Koma ka ga abin da ke ciki

Koma ga abubuwan da ke ciki

 DARASI NA 5

Sama’ila Ya Ci Gaba da Yin Abin da Ya Dace

Sama’ila Ya Ci Gaba da Yin Abin da Ya Dace

Sama’ila ya soma zama kusa da mazauni tun yana yaro kuma ya yi aiki a wurin. Mazauni wuri ne da mutane suke zuwa don su bauta wa Jehobah. Ka san abin da ya sa Sama’ila yake zama kusa da mazaunin kuma yana aiki a wurin? Bari mu fara koya game da mamar Sama’ila, wato Hannatu.

Hannatu ta daɗe tana neman haihuwa, amma ba ta samu ba. Saboda haka, ta yi addu’a ga Jehobah kuma ta roƙe shi ya taimake ta. Ta yi wa Jehobah alkawari cewa idan ta haifi ɗa, za ta kai shi ya yi aiki a mazauni kuma ya zauna kusa da wurin. Jehobah ya amsa addu’arta kuma ta haifi ɗa, sai ta sa masa suna Sama’ila. A lokacin da Sama’ila ya kai shekara uku ko huɗu, Hannatu ta kai shi mazauni don ya bauta wa Allah a wurin, kamar yadda ta yi alkawari.

Eli ne babban firist a wannan mazaunin. Saboda haka, shi ne yake wakiltar mutane a gaban Allah. Yana da yara maza biyu da suke aiki a matsayin firistoci a mazaunin. Ka tuna, mazaunin gidan Allah ne, inda mutane suke zuwa su bauta masa. Saboda haka, ya kamata a riƙa yin abin da ya dace a wurin. Amma yaran Eli suna yin abubuwan da ba su da kyau, kuma Sama’ila yana ganinsu. Sama’ila ya yi abubuwan da ba su da kyau kamar yadda yaran Eli suka yi kuwa?— A’a. Ya ci gaba da yin abin da ya dace, kamar yadda iyayensa suka koya masa.

Mene ne ya kamata Eli ya yi wa waɗannan ’ya’yansa?— Ya kamata ya yi musu horo kuma ya hana su yin aiki a gidan Allah. Amma Eli bai yi hakan ba. Saboda haka, Jehobah ya yi fushi da shi da kuma yaransa maza biyu. Jehobah ya ce zai yi musu horo.

Sama’ila ya gaya wa Eli sakon Jehobah

Wata rana, sa’ad da Sama’ila yake barci da dare, ya ji wani yana kiransa, ‘Sama’ila!’ Sai je wurin Eli da gudu, amma Eli ya ce masa: ‘Ban kira ka ba.’ Hakan ya faru har sau uku. A lokaci na ukun,  Eli ya gaya wa Sama’ila cewa idan aka sake kiransa, ya ce: ‘Ka yi magana, Jehobah, gama ina jin ka.’ Abin da Sama’ila ya yi ke nan. Sai Jehobah ya ce masa: ‘Ka gaya wa Eli cewa zan yi wa iyalinsa horo domin abubuwa marasa kyau da suka yi.’ Kana ganin ya yi wa Sama’ila sauƙi ne ya gaya wa Eli wannan saƙon?— A’a. Sama’ila ya ji tsoro, amma ya yi abin da Jehobah ya ce ya yi. Abin da Jehobah ya faɗa ya faru. An kashe yaran Eli biyu, kuma Eli ma ya mutu.

Sama’ila ya kafa mana misali mai kyau. Ya yi abin da ya dace, ko da yake ya ga wasu mutane suna yin abubuwan da ba su da kyau. Kai kuma fa? Za ka zama kamar Sama’ila kuma ka ci gaba da yin abin da ya dace? Idan ka yi hakan, za ka sa Jehobah da kuma iyayenka farin ciki.

KARANTA NASSOSIN NAN

  • 1 Sama’ila 2:22-26; 3:1-21