Koma ka ga abin da ke ciki

Koma ga abubuwan da ke ciki

 BABI NA BAKWAI

Bege na Gaskiya ga Ƙaunatattunka da Suka Mutu

Bege na Gaskiya ga Ƙaunatattunka da Suka Mutu
  • Ta yaya muka sani cewa za a yi tashin matattu da gaske?

  • Yaya Jehobah yake ji game da ta da matattu?

  • Waye za a ta da daga matattu?

1-3. Wace abokiyar gaba ce take bin dukanmu, kuma me ya sa bincika abin da Littafi Mai Tsarki ya koyar zai ba mu kwanciyar hankali?

KA YI tunanin kana tsere wa wani mugun abokin gaba. Ya fi ka ƙarfi kuma ya fi ka gudu. Ka san cewa ba shi da tausayi domin ka ga yadda ya kashe wasu abokanka. Dukan ƙoƙari da ka yi ka guje masa, sai kusa yake yi da kai. Kuma babu wani bege. Kwatsam, sai mai ceto ya ɓullo daga gefenka. Ya fi abokin gabanka ƙarfi sosai, kuma ya yi maka alkawarin zai taimake ka. Wannan zai kwantar maka da hankali!

2 A wata hanya, irin wannan abokin gaba yana bin ka. Hakika, dukanmu. Kamar yadda muka koya a babi na baya, Littafi Mai Tsarki ya kira mutuwa abokiyar gaba. Babu wani cikinmu da zai iya guje mata. Da yawa cikinmu mun ga wannan abokiyar gaba ta halaka mutane da muke ƙauna. Amma Jehobah ya fi mutuwa ƙarfi sosai. Shi ne mai Ceto mai ƙauna wanda yake nuna mana yana shirye ya yi nasara a kan wannan abokiyar gaba. Kuma ya yi alkawarin zai halaka wannan abokiyar gaba, mutuwa, har abada. Littafi Mai Tsarki ya ce: “Maƙiyi na ƙarshe da za a kawar, mutuwa ne.” (1 Korinthiyawa 15:26) Wannan albishir ne babu shakka!

3 Bari mu ɗan bincika yadda wannan abokiyar gaba take shafanmu sa’ad da ta ɗauki wani. Yin haka zai taimake mu  mu fahimci wani abin da zai sa mu farin ciki. Jehobah ya yi alkawarin cewa matattu za su sake rayuwa. (Ishaya 26:19) Za a sake mai da su su rayu. Wannan shi ne bege na tashin matattu.

SA’AD DA ƘAUNATACCE YA MUTU

4. (a) Menene yadda Yesu ya ji game da mutuwar wanda yake ƙauna ya koya mana game da yadda Jehobah yake ji? (b) Yesu ya ƙulla wace abokantaka ta musamman?

4 Wani wanda kake ƙauna ya taɓa rasuwa? Baƙin ciki, da makoki, da ganin ba abin da za mu iya yi sai su cika mutum. A irin waɗannan lokatai, muna bukata mu je ga Kalmar Allah domin ta’aziyya. (2 Korinthiyawa 1:3, 4) Littafi Mai Tsarki ya taimaka mana mu fahimci yadda Jehobah da Yesu suke ji game da mutuwa. Yesu, da ya ke kamanin Ubansa, ya san baƙin cikin rasuwar wani. (Yohanna 14:9) Sa’ad da Yesu ya je Urushalima, Yesu yakan ziyarci Li’azaru da yayyensa mata, Maryamu da Marta waɗanda suke gari na kusa, wato Betanya. Suka zama aminai. Littafi Mai Tsarki ya ce: “Yesu dai yana ƙaunar Martha, da ’yar’uwarta, da Li’azaru.” (Yohanna 11:5) Kamar yadda muka gani a babi na baya, sai Li’azaru ya mutu.

5, 6. (a) Yaya Yesu ya yi sa’ad da yake tare da dangi da kuma abokanan Li’azaru da suke makoki? (b) Me ya sa nisawar Yesu take ƙarfafamu?

5 Yaya Yesu ya ji game da rashin abokinsa? Labarin ya ce Yesu ya je wurin dangin Li’azaru da kuma abokanansa sa’ad da suke makoki. Ganin su ya motsa Yesu ƙwarai. “Ya ji haushi cikin ruhunsa, yana jin zafi a ransa.” Sai, labarin ya ce, “Yesu ya yi kuka.” (Yohanna 11:33, 35) Hawayen Yesu sun nuna cewa ba shi da bege ne? Ko kaɗan. Hakika, Yesu ya sani cewa abin al’ajabi ya kusa faruwa. (Yohanna 11:3, 4) Duk da haka, ya ji zafi da baƙin ciki da mutuwa take kawowa.

6 A wata hanya, nisawar Yesu tana ƙarfafa mu. Tana koya mana cewa Yesu da Ubansa, Jehobah, ba sa ƙaunar mutuwa.  Amma Jehobah Allah yana da iyawar ya yaƙi mutuwa kuma ya yi nasara! Bari mu ga abin da Allah ya ba Yesu ikon yi.

“LI’AZARU, KA FITO!”

7, 8. Me ya sa batun Li’azaru ya kasance kamar babu wani bege ga waɗanda suke kallo, amma menene Yesu ya yi?

7 An binne Li’azaru a cikin kogo, sai Yesu ya ce a cire dutsen da aka rufe bakin kogon da shi. Marta ta ce a’a domin bayan kwana huɗu, gawar Li’azaru ta fara ruɓewa. (Yohanna 11:39) A matsayin mutane, babu wani abin da za a iya yi kuma.

Tashin Li’azaru daga matattu ya kawo farin ciki matuƙa—Yohanna 11:38-44

8 Aka ɗauke dutsen, sai Yesu ya yi kira da babbar murya: “Li’azaru, ka fito.” Menene ya faru? “Shi wanda ya mutu ya fito.” (Yohanna 11:43, 44) Za ka iya tunanin irin farin cikin mutanen da suke wurin? Ko Li’azaru ɗan’uwansu ne, ko dangi, ko aboki, ko maƙwabci, sun sani cewa ya mutu. Sai ga shi mutumin da suka sani abin ƙauna yana tare da su kuma. Hakan kamar ba zai yiwu ba. Da yawa hakika sun rungumi Li’azaru don farin ciki. Hakika wannan nasara ce bisa mutuwa!

Iliya ya ta da ɗan gwauruwa—1 Sarakuna 17:17-24

9, 10. (a) Ta yaya Yesu ya nuna Tushen ikon da ya yi amfani da shi ya tashi Li’azaru? (b) Menene amfanin karanta labaran Littafi Mai Tsarki na tashin matattu?

9 Yesu bai yi da’awar ya yi wannan mu’ujiza mai ban al’ajabi da ikon kansa ba. A cikin addu’arsa kafin ya kira Li’azaru, ya bayyana sarai cewa Jehobah ne Tushen ta da mamacin. (Yohanna 11:41, 42) Wannan ba shi ba ne kawai lokacin da Jehobah ya yi amfani da ikonsa a wannan hanyar. Tashin Li’azaru yana ɗaya daga cikin mu’ujizoji tara irin wannan da suke rubuce cikin Kalmar Allah. * Karatu da kuma nazarin waɗannan labaran abin ban farin ciki ne. Sun koya mana cewa Allah ba ya nuna bambanci, domin  tashin matattun ya haɗa da manya da yara, mata da maza, Isra’ilawa da waɗanda ba Isra’ilawa ba. Kuma wannan suna kwatanta farin ciki mai yawa! Alal misali, sa’ad da Yesu ya ta da ’yar yarinya daga mutuwa, iyayenta “suka yi mamaki nan da nan da mamaki mai-girma.” (Markus 5:42) Lalle, Jehobah ya ba su dalilin farin ciki da ba za su taɓa mantawa ba.

Manzo Bitrus ya ta da mace Kirista Dokas—Ayukan Manzanni 9:36-42

10 Hakika, waɗanda Yesu ya ta da su daga matattu sun sake mutuwa daga baya. Amma wannan ya nuna cewa da ma ba a tashe su ba ne? A’a. Waɗannan labarai na Littafi Mai Tsarki sun tabbatar da wata gaskiya mai muhimmanci kuma suna ba mu bege.

KOYO DAGA LABARAN TASHIN MATATTU

11. Ta yaya labarin tashin Li’azaru daga matattu ya taimaka wajen tabbatar da gaskiyar da take rubuce a Mai-Wa’azi 9:5?

11 Littafi Mai Tsarki ya koyar da cewa matattu “ba su san kome ba.” Ba su da rai kuma ba sa rayuwa a wani waje. Labarin Li’azaru ya tabbatar da haka. Bayan ya sake rayuwa, Li’azaru ya burge mutane ne da kwatancin yadda sama take? Ko kuma ya tsorata su ne da labarai masu ban tsoro na wutar jahannama? A’a. Littafi Mai Tsarki bai ƙunshi irin waɗannan labarai ba daga wurin Li’azaru. A cikin kwanakin nan huɗu da yake matacce, bai “san komi ba.” (Mai-Wa’azi 9:5) Li’azaru yana barci ne na mutuwa.—Yohanna 11:11.

12. Me ya sa za mu tabbata cewa tashin Li’azaru daga matattu ya faru da gaske?

12 Labarin Li’azaru kuma ya koya mana cewa tashin matattu gaskiya ne, ba ƙage ba ne. Yesu ya tashi Li’azaru a idon jama’a ne. Har shugabannin addinai, da ba sa ƙaunar Yesu, ba su musanci wannan mu’ujiza ba. Maimakon haka suka ce: “Me muke yi? Gama mutumin nan [Yesu] yana yi alamu dayawa?” (Yohanna 11:47) Mutane da yawa suna so su ga Li’azaru da ya tashi daga matattu. Domin haka, da yawa suka ba da gaskiya ga Yesu. Li’azaru ya tabbatar musu cewa Allah ne ya aiko Yesu. Wannan tabbacin yana da ƙarfi  ƙwarai da wasu shugabannin addinin Yahudawa masu taurin zukata suka shirya su kashe Yesu da Li’azaru.—Yohanna 11:53; 12:9-11.

13. Wane dalili muke da shi na gaskata cewa Jehobah hakika zai iya ta da matattu?

13 Ba daidai ba ne a gaskata cewa tashin matattu gaskiya ne? Daidai ne, domin Yesu ya koyar da cewa wata rana “dukan waɗanda suna cikin kabarbaru” za a tashe su. (Yohanna 5:28) Jehobah shi ne Mahaliccin dukan rai. Zai yi wuya ne a gaskata cewa zai iya sake halittar rai? Hakika, yawanci zai dangana ne a kan tunanin Jehobah. Zai iya tuna dukan ƙaunatattunmu da suka mutu kuwa? Taurari marasa iyaka sun cika sararin samaniya, duk da haka, Allah ya ba kowane suna! (Ishaya 40:26) Saboda haka, Jehobah Allah zai iya tuna dukan ƙaunatattunmu da suka mutu, kuma yana shirye ya sake ba su rai.

14, 15. Kamar yadda abin da Ayuba ya ce ya kwatanta, yaya Jehobah yake ji game da ta da matattu zuwa rai?

14 Amma, yaya Jehobah yake ji game da ta da matattu? Littafi Mai Tsarki ya nuna cewa yana ɗokin ya ta da matattu. Ayuba mutum mai aminci ya yi tambaya: “Idan mutum ya mutu, za ya sake rayuwa?” Ayuba yana magana ne game da jira a kabari har sai lokaci ya yi da Allah zai tuna da shi. Ya ce game da Jehobah: “Za ka yi kira, ni ma in amsa maka: Za ka yi marmarin aikin hannuwanka.”—Ayuba 14:13-15.

15 Ka yi tunani! Jehobah yana murna ya maido da matattu zuwa rai. Ba abin farin ciki ba ne mu fahimci cewa Jehobah yana jin haka? Amma tashin matattu da ke zuwa a nan gaba kuma fa? Wa za a ta da daga matattu, kuma a ina?

“DUK WAƊANDA KE KABURBURA”

16. Za a tashi matattu a wane irin yanayi?

16 Labarin Littafi Mai Tsarki na tashin matattu ya koya mana abubuwa da yawa game da tashin matattu. Mutane da aka maido zuwa rai a nan duniya sun sake saduwa  da waɗanda suke ƙauna. Tashin matattu na nan gaba zai yi kama da wannan—amma zai fi kyau. Kamar yadda muka koya daga Babi na 3, nufin Allah shi dukan duniya ta zama aljanna. Saboda haka matattu ba za a tashe su a duniya da take cike da yaƙe-yaƙe, yin laifi, da kuma cututtuka ba. Za su sami zarafin su rayu a wannan duniya a cikin yanayi na lumana da farin ciki.

17. Yaya yawan tashin matattun zai kasance?

17 Wa za a tasa? Yesu ya ce ‘dukan waɗanda suna cikin kabarbaru [da aka tuna da su] za su ji muryatasa [Yesu], su fito kuma.’ (Yohanna 5:28, 29) Hakazalika, Ru’ya ta Yohanna 20:13 ta ce: “Teku kuma ya bada matattun da ke cikinsa; mutuwa da Hades kuma suka bada matattun da ke cikinsu.” “Hades” na nufin kabari na ’yan adam. (Dubi Rataye, shafuffuka 212-213.) Waɗannan kaburbura za su kasance ba kome cikinsu. Dukan biliyoyin mutane da suka huta a cikinsu za su sake samun rai. Manzo Bulus ya ce: “Za a yi tashin matattu, na masu-adalci da na marasa-adalci.” (Ayukan Manzanni 24:15) Menene wannan yake nufi?

A Aljanna, za a ta da matattu kuma za su sake saduwa da waɗanda suke ƙauna

18. “Masu-adalci” da za a tashe su daga matattu sun haɗa da su waye, kuma ta yaya wannan begen zai shafe ka?

18 “Masu-adalci” sun haɗa da yawancin mutane da muka karanta game da su a cikin Littafi Mai Tsarki waɗanda suka rayu kafin Yesu ya zo duniya. Za ka tuna da Nuhu, Ibrahim, Saratu, Musa, Rut, Esta, da wasu kuma masu yawa. Wasu cikin waɗannan maza da mata masu bangaskiya an yi maganarsu a Ibraniyawa sura 11. Amma “masu-adalci” kuma sun haɗa da bayin Jehobah na zamaninmu. Godiya tā tabbata ga begen tashin matattu, mun ’yantu daga tsoron mutuwa.—Ibraniyawa 2:15.

19. Su waye ne “marasa-adalci,” kuma wane zarafi Jehobah ya ba su don alherinsa?

19 To mutanen da ba su bauta wa Jehobah ba kuma ba su yi masa biyayya ba domin ba su san shi ba fa? Waɗannan biliyoyi na “marasa-adalci” ba za a manta da su ba. Su  ma za a ta da su kuma a ba su lokaci so koyi game da Allah na gaskiya kuma su bauta masa. A cikin shekara dubu, za a ta da matattu kuma a ba su zarafin su haɗu da mutane masu aminci a duniya su bauta wa Jehobah. Zai kasance lokaci mai ban sha’awa. Wannan lokaci ne Littafi Mai Tsarki yake kira Ranar Hukunci. *

20. Menene Jahannama, kuma waye suke zuwa can?

20 Amma wannan yana nufi ne cewa dukan wani mutumin da ya taɓa rayuwa za a tashe shi daga matattu? A’a. Littafi Mai Tsarki ya ce wasu matattu suna “Jahannama.” (Luka 12:5) Jahannama ta samo sunanta ne daga juji da yake bayan Urushalima ta dā. Gawaki da kuma datti ake ƙonawa a wurin. Yahudawa sun ga cewa gawawwaki da aka jefa a can ba su cancanci a binne su kuma a tada su daga matattu ba. Saboda haka Jahannama alama ce da ta dace na madawwamiyar halaka. Ko da yake Yesu zai saka hannu wajen yi wa rayayyu da matattu hukunci, Jehobah shi ne babban Alƙali. (Ayukan Manzanni 10:42) Ba zai ta da waɗanda ya ga miyagu ne da ba su da niyyar canji.

TASHIN MATTATU ZUWA SAMA

21, 22. (a) Wane irin tashin matattu ne kuma ke akwai? (b) Wanene ne na farko da ya sami tashin matattu zuwa rayuwa ta ruhu?

21 Littafi Mai Tsarki ya kwatanta wani irin tashin matattu zuwa rayuwa ta ruhu a sama. Misali ɗaya ne kawai aka rubuta a cikin Littafi Mai Tsarki na irin wannan tashi, na Yesu Kristi.

22 Bayan an kashe Yesu, Jehobah bai ƙyale Ɗansa mai aminci ya kasance a cikin kabari ba. (Zabura 16:10; Ayukan Manzanni 13:34, 35) Allah ya ta da Yesu daga matattu, amma bai tashe shi mutum ba. Manzo Bitrus ya yi bayani cewa “An matar da shi cikin jiki, amma an rayadda shi cikin  ruhu.” (1 Bitrus 3:18) Wannan hakika babbar mu’ujiza ce. Yesu ya sake rayuwa, ruhu ne mai iko ƙwarai! (1 Korinthiyawa 15:3-6) Yesu shi ne na farko wajen samun irin wannan tashin matattu na ɗaukaka. (Yohanna 3:13) Amma ba shi ne na ƙarshe ba.

23, 24. Su waye suke cikin “ƙaramin garke” na Yesu, kuma adadinsu nawa ne?

23 Domin ya sani ba da daɗewa ba zai koma sama, Yesu ya gaya wa mabiyansa masu aminci cewa zai ‘shirya musu wuri’ a can. (Yohanna 14:2) Yesu ya kira waɗanda za su tafi sama “ƙaramin garke.” (Luka 12:32) Mutane nawa ne za su kasance a cikin wannan ƙaramin rukuni na Kiristoci masu aminci? In ji Ru’ya ta Yohanna 14:1, manzo Yohanna ya ce: “Na duba kuma, ga Ɗan ragon [Yesu Kristi] yana tsaye bisa dutsen Sihiyona, tare da shi kuma mutum zambar ɗari da zambar arba’in da huɗu, suna da sunansa, da sunan Ubansa, a rubuce bisa goshinsu.”

24 Waɗannan Kiristoci 144,000, sun haɗa da manzannin Yesu masu aminci, da aka ta da zuwa rayuwa a sama. Yaushe ne tashinsu daga matattu ya kasance? Manzo Bulus ya rubuta cewa zai faru a lokacin bayyanuwar Kristi. (1 Korinthiyawa 15:23) Kamar yadda za ka fahimta a Babi na 9, yanzu muna wannan lokacin ne. Saboda haka raguwar 144,000 waɗanda suka mutu a zamaninmu ana ta da su a take zuwa rayuwa a sama. (1 Korinthiyawa 15:51-55) Amma yawancin ’yan adam suna da begen tashi daga matattu cikin Aljanna a duniya.

25. Menene za a bincika a cikin babi na gaba?

25 Hakika, Jehobah zai yi nasara bisa abokiyar gabanmu mutuwa, kuma za ta shuɗe har abada! (Ishaya 25:8) Amma wataƙila ka yi mamaki, ‘Menene waɗanda aka tashe su zuwa sama za su yi a can?’ Za su kasance a cikin gwamnati mai ban sha’awa na Mulkin sama. Za mu koyi abubuwa game da wannan gwamnatin a babi na gaba.

^ sakin layi na 9 Wasu labaran za a same su a 1 Sarakuna 17:17-24; 2 Sarakuna 4:32-37; 13:20, 21; Matta 28:5-7; Luka 7:11-17; 8:40-56; Ayukan Manzanni 9:36-42 da kuma 20:7-12.

^ sakin layi na 19 Domin ƙarin bayani game da Ranar Hukunci da kuma dalilin hukunci, don Allah ka dubi Rataye, shafuffuka na 213-215.