu zai kammala yaƙinsa?

18 Babu shakka, reshe ta juye da mujiya kuma waɗanda Yesu ya hukunta a matsayin “tumaki” sun tsira! Shaiɗan ba zai sami damar halaka “taro mai-girma” ba, maimakon haka, waɗannan tumakin da ake gani ba su da mai ceto, za su tsira daga harin maƙiyin kuma za su “fito daga cikin babban tsananin.” (R. Yoh. 7:9, 14) Bayan Yesu ya halaka dukan maƙiyan Mulkin Allah, zai jefa Shaiɗan da aljanunsa cikin rami marar matuƙa. Za a bar su a cikin  wannan wurin har shekara dubu kuma ba za su iya yin kome ba.—Karanta Ru’ya ta Yohanna 6:2; 20:1-3.

Yadda Za Mu Yi Shiri

19, 20. Ta yaya za mu iya yin amfani da darasin da ke Ishaya 26:20 da 30:21?

19 Ta yaya za mu shirya kanmu don waɗannan abubuwan da za su girgiza duniya da suke gab da faruwa? Wata Hasumiyar Tsaro da aka wallafa da daɗewa ta ce: “Za a cece mu idan muka yi biyayya.” Me ya sa? Za mu sami amsar wannan tambayar a gargaɗin da Jehobah ya yi wa Yahudawan da aka kai bauta a ƙasar Babila ta dā. Jehobah ya annabta cewa za a halaka Babila, amma mene ne aka bukaci bayin Allah su yi don su shirya kansu? Jehobah ya ce: “Ku zo, mutanena, ku shiga cikin ɗakunanku, ku rufe wa kanku ƙofofi: ku ɓuya kaɗan, har fushin ya wuce.” (Isha. 26:20) Ka lura da fi’ilan nan: “zo” da “shiga” da “rufe” da kuma “ɓuya.” Dukan su umurni ne. Yahudawan da suka bi wannan umurnin sun zauna a gidajensu nesa da sojojin da suke kashe-kashe a cikin unguwa. Saboda haka, za su tsira idan suka bi umurnin Jehobah. *

20 Wane darasi ne za mu iya koya? Kamar yadda ya faru da waɗannan bayin Allah a zamanin dā, mu ma za mu tsira daga waɗannan abubuwan da ke gab da aukuwa idan muka bi umurnin Jehobah. (Isha. 30:21) Muna samun waɗannan umurnin a ikilisiya. Saboda haka, ya kamata mu riƙa yin biyayya ga umurnin da ake ba mu. (1 Yoh. 5:3) Idan muka yi hakan a yau, za mu daɗa kasancewa a shirye mu yi biyayya a nan gaba. A sakamakon haka, Jehobah wanda shi ne Ubanmu da kuma Sarkinmu Yesu Kristi za su kāre mu. (Zaf. 2:3) Wannan kāriyar za ta sa mu shaida yadda Mulkin Allah zai kawar da dukan maƙiyansa baki ɗaya. Hakan zai zama aukuwar da ba za mu taɓa mantawa ba!

^ sakin layi na 6 Ya dace idan aka ce halakar “Babila Babba” ainihi tana nufin halakar dukan ƙungiyoyin addinai, ba dukan mutanen da ke addinin ba. Saboda haka, yawancin mutanen da suke goyon bayan Babila a dā za su tsira daga halakar, kuma za su nemi su nisanta kansu daga addini kamar yadda littafin Zakariya 13:4-6 ya nuna.

^ sakin layi na 19 Don ƙarin bayani ka duba littafin nan Isaiah’s Prophecy—Light for All Mankind I, shafuffuka na 282-283.